← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 85

Sashe 28

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Angel tana ƙanƙame da Junaid tana ta Addu'a idonta a rufe,
Junaid ya kawo kansa saitin kunnenta yace "ki zamo jaruma, kisa a ranki zaki iya yaƙar wannan ma..." bai ƙarisa maganar ba yaji Munafurr yana cewa "Junaiduu idan kana son fita daga cikin masarautar nan da ranka toh sai kayi mun abu ɗaya! da hannunka nake so ka kashe sarki Raamud a yanzu babu jira..."
Junaid abun mamaki ya bashi, kallon sarki Raamud yayi yana mai jin takaicinsa sannan ya kalli Munafurr yace "inda ace anban damar na kashe shi ai da yanzu babu labarinsa saboda kallonsa ma banaso nayi, yanzu a raye ake buƙatarsa..."
Munafurr yace "kaii yaro kar kamun tirjiya kayi abunda na saka ka.."
"ShaiÉ—ani baya bani umarni nabi..." a cewar Junaid.
tintsirewa da dariya Munafurr yayi yana faɗin "idan baka kasheshi ba ni zan kashe ka..." ya ƙarasa maganar yana cillo wa Junaid takobinsa, cikin nuna jarumta Junaid ya kaicewa takobin tareda yowa kan Munafurr da gudu zai naushe shi daman yana jin takaicin kashe masa sojoji da yayi a gabansa, yana zuwa kuwa Munafurr yasa hannu ya cabke wuyan Junaid ya ɗaga shi sama da hannu ɗaya, Junaid ƙoƙarin ƙwace wa yake yi amma ba hali domin ba ƙaramin riƙo akayi masa ba,
Angel saita Munafurr tayi da bindigarta ta harba, Lokaci guda Munafurr ya cabke bullet da ɗayan hannunsa yana karya wuya idonsa akan Angel ya ƙara tintsirewa da dariya yana faɗin "kee zaki iya dani ko?.."
Angel fashewa tayi da kuka ta durƙusa da gwiwowinta, shi kuwa Junaid ƙafarsa ne yake ta lilo ya gagara ƙwacewa daga shaƙar da Munafurrr yayi masa ana cikin wannan halin har Junaid ya fara fita hayyacinsa lokaci guda Munafurr ya cillashi gefe sakamakon mashin da aka caka masa ta bayansa, kafin ya waiwaya an ƙara caka masa!
Munafurr waiwayawa yayi yana kallon sarki Raamud wanda ya zagaya ba tareda kowa ya saniba yaje ya ɗauko takobi da mashi ya wurga wa Junaid da Angel yana faɗin "ku tashi ku yaƙi wannan shaiɗanin mutumi marar tausayi idan baku kashe shi ba to shi zai kashe ku..." shima yana riƙe da nasa takobin zai ƙara caka masa yaji Munafurr yayi wurgi dashi gefe guda yasa hannu yana cire mashin da sarki Raamud ya caka masa a fusace ya miƙa hannunsa saiga takobinsa shima ya tafo gareshi ya cabke shi,
Junaid miƙe wa yayi yana maida numfashi hannunsa riƙe da takobin da sarki Raamud ya wurga masa, itama Angel miƙewa tayi saiga sarki Raamud shima ya taso duk suka jeru suna fuskantar Munafurr,
Uma Bara'at kam tana gefe guda tana zaune sai kallon Junaid take wanda goshinsa yake ɗaure da jan ƙyalle, ta gane ƙyallen Ayush ce itama Ayush daga wajen umanta ƙyallen ya fito wato ita kanta Bara'at, sai dai ba haka kawai Ayush ta ɗaurawa Junaid ƙyallen ba akwai saƙo a tattare da wannan ƙyallen...

Junaid da sarki Raamud ne suka rufa gurin Munafurr da gudu suka fara kai masa sara shima haka yake binsu da takobinsa har ya sari Junaid a ciki yayin da ita ma Angel ta rufa masa ta sari ƙafarsa saboda Munafurr ba ƙaramin tsayi ne dashi ba duk ɗinsu a kunkuminsa suka tsaya,
Munafurr jin zafin sarar da Angel tayi mishi ne yasa yakai mata canki itama tayi baya tana birgima, shima sarki Raamud saida ya saita wajen penus ɗin Munafurr ya caka masa wuƙar, wani irin ihuu Munafurr yayi har saida duwatsu suka fara girgiza a fusace Munafurr yakai sara wa sarki Raamud badan sarki ya kaice ba babu abunda zai hana Munafurr ya fille masa kai, Junaid ne shima ya tashi ga jini yanda yake zuba masa domin ba ƙaramin yankuwa yayi a ciki ba Allah yaso ba caka wa akayi ba, ya ƙwalla ƙiran Angel yana faɗin "ki miƙe mu gama da wannan matsiyacin.." wani irin tsalle Angel tayi ta miƙe tsaye da takobinta a hannu ta tafo gurin Junaid da gudu yayin da shi kuma ya sauƙe tafin hannunsa ɗaya ƙasi tana zuwa ta taka hannunsa ya ɗagata sama ya cillata wajen Munafurr ta ƙara yin sama tayi wani ihu ta dage ta sari hannunsa daga saman kafaɗa nan take saiga hannun Munafurr ɗaya ya faɗo ƙasi, kafin Angel ta sauƙo ƙasa kuwa Munafurr ya juyo a wahale ya kai mata sara a wuyanta da hannunsa ɗaya mai riƙe da takobi sannan ya canketa gefe saida tayi sama kamar ƙwallo zata faɗo ƙasi Junaid a ruɗe yayi wani irin ihu yana ƙiran sunanta "Anngeeelll...." ya yo kanta da gudun gaske kafin ta ƙarasa faɗowa ƙasa yakai hannu ya cabketa sukayi ƙasi a tare yana rungume da ita ga jini kuwa yanda yaketa tsiyayowa daga wuyanta ga shatar yankan da akayi mata a wuya ya yanke mata maƙogaro dan ma bakin takobin ne ya sareta da wuyanta zai sare mata gaba ɗaya,
Jikin Angel ne yake kakkarwa sosai murya na rawa daƙer take faɗin "mutuwa zanyi! mutuwa zanyi!! mutuwa zanyi!!! innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Ogah Junaid ka te te temake niiii...."
Shima Junaid hawaye yake yi yana faɗin "bazaki mutu ba Angel insha Allahu zaki tashi kinji..". Angel dishi-dishi ta fara gani idanuwanta suna shirin rufewa bakinta na kakkarwa a hankali take furta "Laa i la ha illa llaa mu ha mma du raaasulullaahh.....". ta cacumi Junaid sosai daga nan bata ƙara motsi ba ga baki a buɗe kamar wacce zatayi magana abunda ta gama furtawa last kenam rai yayi halinsa, ga ido a buɗe tana kallon sama!!!!

A hankali Junaid ya furta "Angel.." bakinsa na kakkarwa jikinsa ne gaba ɗaya yahau ɓari yana jijjigan Angel tareda faɗin "No! no!! noo!!! noooo!!!! kar ki tafi Maryam Please help me don't leave me aloneeee...."
wani irin ihuu Junaid yayi, kuka yake sosai kamar wanda ransa zai fita yana rungume da Angel sosai a jikinsa, Rumana ce ta fara masa gizo ga kuma Angel idonsa a ƙanƙame, haƙwarensa ne suka fara kakkarwa suna dukan juna tsabar raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarsa....

Sarki Raamud ne yake ta fafatawa da Munafurrr shima sararsa akayi a saitin ƙirjinsa sannan aka wurga shi gefe,
tintsirewa da wani irin mahaukacin dariya Munafurr yayi da hannunsa ɗaya, idonsa akan Junaid wanda yake rungume da Angel, Munafurr da takobinsa ya saita Junaid sannan ya wurga masa takobin kafin takobin ya iso ya soki Junaid Bara'at ta tafo da gudun gaske ta rufa kan Junaid tana juyowa kuwa wannan takobin ya shige cikinta, wani irin ƙara Bara'at tayi ta yo báyá ta kwanta a jikin Junaid ta bayansa yaji sauƙar mutum a kwance, juyowa yayi a tsorace yana gudun abunda zai gani domin ihunta ya girgiza masa kunne, ido ya zaro waje baki a buɗe ganin Mata ga tsohon ciki ta sadaukar da rayuwarta akansa, wuƙar gaba ɗaya ya lume a cikinta sai ƙotar wuƙar a waje!!
Da gudu sarki Raamud ya tafo gurin yana ambaton sunata ya ɗagota daga kan Junaid ya kwantar da ita a saman cinyarta ya rungumeta sosai da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana rungume da tsinin cikinta ya kasa furta komai sai ido da yaketa zarowa, hankalinsa ne ya fara barin jikinsa, ƙwaƙwalwarsa ce take juyawa, sarki Raamud gaba ɗaya ya fita hayyacinsa ko kuka ya kasa yi...

Junaid ne ya ƙwantar da Angel ya tashi yazo gaban Bara'at ya durƙusa sannan yasa hannu ya zaro takobin da yake nitse a cikin ta, lokaci guda shima ya ƙara fashewa da matsanancin kuka ga jan ƙyalle a ɗaure da goshinsa,
Chapter 28 · 0% Book details