← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 69

Sashe 8

Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washe gari da safe Iya ta sami Mama a lokacin ta na toya k'osan da zasui kari da shi tace.
"Waini Maimuna ba'a kasafta kud'in nan bane? Na ji shiru ba'a ce Iya ga naki ba. “
"Wani kud'i?“
Mama ta tambayeta don ita a tunaninta wasu kud'i ne Baba ya samu da ban.
"Ban gane wani kud'i ba, ki jiki da wata iriyar tambaya, to kud'in da jikokina suka samo.“
D'an k'aramin murmushi Mama ta yi tace.
"To ki bari in Babansu ya tashi sai ki tambayesa, in kuma in taso miki shi to? “
"Aini na san ba za ki bari a bani ko ficika a kud'in nan ba Maimuna, na rasa me na yi miki a duniyar nan kika bi kika tsaneni daga ke har 'ya'yanki bare ma waccan me tak'adiriyar k'irar samudawa, da fari kamar arnan zabiya, na tabbata da Nimha ce ta samo kud'in nan biyu za'a raba a bani, amman da yake ku mugaye ne an halicci rowa a jininku biyar kun gagara ba ni, kuje kui ta ci insha Allahu sai kun shekara kuna zabga gudawar da ba ta da comlayin, tuban sardauna kawai.“
Shukhura da Nusrat da ke kallo a 'yar k'aramar wayar Mama, duk suna jin abinda Iya ke cewa, zumbur Shukhura ta mik'e ta fito.
"Ki gani a kanki me mugun alkaba'i, insha Allahu kanki bakinki zai komo, naga kud'i namu ne ko, to ba za'a bayar d'in ba kiyi abinda za ki, rowa kuwa mu muka yanke mata cibi, kuma zan nuna miki ni babbar tak'adirya ce don naga kwana biyu kin manta da tak'adirancin nawa, inma tuban galadima ne ko wambai tunda mu musulmai ne Alhmdlillh. “
Tun fara maganar Shukhura Baba ya fito, shi yaiwa Mama alamar ta yi shiru daga k'ok'arin dakatar da Shukhura da take har sai da Shukhuran ta kai aya ya ja hannun Iya suka fice da ke neman fisgewa ta na d'an kuka, sai da sukaje d'akinta sannan ya sake ta yai k'asa da muryarsa sosai yace.
" Tun da na auro Maimuna gidan nan take d'aukar cin kashinki Iya, ba ta tab'ai miki kallon banza bare musu da ke, amman har ta haihu kina yi a gaban 'ya'yanta wanda Shukhura ba ta iya d'auka har sai ta rama sannan kuma kisa in daketa k'arshe kuma kanki abin zai dawo, amman har yau kink'i daina abubuwan da kike, maganar kud'i kuma da kike yaran nan daga su har mahaifiyarsu biyar basu karb'a ba ni suka barwa saboda hidimar gida da kuma auransu in ya taso amman kuma kinzo kina fad'ar maganganu a kai, yanzu meye ribar sa'insa da jikarki? Dan Allah Iya ki canja, ki dinga jan girmanki.“
Kuka iya ta ja had'e da fad'in.
"Tashi ka fita Audu, tashi ka fita nace tun kafin na tsine maka ka bi duniya, har ni za kazo ka gayawa maganganun banza, a gabanka 'yarka tai mini cin mutumci ka kasa d'aukar mataki saboda an baka kud'i?
Jeka kawai Audu na barwa Maimuna da 'ya'yanta kai.“
"Kiyi hak'uri Iya, yanzu zanje na lillisa mata jikinta. “
Kukan Inna ne ya tsaya cak tace.
"Idan har kana son albarka a gurina kada ka tab'a lafiyar tak'adiriyar yarinyar nan, don wallahi kaf tak'adirancinta za ta sauke mini yau.“
B'oyayyen murmushi Baba ya yi ya tashi ya fita.

Yusra da ta dawo daga siyo sikarin da Mama ta aiketa tacewa Mama.
"Wasu a mota sunce suna sallama da Baba. “
Baba da shigowarsa kenan maganar ta sauka a kunnensa ya juya had'e da fad'in.
"Bari naje naga su waye.“
Sai kuma gashi ya dawo yace Yusra ta d'auko tabarmi, ta d'auko taje ta shimfid'a a soro.

Bayan gaishe² Alhj Faruoq ya gabatarwa da Baba abinda ke tafe da su, sannan ya d'ora da cewar.
"Da fatan ba maganar wani a kanta. “
Baba yace.
"Ba maganar kowa a kanta, kuma na yi masa izini yazo ya nemi soyayyarta idan har ta amince mishi babu abinda zai hana na bashi ita, Allah ya tabbatar mana da alkhairi. “
Godiya Alhj Faruoq sukai da shi da abokinsa da suka zo tare, sannan ya sanya driver d'insa da ya tuk'osa ya fito da akwatin da suka zo da shi, akwati ne mai kyau madai daici, Alhj Farouq yace.
"A bawa Shukhura, kayan sun gani suna so ne. “
Baba yace bazai karb'a ba suka ce ai 'yarsu suka kawo, idan kwa bai ansa ba to baiyi na'am da su ba, daga haka sukai masa sallama suka tafi shi kuma ya ja akwatin ya nufi cikin gida......

300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.

Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.

Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.

#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*

Wattpad@Rashuna

*KATANGA*

____________
*FIVE*
A haka rayuwa take juyawa cikin d'an k'aramin familyn nan, Nusrat ta yi candy, su Shukhura kuma saura shekara d'aya su yi, a lokacin ne kuma aka saka musu ranar saukarsu ta islamiya da yake duk ajinsu d'aya har Nimha.
3/4/2014 shine ya kama ranar saukar tasu.
Iya ba ta sauya daga halinta na nuna banbanci tsakanin jikokinta ba har ma ga 'ya'yan nata, don yanzu Baba bai samun cininki sosai a kasuwa sai ya zamto abinci ma Baffa Shamsu ne ke ajiye musu duk wata, saboda ya dawo nan kusa da gidan nasu da zama.
Hakan da matarsa ta gani ne yasa ta d'au babban mataki a kansa, abincin da yake sauke musu sai ya koma saukewa gidan su matar tasa duk wata, gaba d'aya ta bi ta mallake shi ta kanainaye shi ba ta bari ya morawa kowa abin biyar face 'yan uwanta, zagi da tsinuwa kuwa ta na shan shi gurin Iya amma a bayan idonta, in a gaban idonta ne kanzil ba ta iya tofawa, saboda abincin da take kawo mata rana da dare kar taje a daina kawo mata ta shiga uku da cin tuwo don yanzu sai su jera sati suna cinsa huni sir, don yanzu rayuwar gidan lallab'ata suke duk abinda Baba ya samo ciki ake k'ok'arin bawa hak'k'insa.

3/4/2014
Ta kama ranar lahadi kenan, ranar da zuk'ata da yawa ke cikin farin cikin kammala saukar karatun alqurani mai girma, za'a bawa kowa allonta na shaidar saukarta, irin wannan ranar ce ko wani bawa ke burin ta riskesa.
Tun daga farkon layin makarantar tasu mak'il yake da mutane ko 'yan saukarma ba'a hangowa saboda suna tsakiya a cikin rumfa,banda sautin qira'ar Shukhura mai matuk'ar dad'i babu abinda kake juyowa a gurin mutane da dama sun nutsu suna saurarar karatun da ke saukar da nutsuwa a zuk'ata.
Bayan kammala karatun Shukhura ta taso a hankula ta koma gurin zamansu, tun tasowarta FANDA ke binta da kallo, duk da kasancewar ga tsantsar yarinta nan a fuskarta ya na kallo amman kuma ta kama zuciyarsa sosai, tabbas idan ya bari lokaci ya shud'a wani ne zai riga shi mallakarta, don irin su Shukhura ba wanda ake kalla a kau da kai bane, bare nan gaba ta k'ara girma, har ta zauna idonsa ya na kanta, a hankali ya sauke idonsa akan wacce ke Kusa da ita, tabbas ya gano kama a tattare da su ya na kyauta zatan 'yan biyu ne, duk kallon da yake binta da shi mahai finsa Farouq Fanda na lura da shi, ko ma wacce yarinyace wannan tabbas ta taki sa'a gurin d'an nasa, kallo d'aya idan yaiwa mace to tabbas ta taki babbar sa'a, tun kammala karatunsa yake masa zancen aure amma yake tai masa kwana kwane, amman yau yaga alamun d'an nasa yayi kamu, idan kuwa hakane zai fi kowa farin ciki, bare kuma mahaifiyarsa ta ji labari da Hajiya Inna, murmushi ya yi ya na gano yadda Inna za ta d'auki zancen.
Kallonsa ya yi har lokacin idonsa na kan Shukhura, wani kyakkyawan murmushi ya saki ya saka bakinsa dai² kunnansa yace.
"Da dukkan alamu dai yau yarona yaga matar aure. “
Kunya ce tai mugun kama shi, ashe dai duk abinda yake mahaifinsa na lura da shi, shafa kansa ya yi ya na mai sunkui da kai, shafa kansa Abban nasa ya yi yace.
"Soyayya ta na da kyau yarona, Allah yasa matar arzik'i ce. “
A can k'asan mak'oshi ya amsa da
"Amin“
Ya na mai jin muguwar soyayyarta a zuciya wannan shi ake kira love at first sight.
Chapter 8 · 0% Book details