← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 69

Sashe 18

Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ashe ba kallo Shukhura taje ba, can bakin titi taje gurin me saloon ta siyo farata koraye shar da su, ta biya gurin me zob'o ta siyo, ta sayi cewing gum ta jefa a baki sannan ta yo gida, a wani d'an lokon babban tsakar gida ta ajiye faratan da zob'on kana ta shigo.
Sai da ta bari d'aya ta gota ta tabbata a lokacin baccin kowa ya yi nisa ta salallab'a a hankula ta zare sakatar gurinsu ta fice, bayan ta d'auko farar hodarsu, ko tsoron duhun dare ba ta yi, bursuna farar hodar ta yi tun daga fuskarta har wuyanta, ta cire hijabinta sai ta bar wata hula me cibiri cibirin gashi a kanta, rigar jikinta dama ta wani tsohon uniform d'inta na islamiya ne da take bacci da ita.
Cikin dabara ta man manna faratan a yatsunta da chewing gum, ta d'aga jarkar zob'on nan ta shanye ta bar d'an guntu a ciki, nan da nan bakinta ya yi jajir, ta guntsi ragowar a bakinta, turmi ta taka ta zira hannunta ta saman k'ofar d'akin Iya a hankula ta zare sakatar kana ta tura ta shiga ta mayar ta rufe, kallon Iya da ke bacci akan gado ta yi, sakamakon haska 'yar k'aramar cocilan d'in da ke hannunta da ta yi a ranta tace.
'Za ki gane kurenki ne.'
Kan ruwan cikinta ta hau ta zauna, cikin bacci Iya ta ji masifar nauyi ya ziyarceta, a hankula ta bud'e idanuwanta duk a tunaninta madannin dare ne ya danneta, ido biyun da ta yi da Shukhura nan take wani mugun tsoro ya kamata ta bud'e baki za tayi ihu Shukhura ta yi saurin toshe mata baki da wani tsumma da ta yayibo a gefenta, cikin wata iriyar murya me ban tsoro tace.
"Kada ki mana ihu a nan, in ba haka ba zamui daga daga da namanki. “
Nan da nan jikin Iya ya fara rawa kar kar ta fara biya duk wata addu'a da tazo bakinta, son tashi take amma gaba d'aya ta k'asa tashi, hannu Shukhura ta Saka ta karto gefen fuskar Iya had'e da juyar da idanuwanta, rintse ido Iya ta yi kafin ta ji saukar muryar Shukhura a kunnuwanta.
"Al'quran kika kuma tsangwamar Nusrat a cikin gidan nan sai mun cire miki k'afa d'aya da hannu d'aya, mu kuma maidar miki bakinki k'eyarki, sannan mu d'aukeki zuwa cikin ruwa, kima gode Allah kin fara manyanta da wallahi yau sai mun sakaki murmushi da hak'ori d'aya.“
Iya firgita Iya ta firgita, wani mugun tsoro ne ya kuma shiga jikinta ko k'wak'k'waran motsi ta kasa, ta na san magana amman ba dama saboda ta toshe mata baki da t'summa kuma ta rik'e da d'aya hannunta, um umm kawai take ta na girgiza kai hawaye na zuba a idonta, tausayi ta bawa Shukhura don tasan ta sha nauyi, don Iya irin siraran tsofaffin nan ne, ita kuwa Shukhura ta na da jiki, d'agata ta yi ta sauka daga kan gadon ta cire hannunta daga bakinta had'e da fad'in.
"Kada kuma ki sake ki mana ihu don wallahi zan maidar miki da idonki goshi ki zama mai ido d'aya. “
Ta na maganar ne ta na ja da baya, yayin da Iya tace.
"Allah ya baku hak'uri wallahi na daina takura mata, ba iya ita kad'ai ba ma wallahi dukansu na daina shiga harkarsu.“
Wani ihu Shukhura ta yi ta na zaro harshe ya yin da Iya ta yi wani hantsile ta koma k'arshen gado goshinta ya bugi da bango, duk azabar da ta ratsa ta k'wak'wal warta amma haka ta d'inke bakinta saboda tsoron kar ta yi ihu a maidar mata da idonta goshi, ja da baya Shukhura ta ci gaba da yi had'e da fad'in.
"Kada kuma ki sake ki juyo sai mun b'acewa ganinki in ba haka ba kuma zamui sama da ke zuwa fadar sarkin aljanu. “
Ta na kawowa nan, ta bud'e k'ofa ta fice, ta taka turmi ta maidar mata da sakatar ta, kana ta d'auke turmin ta mayar da shi mazauninsa, sannan ta d'auki hijabinta ta shige ciki, ta na k'ok'arin mayar da sakata ta ji muryar Baba yace.
"Waye nan?“
K'irjinta ta ji ya yi wani irin bugu nan da nan wani mugun tsoro ya kama ta ta fara rawa da bakinta.
"Um nice, fitsari na fito naga kamar ba'a saka sakata ba, shine na duba. “
Ta na kawowa nan ta yi saurin fad'awa band'aki don gudun kada ma ya fito ya ganta.
Fuskarta ta wanke da sabulu, ta cire faratan ta jefa a shadda, kana ta fito ta koma d'aki, sai bayan da ta kwanta a shimfid'arta wata muguwar dariya tazo mata, fashewa ta yi da dariya sosai ta na hango yadda idanuwan Iya suka firfito gaba d'aya kamar na mayyar da aka kama, wata dariyar ta kuma fashewa da ita, Nusrat da ke gefenta ta farka ta na kallonta a tsorace.
'Anya kuwa babu almutsutsai akan Shukhura kuwa. '
Taji zuciyarta ta jefo mata wannan tambayar kafin ta ji muryar Baba ya na k'walo mata kira.
" 'Yar baiwa“
"Na'am Baba. “
Ta amsa, ta tashi ta fita jiki a sanyaye.
"Lafiya kuwa nake jiyo dariya a d'akin ku?“
"Wallahi Baba Shukhura ce, kuma ban san me takewa dariyar ba, anya Baba ba za'a nema mata magani ba, ni wasu abubuwan in ta na yi gani nake kamar ba ita kad'ai ba. “
Murmushi Baba ya yi yace.
"Shukhura. “
"Na'am.“
Ta amsa cikin muryar shagwab'a ta fito ta na sosa kai.
"Me ya sakaki dariya cikin tsohon daren nan? “
Sai da ta fara turo baki gaba sannan tace.
"Kawai tuno yadda na tumur mushi hadiza d'azu a makarantar allo na yi, tsokanar Yayarmu ta yi ni kuwa na had'a mata jini da majina ta mik'e da k'yar jiki duk yai tsami kamanninta duk sun sauya bakin nan kamar zunb'utun zakara. “
Ta kuma fashewa da wata dariyar.
"To jeki ki kwanta, kinga dare ne kada ki kuma dariyar, kinji Mamanmu. “
D'aga masa kai ta yi, ta koma d'aki, ya bita da idanuwa a zuciyarsa ya na nema mata shiriya, duk da a zuciyarsa shima ya fara tunanin ba ita kad'ai bace, don al'amarin nata akwai ban tsoro, shiyasa ya daina dukanta ko me Iya tace tayi mata, don ya san itama Iyan da laifinta, kuma duk irin dukan da zaiwa Shukhuran ba shi zai hana ta samo ta inda za ta rama akan Iya ba.
Duban Nusrat ya yi yace.
"Je ki kwanta 'Yar baiwa, zamui maganar da Mamanku da safe.“
"Toh“
Tace had'e da juyawa ta koma d'akin, ta na kwanciya Shukhura ta rungumota ta baya ta na sakin dariya.
"Ina sonki Yayarmu, matuk'ar ina numfashi bazan tab'a bari a tab'a mini ke ba na k'yale, da a tab'a ki gara ni a tab'a ni. “
Wasu hawaye ne suka zubo a fuskar Nusrat wa'yenda ba ta san dalilin zubowarsu ba, hannu ta saka ta baya ta rik'e hannun Shukhura gam had'e da fad'in.
"Nima ina sonki k'anwata, amma don Allah ki daina fad'a kinji k'anwata. “
"Zan daina, idan har aka daina tab'aki, fatana na saka tsoron ki a zuciyar duk me tab'aki, yadda ko ganinki ya yi sai yai shayin yi miki magana."
Ta na kawowa nan ta kuma rungumota a haka bacci ya d'auketa saboda ba ta da wuyar yin bacci, Yusra da ta farka ta jita ba jikin Nusrat ba ta yi juyi ta shige jikinta, hannu Nusrat ta saka ta na shafa kanta, ta na shafo kan Shukhura da d'aya hannun, har lokacin hawaye na zuba a idanuwanta, ta tabbata hawayen k'aunar da 'yan uwanta suke mata ne, kyakkyawar Katanga mahaifiyarsu ta gina musu a zuciyoyinsu na k'aunar junansu, babu ruwansu da k'yashi ko bak'in cikin anyiwa wani abu a cikinsu ba'aiwa d'aya ba, ta na fatan soyayya da k'aunar da sukewa junansu suci gaba da ita har k'arshen numfashinsu, kada Allah ya bawa wani nasarar rusa katangar alak'ar da take ginanna a zuk'atansu.
Dubanta ta kai ga mahaifiyarsu da ke baccinta cikin kwanciyar hankali, duk abubuwan da suka faru ba ta san anyi ba, kasancewarta me nauyin bacci, shiyasa ko wani abun Baba ke buk'ata a gurinsu sai dai ya k'wallowa Nusrat kira.
A b'angaren Iya kuwa k'wak'wame da bango wani wahalallen bacci ya yi gaba da ita, ba tare da ta shirya zuwansa ba.
Chapter 18 · 0% Book details