← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 69

Sashe 16

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun sanda aka saka ranar tarewar Bulki Malam da Abdullahi suke kwantarwa da Maimuna hankali ita kuma ta nuna musu hakan ba komai bane dama ai namiji mijin mace hud'u ne.
D'aki d'aya shi ya zama na Maimuna, d'aya na Abdullahi d'ayan kuma na Bulki.
Ranar juma'a aka d'aura auransu kuma a ranar ta tare, farin ciki gurin Iya ba'a magana kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha, tunda take ba ta tab'a taka gurinsu ba sai a ranar da aka kawo Bulki.
To zamansu dai ga shinan da dad'i babu dad'i a haka rayuwar take juyawa.
Shekarar Nusrat d'aya Maimuna ta sake haihuwar mace wacce taci sunan mahaifiyar Maimuna SAFIYYA suke kiranta SHUKHURA, wata uku tsira Bulki ma ta haifi 'yarta mace wacce taci sunan Iya na gaskiya ZAINAB suke kiranta da NIMHA, anan fa Iya ta baje kolin gata da soyayya, fad'i take yanzu ne aka haifa mata jika.
Tun haihuwar Shukhura sai da Maimuna ta shekara biyar kafin ta haifi wata macen aka saka mata NA'IMA suke kiranta da YUSRA, ita kuwa Bulki ba ta sake haihuwa ba tun daga kan Nimha.

Malam yadda kuka san bai da wata jika sai Nusrat, komai ya samu 'Yar baiwa, kayan ciye² kuwa sai ta rage ake samwa k'annenta, ta shak'u da kakan nata fiye da zatonku masu karatu, shima kuma ta shiga ransa sosai da sosai, ya na bata kulawa ne ba wai don fifici ko wani abuba, sai dai shi a ganinsa dole ne jikanka na fari ya banbanta da sauran, saboda gaba d'aya soyayyar da kakewa d'an naka kake 'yebowa ka aza a kansa.
Amman a gurin Iya da Bulki cin fuskane kawai, don a nuna ba'a son Nimha, hakan yasa suma suka d'auki dukkanin tsana suka d'ora akan Nusrat.

Nusrat Fara ce, amman farinta mai duhu ne, fuskarta siririya ce mai d'auke da siririn dogon hanci, idanuwanta suna da girma matsakaici masu shape d'in k'wan k'walati, cikin idonta fari ne tas ruwa ya kwanta a cikinsa mai maik'o, k'wayar idonta kuwa bak'a ce me silkin brown a ciki, bakinta d'an madai daici ne haka zalika lab'b'anta basu da wani tudu, ko ya ta motsa bakinta wani siririn dimple ne ke bayyana a gefen kumatunta na tsaye wanda yake k'ara fito da zallar kyahunta.
Shukhura kuwa fara ce k'al, suna yanayi da Nusrat, amman ta fi Nusrat kyau, kina ganinta kai tsaye za ki kirata kyakkyawa, saboda ita ko ba tai murmushi ba kumatunta a lotse yake, kuma nata irin na kwance ne.
Yusra ma fara ce kamar Shukhura, itama ta na yanayi da su, amman kuma ba ta da dimple.

A yanzu shekarun Nusrat goma sha biyar a duniya, ta na sss1, su Shukhura kuma shekarunsu goma sha hud'u suna jss 3
auta Yusra kuma shakarunta tara a duniya ta na aji hud'u a primary.
Allah ya yiwa Malam rasuwa shekaru hud'u da suka wuce bayan ya yi jinya kad'an, kowa ya ji babu dad'i domin anyi babban rashi mai girma, musamman Nusrat, bayan mutuwarsa ne kuma soyayyar da Abdullahi wanda yanzu suke kira da Baba yakewa Nusrat ta fara bayyana, don har ga Allah ya fi k'aunarta ya na b'oyewa ne saboda kada ya kuma janyo mata bak'in jini.
mutum ne me wadatar zuciya, ba wani k'arfi ne da shi ba sai dai rufin asiri na Ubangiji, don sun wuce cin yau da na gobe a gidansa, haka zalika bai bar iyalansa a wulak'ance ba, a ko da yaushe za ka samesu cikin kyakkyawar kamala.

Shamsu ya yi aure da matarsa Fiddausi da d'iyarsu Amima sa'ar yusra, sunanta na gaskiya Zainab, shima Iya ya yiwa takwara, a kaduna suke a zaune a saboda anan ne yake aiki, ya ninka yayan nasa sosai a fannin dukiya wanda k'arara Iya ke nuna banbanci tsakaninsu da Baba.
Aunty Maryam kuma mijinta ya koma kano da aiki don haka ya d'ebe su suka koma kano da zama, 'ya'yansu hud'u yanzu, Hidaya, Abdul, Hibba, Abbas, suma sosai Iya take ji da su saboda suma mahaifinsu na da kud'i, kuma anai mata aike akan kari.

*Wannan kenan*

300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
in kuma katin waya ne ki turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.

Garab'asa gareku masoyana, duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.

Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana.

#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*

Wattpad@Rashuna

*KATANGA*

____________
*TWO*
Yau ta kama lahadi, duk da suna cikin hutun makarantar boko, su Nusrat duk sun tsefe kawunansu zasu kitso, sai da Nusrat ta fara wanka ta yiwa Yusra ma ta wanke mata kanta ta taje ta shafe mata shi da mai sannan suka shirya zasu tafi, kallon Shukhura Mama ta yi da ta saka hijabi zasu tafi tace.
"Ke yanzu ba za ki wankan ba haka za ki bisu?“
Sai da ta fara turo baki gaba kana tace.
"To Mama nan da nan d'in sai na yi wanka, abinda yanzun nan za'a mana mu dawo. “
"Allah ya shirya. “
Mama kawai tace ta na mik'awa Nusrat kud'in kitson nasu had'e da fad'in.
"Ta fara yi miki kitson, kuma tai miki manya don kinsan yadda yawan kanki yake, kuma ke zan barwa girkin dare don fita zan yi, saura kuma kice a fara yiwa Yusra don na san hali. “
Murmushi Nusrat ta yi, bayan ta saka hannu biyu ta anshi kud'in kana tace.
"Mun tafi.“
Maman tace.
"Allah ya tsare, ku dai yi addu'a kafin ku fita. “Tace.
"Amin, tom insha Allah.“ Tare da jan hannun Yusra suka bi bayan Shukhura da ta fita tun d'azu.

Har sun d'an gota gurin Iya ta hango giftawarsu da sauri ta k'walowa Nusrat kira.
"Ke ke A'i zo nan. “
Da yake haka take kiranta tun ma Malam na raye, juyowa Nusrat ta yi, Yusra ta turo baki gaba tace.
"Wallahi na san aiki za ta sakaki, kawai kizo mui tafiyarmu mu rabu da ita.“
Murmushi Nusrat ta yi tace.
"Bara dai naje na ji kiran da take mini.“
"Tak'i ta rabu da ni d'in, shegiya ifrituwa me zunb'utun baki. “
Suka jiyo muryar Iya daga ciki, kuma turo baki Yusra ta yi ta na hararar gurin kafin ta fice waje da sauri, Nusrat kuma ta nufi gurin Iyan ta na murmushi.
Gyaran d'aki tace tai mata da wankin band'aki sai 'yan tsunmokaranta ma da tace ta wanke mata.

Kallon Shukhura Nana me kitso ta yi tace.
"Ina su Yayar taku?“
"Ga sunan suna hanya. “
"To shiga ciki, gani nan bari na k'arasa sharar nan. “
Rufe bakinta kenan Yusra ta yi sallama, kallon ta Shukhura ta yi bayan ta amsa sallamar ta ta tace.
"Ina Yayarmun?“
"Ba Iya ce ta kirata ba, har ta na ce mini ifrituwa. “
Wani haushi ne ya kama Shukhura, ta zura takalminta ta fasa shiga d'akin ta fice a fusace Yusra ta biyo bayanta.

Kamar an jefota ta shigo ta na kallon Nusrat da ke zubar da shara.
"Sannu"
Tace mata, kafin ta shige zuwa gurin Iya, iya na ganinta ta d'aure b'arin goron da ta b'antara a gefen zaninta kana tace.
"To rasa kunya b'eran tanka, kinzo kimin rashin kunyar taki ne? “
Kar katar da kai Shukhura ta yi tace.
"Ashe 'Yar aljanu na da rana tun da har an iya sakata aiki, me yasa ba ki kirawo 'yar lelen taki tai miki ba sai ita za ki saka, amma in abu zaki bayar babu wanda ke gabanki sai Nimha, amman in aikine sai wacce kika raina, don kin san Nimha ko tsintsiya ba za ta iya d'aga miki ba.
Bayan kuma kitso zamu je kina gani kuma Mamanmu na zaman jiranmu“

"Tunda dai ba ke na saka ba, ki shige ki bani guri, kiyi can da rashin kunyarki. “
Cewar Iya
"Waa aini kin san abinda bazai tab'a yuyuwa bane, don wallahi bazan bautawa wanda bai san ina yi ba, in cin mutumci ne ya taso azo a tarkace mini, lalalala wallahi, itama ita taga za ta iya.“
"Ni kikewa cin mutumci Safiya, Allah ya dawo da Audu, wallahi za ki gane Ubanki na haifa. “
"Amin, ya dawo d'in ki gaya masa, wallahi duka d'aya yamin kinsan sai na bi ta inda zan rama, Allah ya baki sa'a. “
"Wai da sa'ar ki kikeyi ne Shukhura?“
Cewar Nusrat ta na kallonta, ba ta bata amsa ba ta fice ta na zunb'uro baki, Iya kuwa k'ifi² ta yi da ido tunowa da ta yi sanda ta saka Nusrat a gaba ta na zaginta Shukhura ta amshe ta hayayyak'o kamar za ta daketa har sai da Mama ta fito ta kikkifawa Shukhura mari, shine Baba ya na dawowa Iya ta kwashe ta gaya masa, aikwa ranar Shukhura ta sha duka gurin Baba, ita kuwa ta d'auki aniyar wallahi sai ta rama akan Iya, sai da ta bari duhu ya yi ta kad'a karkashinsu me yauk'i taje ta zuba a band'akin Iya,don ta na da tabbacin yanzu za ta fito ta shiga band'akin ta lab'e a bayan k'ofa, Iya na shiga ta yi sufa ta fad'i Shukhura ta fito ta na ta k'yak'yata mata dariya, tace mata kad'an ta gani muddun ta na sakawa Baba na dukanta, Iya kuwa jiki yai tsami da k'yar ta iya mik'ewa.

"Yanzu Mama kina kallo ga Iya can ta saka Nusrat aiki.“
Shukhura ta fad'a ta na turo baki gaba. “
"To meye, don ta sakata aiki?“
Mama ta fad'a ta na cigaba da tankad'en da take.
"Amma Mama kefa kikace a fara mata kitson saboda za ki bar mata girki.“
"Yanzu kuma na fasa ba, kije ke a fara miki sai ki baro Yusran a can in Yayar taku tazo sa taho tare sai ki karb'i girkin na samu na fita. “
"Amma Mama....“
Dakatar da ita Mama ta yi had'e da fad'in.
"Ban san jin komai ki shige kije kiyi abinda na saki. “
Fita ta yi ta na tutturo baki Mama ta girgiza kai had'e da fad'in.
"Allah ya shirya. “
Chapter 16 · 0% Book details