← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 69

Sashe 11

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka rayuwa take tafiya har aka shiga watan azumi, soyayyar Shukhura da Mustapha kuwa ta yi k'arfin da ba kwa zato, har an kawo kud'i an saka rana ta na yin candy, Nimha ma Saminu ya kawo kud'inta tare za'a had'asu da Shukhura, babu haukan da Umma ba ta yi ba, Baba kuwa yace ba ta isa ba, ai arzik'i na Allah ne.
Nusrat dai har yanzu babu wanda take saurara har ta kaima yanzu in za ta fita nik'af d'inta take mak'alewa a hammata sai taje soro ta d'aura don kar ma a ganta ace ana sonta, sun sha fad'a sosai da Shukhura har tace sai ta gayawa Mama, sai kuma ta kasa fad'a, ita tausayi ma Nusrat d'in take bata gani take kamar da aljani take yin mafarkin nata da take kira gaskiya.
Iya da Nimha kuwa sun dinga mata habaici kenan wai Allah ya yi mata nauyin k'afa gashi har za'a aurar da k'annenta biyu ita ko mashin shini ba ta da, ita kuwa ko kad'an hakan ba ya damunta lokacin auran nata ne bai zo ba idan yazo kowa zai sha mamaki.
Mama da Baba kuwa Nusrat d'in tausayi take basu, don Baba har rubutu yake yi ya na bata ta sha na taimako ko Allah zai fito mata da nata mijin itama ya had'asu gaba d'aya ya aurar.
Yau aka kai azumi na goma, kuma yaune Mustapha ya kawowa Shukhura kayan Shan ruwa, madara ce peak ta ruwa katan uku sai bomvita babban robar uku milo babban gwangwani uku, sai suger k'aramin buhu, k'wai kiret biyar, sai kuma kayan fruit, Iya kuma ya aiko mata da katan d'in maltina da madara, saboda kullum yazo zance har soro take zuwa su gaisa ya d'an bata hasafi, tun Shukhura na jin takaicin hakan da kunya har tazo ta sake gaba d'aya, don lamarin Iya sai du'ai son abun duniyarta har ya fi na daa.
sai tsalle take ta na murna, da yazo da daddare tun kafin Shukhura ta fita ta riga ta fita don ta na ankare da hararar da take zabga mata in taje, har k'asa ta tsuguna ta nai masa godiya kamar za ta ari baki.
Umma bak'in cikin duniya ya isheta, ta na kallo aka shige da wa'yannan uban kayan d'akin Mama, ita kuwa Saminu kayan fruit kawai ya kawo sai k'wai kiret uku, takaicin duniya duk ya bi ya isheta ta dinga tsine masa albarka, ji take kamar ta rufe Nimha da duka don ta kaici, amman ta ci alwashin daga bikin Nimhan har na Shukhuran babu wanda muddun rai ba za ta zuba ido 'yarta ta fad'a gidan wahala ba 'yar kishiyarta ta tsunduma gidan hutu ai taci baya, za ta yi duk yadda za tai taga wannan auran bai yi ba, ko na Nimha ya yi to tabbas na Shukhura bazai yuyu ba za ta shiga duk inda za ta shiga ba tare da ta nemi taimakon kowa, saboda daga k'arshe wanda ka nemi taimakonsa shine wanda yake k'ok'arin ganin bayanka, tun da ga shinan a fina finan hausa ana yi da kuma littattafan hausa..........

300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.

Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.

Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.

#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*

Wattpad@Rashuna
https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_

*KATANGA*

____________
*SEVINE*
San da Baba ya shiga cikin gidan Umma kad'ai ya tadda da Nimha a tsakar gida suna karyawa, tun shigowarsa Umma ke bin akwatin hannunsa da kallo, ganin ya nufi d'akinsa zai ajiye tace.
"Babansu wannan akwatin fa? “
Bai magana ba ya shiga ya ajiye kana ya fito ya k'wallawa Mama kira, ta amsa ta fito.
"Kin kai mini ruwan wankan?“
"Eh na kai.“
"To bani kwandon da jallabiyata. “
Duk na kai suna can.“
"To sannu Allah ya yi albarka. “
"Amin.“
Tace ta juya ta koma d'aki, har zai shiga band'aki Umma tace.
"Babansu magana fa nake kaimin shiru. “
"Ko ma dai ta meye idan kinyi hak'uri za kiji.“
Daga haka yai shigewarsa band'akin.

Sai da yai wanka ya shirya, kana ya karya, sannan ya k'wallowa Nusrat kira, da tazo yace.
"D'auki wannan akwatin ki kaimin ita gurin Iya. “
Tace."To“ had'e da d'aukar akwatin ta nufi gurin Iya, shi kuma yacewa su Mama da Umma suzo su same shi gurin Iyan ya biyo bayan Nusrat d'in, Iya na tambayarta wannan akwatin fa dai dai lokacin Baba ya shigo yace.
"Ni nace ta kawo, ajiye kiyi tafiyarki. “
Ajiyewa ta yi ta juya ta fita, kafin zuwan su Mama Baba har ya farawa Iya bayani da suka zo kuma ya had'u ya d'ora musu bayanin yadda sukai da su Alhj Faruoq, kafin su bud'e akwatin suga meye a cikinta, lesuka ne 'yan ubansu masu matuk'ar kyau da tsada har kala uku, atamfofi ma uku, sai mayafansu da takalma da jaka, Iya murna da farin ciki kamar ta yi me, sai gud'a take.
"Kai Amma wannan yarinya akwai goshin arzik'i, duk inda tai arzik'i binta yake da gudu ya na kamota, gashi har yau mune zamu had'a zuri'a da familyn Fanda, ai abin sam barka ne wannan.“
Umma kuwa bak'in ciki kamar ta yi me kawai yak'en dole take don kar ace ta na bak'in ciki, Mama kam shiru tai ba tace komai ba, Babane yacewa Mama.
" ga su nan ki ajiyesu kar tai amfani da su, har sai yaron yazo sun fahimci juna, idan ta aminta da shi to, idan ba ta so ba zan mata dole ba, don haka kece mahaifiyarta ke kika san ta yadda za ki biyo mata. “
"Ai ta aminta da shi ma Audu, wace sakaryar ce za ta k'i zuk'ek'en saurayi d'an gidan Fanda, ga kyau ga kud'i ga ilimi ga kuma ladabi da biyayya, ko ni da nake tshohuwa wallahi ya na mugun birge ni, ai ku kwantar da hankalinku aure kamar anyishi an gama. “
Baba baice komai ba ya yi musu sallama ya tafi kasuwa, sai Umma ce tace.
"Iya dama kin sanshi ne? “
"Inma ban sanshi ba tun da ya na son jikata aikwa saninsa ya zama dole. “
Shukhura da Nusrat suka d'ago suka kalli mahaifiyarsu bayan sun gama kallon kayan suka had'a baki gurin fad'in.
"Mama kayan waye to?“
"Naki ne Shukhura. “
"Nawa kuma Mama?“
Ta fad'a ta na kallon fuskar Nusrat kafin ta mayar dubanta kan Maman, ita kuma tai musu bayani kamar yadda Baba ya yi mata ta d'ora daa.
"Ba dole za'a miki ba Shukhura, ba kuma za'a tab'a musu kaya ba har sai kun fahimci juna kin kuma aminta da shi, sunzo sun nemi izini ne sun kuma kawo kayan na gani ina so.
Ki tsayar da zuciyarki guri d'aya, kada dukiyarsu ta rud'e ki ko wani abu na k'yale² idan har bai kwanta miki a rai ba, ki same ni ki gaya mini ni kuma zan gayawa Babanku sai a mayar musu da kayansu a basu hak'uri.“
D'aga kai kawai Shukhura ta yi ta na sunkui da kai k'asa, Mama ta mayar da kallonta ga Nusrat tace.
"Yayarsu babu wani wanda ya tab'a tunkararki da zancen soyayya ne?“
Kai tsaye tace.
"Eh babu Mama. “
Shukhura ce tai saurin d'ago kai ta kalli Nusrat d'in yayin da Nusrat d'in ta galla mata harara, ganin hakan da Mama ta yi ne yasa tace.
"Gaya mini Shukhura waye? In ita kunya ta hana ta fad'a. “
"Babu kowa Mamanmu. “
Shukhura ta bata amsa.
"To shikenan tun da ba za ku gaya mini ba, idan Babanku ya dawo kwa gaya masa, Allah dai ya had'aku da mazaje na gari.“
Suka amsa da. "Amin." A tare.

Da yamma Hajiya Suwaiba tazo gidan su Shukhura, Mama tai mata tarb'a ta mutumci da girmamawa dai² da k'arfinsu, yayin da Hajiya Suwaiba take ta yabawa da karamcinsu, ta kuma samu sirikartata 💯.
Kayan kwalliya ta kawo mata tace ita da 'yar uwarta, don Mustafa yace mata ya na jin fa 'yan biyu ne, Inna kuwa daga jin haka har ta fara murnar za'a haifo musu tagwaye.
Tun daga kan mayuka na gyaran fata babu abinda babu a ciki, godiya sosai Mama tai mata, ta rakata gurin Iya suka gaisa, Iya yadda kuka san ta gurfana a gabanta tai mata sujjada aikwa da ta tashi tafiya ta ajiye mata then thauthand, murna gurin Iya ba'a magana ta taho filin tsakar gidansu ta na ta rangad'a gud'a ta na shiwa Mama albarka don ta iya haihuwa tunda ta haifo Shukhura jinin arzik'i.
Umma na d'aki takaicin duniya ya bi ya isheta, wani malulun bak'in ciki ne ke damunta, yanzu ta na gani su Maimuna zasu fandama cikin daula, don had'a zuri'a da Familyn Fanda kamar ka tako arzik'i ne, haka za'a mashaheta bora a cikin gidan nan da ita da 'yarta, don Shukhura ba kunya ce da ita, idan ta auri jinin Fanda kanta zai k'ara girma ta kuma taka wanda taga dama, tazo ta na d'agawa k'arshe ma komai na gidan ya dawo hannunta, da ace Nusrat ce ta san ba ta da matsala za ta dubeta tamkar mahaifiyarta, Shukhura kuwa babu abinda take hanga cikin idanuwanta banda tsantsar taya mahaifiyarta kishi, idan kwa ta samu wannan power ta riga ta zama sorry a cikin gidan nan daga ita har 'yarta, don haka dole ne ta nemi mafita tun lokaci bai nemi k'ure mata ba.
Chapter 11 · 0% Book details