Sashe 6
Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read
A cikin mota Nusrat ta samu Yaa RJ, tun fitowarta yake sakar mata murmushi ta cikin gilashin motar har ta k'araso gaban motar, a bud'e murfin motar yake don haka ta shiga ciki ta zauna suka had'a ido da Hidaya da ta juya ta koma cikin gidan.
Shiru ne ya biyo baya sai kanta da ta sunkuyar k'asa ta na watsa da yatsan hannunta, yayin da shi kuma ya kafeta da idanuwansa, ya na jin wani sabon yanayi a kanta, ya san Nusrat yarinya ce ta yi k'ank'anta ya furta mata kalmar soyayya, amma ya na jin tsoron ya dawo ya tarar wani ya riga shi nasarar karb'ar soyayyarta, sanyin halinta, yanayin tafiyarta, yanayin maganarta komai ya yi dai-dai da yadda yake son matarsa ta kasance.
"Ina wuni Yaaya?“
Nusrat ta katse shirun da yake tsakaninsu ta kuma katse shi daga tunanin da ya tafi, rintse idanunwansa ya yi ya busar da wata iska mai sanyi saboda yadda muryarta ta shiga jikinsa ta zauna, wani siririn zoben azurfa ya ciro daga d'an k'aramin yatsan hannunsa.
"Muga hannunki. “
Zara zaran yatsunta ta mik'a masa ya zira mata a yatsanta na kusa da babban yatsa.
"Daga nan kaduna zan wuce ta nan jirginmu zai tashi zuwa Uk nan da shekara uku zan kammala karatuna na dawo, ki mini alk'awari ba za ki bawa ko wani saurayi damar k'ulla soyayya da ke ba. “
Ba ta gane inda maganarsa ta dosa ba, don haka ta tsira masa idanuwanta kamar me karantar amsoshin tambayoyin da ke dank'are a zuciyarta, yayin da shi kuma yake jin kallon da take masa har tsakiyar zuciyarsa.
'Meye dalilin da yasa ka bani zobe, me yasa zan maka alk'awarin k'in kula ko wani saurayi bayan ba ni da tabbacin sona kake,
idan ma sona kake anya auranmu zai yuhu kuwa, kana ganin Aunty Maryam za ta bar Katangar alak'ar da take ginanna a tsakaninsu taci gaba da ginuwa?'
Wa'yannan tambayoyin sune cunkushe a ranta amman ta k'asa furta ko da kalma d'aya, ji take bakinta yai mata matuk'ar nauyi.
Hannunta ya matsa had'e da fad'in.
"Pls Nusrat. “
Tsintar kanta kawai ta yi da d'aga masa kanta, ya saki kyakkyawan murmushi, ya d'auko wata leda ya d'ora a kan cinyarta.
"Na gode Nusrat, Allah ya baki ikon cika mini alk'awarina, bari ni zan wuce, ki gaida mini da su Mama. “
"Za su ji insha Allah, Allah ya kaika lafiya, ya kuma baka sa'a akan karatun naka.“
"Aminnnnn“
Yace yana me jin dad'in addu'arta yayin da ita kuma ta fice ba tare da ta d'au ledar da ya ajiye mata ba, murmushi ya yi don ya san za'a rina, a dai-dai lokacin Shukhura ta fito ta na zunb'uro baki, da hannu ya yafitota tazo gareshi, d'an risinawa ta yi ta gaisheshi yace.
"Ga leda nan d'auki ki kaiwa Mama kice ina gaisheta.“
"Tom, an gode. “
Ta d'auki ledar shi kuma ya ja motarsa yai gaba.
_RIDWAN JIBRIL shine cikakken sunansa yayin da ake masa inkiya da RJ, mahaifinsa da Yusuf mijin Aunty Maryam uwarsu d'aya ubansu d'aya, mahaifinsa ya rasu tun ya na yaro a gurin mahaifiyarsa yake da take aure a kaduna, tun bayan auran Yusuf da Aunty Marya ya d'auko RJ ya dawo gurinsa da zama suka rik'eshi tamkar d'ansu na cikinsu, bayan gama karatunsa na_ _secondary ya turasa Uk acan yake had'a karatunsa a fannin jarida._
_Hidaya da Nusrat tasu tazo d'aya sosai, suna k'aunar junansu hakanne yasa Nusrat take yawan zuwa hutu gidansu, yayin da shak'uwa me k'arfi ta shiga tsakaninta da Rj, har ta rikid'e ta koma soyayya a zuciyar RJ, idan har zaije kaduna gurin mahaifiyarsa sai ya fara tsayawa gurin Nusrat ya yin da k'arara Aunty Maryam ke nuna ba ta son alak'arsa da Nusrat saboda akwai wani buri da suka ci a kansa ita da mai gidanta._
Kwata² Shukhura tak'i yadda ta shiga ko gurinsu, ta na filin babban tsakar gida a zaune ta na dakon zaman jiran Baba ya dawo, don kada ma Mama ta hanata aikata abinda tai niya, ledar da RJ ma ya bata a bakin k'ofar d'aki ta ajiye ta fito don duk kada Mama ta ruguza mata shirinta, ta san dai duk tsiya Baba bazai wuce 12 na rana bai dawo ba saboda ba a gida ya kwana ba.
Har kusan k'arfe d'aya Baba bai shigo cikin gidan ba, har ta fara tunanin tashi ta jiyo takun tafiya don haka ta maida idanuwanta kan k'ofar shigowar, aikuwa Baban ne ya yi sallamar ta amsa masa ta nufeshi had'e da d'ora damuwa akan fuskarta, har da fara taro k'walla, gaban Baba ne ya yanke ya fad'i yace.
"Lafiya Shukhura me ya faru? “
"Baba.“
"Na'am fad'a mini me ya faru? “
"Dama kullum Mama ce ke hanani gaya maka.“
"Ina jinki.“
"Duk ranar girkin Umma ba ta bamu abinci ishashshe, da kai da Iya da su ta ciccika muku kwano, kuma har d'anye take ragewa ta b'oye, to yau da safe ba ta toya mana k'osai ba zallar kunu kawai ta dama, ta bawa Nimha ta sayo musu su da Iya. “
Ran Babane ya yi mugun b'aci, ya tabbata Shukhura ba za tai masa k'arya ba, shafa kanta ya yi yace.
"Jeki ciki zanwa tufkar hanci. “
Cike da murna ta shige ciki ta na jin kamar ta sauke abu me nauyi a zuciyarta ko kad'an ba ta damu da hararar da Mama ke ta zabga mata ba.
Sai da ya bari Umma ta gama girki ta raba kowa ta kai masa shima ta kawo masa nasa sannan ya k'wallowa Shukhura kira, ta amsa ta fito da saurinta.
"D'auko mini abincinku.“
"Toh."
Tace da hanzari ta juya ta d'auko.
"Jeki ki anso mini na Iya. “
"Ai yau Iya ba ita kad'ai bace su Aunty Maryam sun zo. “
"Af na sha'afa, da na shiga gurin Iyanma mun gaisa, bar na tan. “
Ya dubi Umma yace "D'auko mun naku, kuma bance ki rage komai ba, inma kin rage da kaina zanzo na duba.“
Tsuru² Umma ta yi da ganinta ka san ba ta gaskiya taje ta d'auko ta kawo masa duban Shukhura ya yi yace.
"Je ki d'aki, ki turo mini Mamanku. “
Shukhura na barin gurin Baba ya dubi Umma yace.
"Yanzu wannan adalci kenan? Kalli abincin da rai d'aya zai ci, ki dubi na rai biyu duk sun taka wanda rai hud'u zai ci kinwa kanki adalci? Ko iya Nimha kad'ai ai sai ta tashi da wannan abincin, idan ni ba na gani ai Allah ya na ganinki kuma hakk'insu bazai tab'a barinki ba. “
Fad'a sosai Baba ya shiga yiwa Umma kamar zai ari baki, ya shaida mata muddun ta kuma irin rabon nan to sai ta bar masa gidansa, Mama da tazo fad'an ya rufe ta da shi akan me za ta hana a gaya masa irin haka na faruwa a cikin gidansa ya d'au mataki tunda ita ba ta gaya masa ba, ita dai Mama hak'uri ta bashi don sosai Baba ransa ya b'aci, ranar huni ya yi ya na surfawa Umma fad'a, abincinma ya yi zuciya ya k'i ci ya juyewa su Shukhura akan nasu na su Umman ma ya datsi rabi ya k'ara musu akai ya kira Shukhura ta d'auka, Umma kuwa sai huci take kamar ta janyo Shukhura tai ta jibgarta.
_____________
Bayan sati guda Baffa Shamsu yazo garin zariya, a lokacin su Aunty Maryam sun koma kwana uku sukai suka tafi.
Transfer yake nema zai dawo zariya gaba d'aya hakanne yasa yazo don neman gidan da zasu samu su zauna, duk da nan kusa da gidansu an masa tallansa to dai ya na son siya amman dai ba su gama cininki ba, tun zuwansa Iya tace.
"Nidai yau aradu shinkafar gwamnati zanci, don wallahi na gaji da cin shinkafar hausa ina karo da tsakuwa ta na farfasa mini hak'ori, kalli nan kaga yadda duk hak'orina ya farfashe, don haka ma ni wallahi in za ka tafi binka zan, don na gaji da cin tuwon masara kullum da daddare na kwanta, gara a dinga dafa mini taliyar nan ta gwamnati me dad'in gaske.“
Murmushi kawai Baffa Shamsu ya yi yace.
"Haba Iya ba na son kina irin wa'yan nan
magan ganun kema dai kinsan Yaya yana matuk'ar k'ok'ari, idan yaji abinda kike cewa bazai tab'a jin dad'i ba.“
"To kar ya ji dad'in mana ni ina ruwana, wani k'ok'ari yake banda son 'yarsa da ya fifita a kaina. “
Ko me ta tuna kuma sai tai shiru kana tace.
"Mubar ma maganar d'an arzik'i maza je ka siyo mana shinkafar, ka kuma siyo mana kaji don yau mu d'an wasa bakinmu, don rabona da ci nikam ina jin tun kan rasuwar Malam. “
Girgiza kai kawai Baffa Shamsu ya yi ya na mamakin halin mahaifiyar tasu sam ba ta da godiyar Ubangiji, duk zuwan da zaiyi sai sunci kaji a gidan, haka zalika Baba ma idan ya ji aljihunsa da nauyi ya na siyo musu su ci amma wai kunji rabonta da ci tun kan rasuwar Malam.