Sashe 7
Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read
Buhun shinkafa biyu da katan na taliya da macaroni biyu Baffa Shamsu ya siyo musu ya ajiye su a d'akin Mama, ya siyo musu kaji guda biyar manya ² gashi kuma aka taki sa'a girkin Umma ne, don haka Shukhura ta na da 1000 tace bari taje titi ta siyo don ta san 'yar kad'an za'a sanmusu, Nusrat ma na da 1000 sai ta bata ta siyo musu guda biyu kuma manya da su.
Ilai kuwa cinya d'aya fukafiki aya sai wuya aya aka saka musu, ko kad'an ba su damu ba Shukhura ta wanke nasu ta tafasa ta fara suya.
K'amshin suyar naman Iya ta ji a ranta tace kaddai matar nan ragewa ta yi take soyawa da hanzari ta fito don ta ganewa idonta, ganin Shukhura ce me suyar ta kai hannu za ta d'auka a cikin wa'yanda ta kwashe, Shukhura ta yi saurin d'auke robar hannun Iya ya sauka a k'asa har sai da ya yi k'ara tace.
"Auchhhhh“
Don ta ji zafi sosai, Shukhura kuwa ko a jikinta ta murgud'a baki tace.
"Ai ba taku bace, wannan tamu ce naje na siyo, da za ki d'auko yamutsats tsan hannunki ki saka mini a ro....“
Ba ta k'arasa ba taji saukar mari a kuncinta, dafe kuncin ta yi ta tsaya ta na kallon Mama da ta fusge robar naman a hannunta ta d'auki cinya manya² guda biyu ta bawa Iyan, sai da Iyan ta ansa kana ta tab'e baki.
"Ai da ba ki daketa ba ai na san duk makirci ne irin naki, ke kitsa mata dukkan abinda takeyi a gidan nan, amma ai Shamsu yazo zai mini maganinta. “
Ta na kawowa nan ta fice daga gurin Shukhura ta bita da d'an iskan kallo, Mama ba ta iya cewa komai ba ta koma d'aki Shukhura ta k'wallowa Nusrat kira.
"Yayarmu zo ki kama mini na shiga band'aki. “
Nimha tace.
"Kawo na miki kan ki dawo. “
"Don aji dad'in d'iba akai d'aki ba, a'a basshi na gode ga Yayarmu nan za ta ansa. “
Umma ta gallawa Nimha harara.
"Maganin shishshiginki kenan ga shinan an gab'a miki magana.“
Memakon Shukhura ta shiga band'aki sai ta fice ta yi gurin Iya.
"Kina ina yau in kinci naman nan ba Mama ce ta kawoni Duniya ba. “
Iya na jin haka ta yi saurin nad'e shi a leda ta saka a k'ark'ashin gado, dama ajiyeshi ta yi sai ta gama da na cikin miyar.
A bakin k'ofa ta cage tace.
"Ki fitomun da namana.“
Sai ki d'auka in kin ganshi ai. “
Bin d'akin tai da ido ta na nazarin inda Iyan za ta ajiye naman, ganin kamar idon Shukhuran ya na sauka a k'ark'ashin gado Iya ta yi saurin d'aukewa ta mik'e tsaye.
"Sai kizo ki k'wata in baki da kunya. “
Kanta Shukhura ta yi gadan² ta kama hannunta za ta murd'e.
"Ke ke ba ki da hankali wai. “
"Eh bani da shi d'in, ta d'auka ta baki naman sannan ki yab'a mata magana kuma kici alqur'an ba ki isa ba. “
Taci gaba da k'ok'arin k'watar naman dai-dai nan Baffa Shamsu ya shigo.
Kyakkyawan maruka ya saukewa Shukhura kana ya tambayi ba'asi Iya ta koro masa bayani, hararar Shukhura ya yi da ke tsugune dafe da kuncinta.
"Dama ance ba ki da kunya to yau zanyi maganin rashin kunyarki. “
Ya zari cagar radio ya yo kanta ta saki ihu ta yi bayan Iya dai- dai lokacin ya kawo mata duka ya sauka a jikin Iya, Iya ta zunduma ihu tsabar azaba.
"Shamsu ka rabu da yarinyar nan dan Allah kar ka daketa, bai saurari Iya ba ya b'anb'aro Shukhura daga jikinta ya hau zuba mata wayar ko ta ina, aikwa ta bud'e murya ta dinga zunduma ihu, Mama ko motsi daga inda take ba tai ba, kuma ta hana su Nusrat zuwa, tace ai gara taji a jikinta gobe ma ba za ta sake ba, Umma kuwa da gudu ta nufo gurin ta na shewa dama a ciki take da ita.
Sai da ya yi mata lilis sannan ya k'aleta,ya fice, Iya na gefe ta na ta matsar k'walla don ta san yau kashinta ya bushe gurin Shukhura, yayin da Umma ke ta shewa ta na fad'ar magan ganu.
"Yau dai an mana maganin mara kunyar gidan nan, aiyiri yiri yiri yiri. “
Wani kukan kura Shukhura ta yi ta saki wani ihu ta yo kan Umma da gudu, tsoro ne ya kama Umma ta mik'e za ta fice ta yi tuntub'e ta fad'i, yayin da Shukhura ta shiga aljanun k'arya ta dinga cin uban Iya da Umma da sanda dukkanninsu sun jigata sosai, har sai da Mama tazo ta janyeta, suna shiga d'aki ta fashe da dariya a ranta tace.
'Saura Baffa Sham sun.'
Mama kuwa zuba mata ido kawai ta yi, don ta d'auki alk'awarin ta daina dukanta daga yau, addu'ar nan ita za ta cigaba da yi mata anai mata rubutu ta na sha.
Da jan jiki Umma ta samu ta komo gurinta, ta na jin mugun shakkar Shukhura a ranta, Iya kuwa kuka ta dinga rusawa don yau babu abinda zaisa ta kwana a cikin gidan nan Shamsu yazo su tafi Kaduna ta wuta da wannan jaraba da masifar da Audu ya haifa.
Hankalin Shukhura bai kwanta ba har sai da ta sakawa Baffa Shamsu cinnaku biyar manya² a riga ai kuwa ya sha muguwar azabar da ta wuce dukan da yai mata.
300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.
Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.
Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.
#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*
Wattpad@Rashuna
*KATANGA*
____________
*SIX*
Ta b'angaren Alhj Faruoq Fanda kuwa ya na zuwa gida ya sanar da matarsa Hajiya Suwaiba wata yarinya ta yi wuff da zuciyar yaronsu, farin ciki tsanta H.Suwaiba ta shiga had'e da fad'in "Wata yarinya ce wannan mai matuk'ar sa'a Alhaji?“
"Ai ban baro gurin saukar nan ba sai da na saka aka samo mini bayanai a kanta.
A nan unguwar cikaji suke zaune, mahaifinta ba wani mai hali bane sai dai rufin asiri na Ubangiji, itace 'ya ta biyu a gurinsa, ta na matakin aji biyu a sss, an shaidu 'yan gidan gaba d'ayansu da tsantsar tarbiya, sunanta na gaskiya Safiyya, amma da Shukhura ake kiranta.“
K'awataccen murmushi H.Suwaiba ta saki tace.
"Kai amman na ji dad'i, Allah yasa itace abokiyar arzik'insa, ai banda hidimar saukar nan da muke ta Maryam da ba abinda zai saka ni zuwa naga sirikata a yau.“
Murmushi Alhj ya yi yace.
"Don zumud'i irin naki, gobe in sha Allah dai zamu je gaisuwa, da kayan na gani ina so, don har ga Allah na yaba da zab'in yaron nawa, don dama ina gudun ya d'auko mana irin wayayyin yaran nan marasa tarbiya, fatanmu dai Allah yasa ba maganar wani a kanta.“
"Amin., amma ka dai sanar da Hajiya Inna ko, don gara a gaya mata tun wuri za'a yo mata kishiya. “
Ta kai k'arshen maganar ta na dariya, dariyar shima Alhajin ya yi yace.
"Ita ai na fara gayowa ta na nan ta cika fam ta na jiran shigowarsa, na san yau dai ba za'a bashi abinci ba nan za'a koro mana shi. “
Alhj Farouq Fanda asalinsa d'an garin Fanda ne, neman kud'i mahaifinsa yazo yi tun Farouq na yaro, a garin kano suka fara zama ya na yin kasuwancinsa kuma Allah yasa masa albarka a ciki, nan da nan ya tara dukiya me d'imbin yawa, Farouq shi kad'ai ne d'ansa wannan dalilin ne yasa ya bashi gata mai yawa, ranar da Faruoq ya gama karatunsa na shari'ah a ranar mahaifinsa ya rasu, sunyi kuka iya kuka da shi da mahaifiyarsa Fatima (Hajiya Inna. )
Bayan rasuwar mahaifinsa ne dukiyoyinsa duk suka dawo k'ark'ashinsa, sannan kuma ya fara aiki a matsayinsa na babban alqali, nan da nan dukiyarsa ta kuma bunk'asa, ga kuma harkokin kasuwancin mahaifinsa hakan ne yasa ya nemi mataimaka kuma ya samu masu aminci, daga kano suka tarkata suka koma zariya da zama a unguwar sabon gari, gida ya dank'ara ba na wasa ba, ya yiwa Hajiya Inna sashinta da ban, zuwansa zariya anan ya had'u da Hajiya Suwaiba suka fara soyayya itama 'yar garin zariyan ce anan unguwar cikaji, ba'a d'au wani lokaci ba akai bikinsa da Suwaiba, Hajiya Inna na mutuk'ar k'aunar sirikar tata, ko kad'an ba ta san wani mugun hali na uwar miji da ake fad'a ba, ta rik'eta tamkar 'yar cikinta, wannan dalilin ne yasa tai alqawarin idan Allah ya azurtata da 'ya'ya maza za ta k'aunaci matansu kamar 'ya'yan cikinta, don a ganinta babu bambamci tsakanin d'anka da sirikar taka tunda an riga an zama d'aya.
'Ya'ya biyu Allah ya azurtasu da su, Mustafa,sai Maryam, sunga gata sosai gurin mahaifan nasu.
Mustafa Faruoq Fanda, wanda abokansa ke kiransa da Fanda ya kammala karatunsa na low har ya zama Barrister mai zaman kansa, komai na shi na rayuwa a sashin Hajiya Inna yake don ta na matuk'ar k'aunarsa, Maryam kuwa rayuwarta ta fi k'arfi a gidan kakanninta na uwa acan cikaji, da yake suma da rufin asirinsu, zamanta a cikaji shiyasa islamiyarsu tazo d'aya da su Shukhura, ba ajinsu d'aya ba, da yake aji biyu ne aka had'e akai saukar, itama Maryam ta yi candy ta na jiran sakamako don ta d'ora daga inda ta tsaya.
Wannan kenan.