← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 69

Sashe 38

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna gamawa suka jere komai akan dining kana kowa ya nufi d'aki don jin ana kiran sallar magariba, wanka Nusrat ta fara shiga tayi kana ta d'auro alwala, sai da ta fara gabatar da sallar magariba kafin ta auko vaselin inta ta shafe ko wani loko da sak'o na jikinta, don haka Nusrat take ko ina na jikinta sai ta shafeshi da mai musamman lokacin sanyi ko kad'an ba ta bari fatarta ta bushe ko alwala ta d'aura sai ta kuma shafe jikinta da mai, kallonta Hidaya take tana daga kwance akan gado tana chart, kasancewar hutun sallah take, gyaran murya tayi, wanda hakan yasa Nusrat in ta d'aga kai ta kalleta kafin Hidayan tace.

"Yayarmu kinji dad'inki wallahi, fatarki tana da mugun kyau, har wani glowing take,wani rantsewa zaiyi da desighners mayuka kike amfani nan kwa bai san vaselin ne manki ba ainihin fatarki ce da Allah ya baki, kika fara amfani da mayukan gyaran fata ban san kuma ya zaki zama ba ."

"Kai Hidaya, kema fa fatarki tana da kyau, ta ma fi tawa shek'i."

"Haka dai kika ce, kuma ni ai da taimakon mayukan da nake amfani da su shiyasa, kema so nake mu gama paper nan na anshi kud'i gurin Daddy muje shoppin kina buk'atar abubuwa da dama, kuma nace ki dinga amfani da nawa kink'i."

Takai k'arshen maganar tana gallara mata harara, dariya Nusrat in tayi tace.

"Sorry, mantawa nake yi wallahi, na riga na saba using da nawa ne."

"Hmmmm ke dai kika jiyo, ai jibi zamu zana takaddar k'arshe gata kuwa shoppin zamuje, kan nan naki ma ware shi zaki muje saloon a wanke miki shi sai ai miki stratchine tunda ba kya yin shampoo, kefa Yayarmu ba matar k'ananan mutane bace wallahi, kalarki irin ta hamshak'an masu nairan nanne wanda ake kira young biloniars (mijin novel)shiyasa naso ki fara scl yadda zaki kuma gogewa ki kece raini."

Murmushi Nusrat in tayi kafin tace.
"Allah dai ya had'amu da mazaje na gari amin."
Ta fad'i hakan don kawai ta kautar da maganar schl in da ta jefo.

Hibba ta riga kowa zama a dining, sanda duk suka fiffito lokacin a plate na biyu take, Daddy ne yace.

"Kaga su Hibba, yau mutuniyar aka dafa miki ne?"

"Ai Daddy gaba d'aya gidannan yau aka yita, tayi mugun dad'i wallahi, a plate na biyu ma nake."

A dai dai nan Mommy ta bud'e wamars in da macaronin ke ciki a tare duk suka yatsuna fuska yayin da Hidaya ta hurgawa Hibba hrara had'e da fadin.

"Ba dole kiji dadinta ba tunda kina sonta, abinda baka so baza ka taba jin dadinsa ba ai."

"Sai dai in baiji had'i ba kuwa."
Ta fad'i hakan tana dariya k'asa k'asa.

Daddy dai cewa Mommy yayi yar kad'an za tayi serving nashi, itama kad'an in ta zuba Hidaya dai cika plate tayi saboda yunwar da take ji zata daure ta cusa haka, kuma da alamu kidney sourc in zata saka macaroni shiga saboda sai zuba k'amshi take, Abdul ma dai to ba laifi wacce ya zuba, kallon Momy Hibba tayi tace.

"Mommy ba ki saka muku wannan ba."
Takai k'arshen maganar tana nuna American Garden, U.S. Mayonnaise, 'yar tsuka Mom ta ja had'e da fad'in.

"Ni ke rabu da ni, macaronin ma sai an mata wani fiili da ban."

"To kai Daddy a saka ma wallahi da mugun dadi."
Ta fad'i hakan tana mayar da kallonta kan Daddyn.
"To saka mini."
Yace da ita, da hanzari ta mik'e ta saka mishi,yana yin one sepun ya fara girgida kai yayin da yayi 3 spun kuwa sai cewa yayi.
"Wai wata irin macaroni ce wannan?"
Hibba na dariya tace.
"Daddy doga ce."
"Kai amma tana da dad'i wallahi, gobe ma da ita zamui dinner."
Dariya Hibba tayi tace.
"Dama Daddy na gaya ma macaroni tana da dad'i sai dai in ba ta ji had'i ba, ba kaga su Aunty Hidaya ko magana baai ba ana ta ziri, momy kuwa har k'arawa tayi."
Takai k'arshen maganar tana tintsirewa da dariya, Daddy sai cewa Momy yayi nima k'aro mun to, basui aune ba Abdul har ya cinye zai kara, Hidaya kuwa ta kusa tashi da wacce ta zuba don ba k'arya girkin yayi mata mugun dad'i, Nusrat ma tayi mata dad'i sosaia ranta sai mamakin Daddy take watakan shi in girki yayi masa dadi washe gari shi zaa maimaita, bayam kammala cin abincinsu Daddy yace Hibba ta biyoshi ta ansar musu kyautarsu don girkin yau ya mugun kayatar da shi..

200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.

#NWA
#KTG
[4/26, 8:43 PM] Rabi: BEBE'ARTH

KTG 23

Kamar yadda Hidaya tace a washe garin da suka gama zana paper ta anshi kud'i hannun Daddynsu suka shirya suka fita, saloon suka fara zuwa aka gyara musu kansu da jikinsu da k'afafuwansu, sunyi matuk'ar kyau ainun musamman ma Nusrat in da ba tab'a yi tayi ba wannan ne karonta ba farko sai fuskarta tayi wani irin haske na ban mamamaki wanda ya k'ara fito da zallar kyahunta, daga saloon in sai suka huce shopping mall, Hidaya ce ta dinga jidar mata duk wani abu da ta san tana da buk'atarshi, bayan ta gama ta kalleta tace.
"Idan akwai abinda kike so a ranki ban d'auka ba ki d'auka."

Murmushi tayi had'e da fad'in.

"Ai kin riga kin gama d'aukar duk wani abu da nake da buk'atarsa."

Da sukaje b'arin under wears ne kawai ta d'aukarwa Yusra wasu 'yan k'ananun brezia guda biyu, sai pant ma biyu undis biyu,don suna da buk'atarsu dama sosai bibbiyu ne da su sike lanjarawa musamman ma Yusran pant inta duk sun ragargaje dama siya mata pant in yana ranta da kuma brezia don k'irgar dangin nata sun bayyana sosai, kallon breziar da ta d'auka Hidaya take yi kafin tace wani abu Nusrat in ta rigata da fad'in.

"Yusra na d'aukarwa."

Murmushi kawai Hidayan tayi kafin ta kuma d'aukowa Yusran komai uku suka zama biyar biyar kenan, ko da sukaje gurin biyan kud'i auna kayan nasu kawai akai kana sukace an biya musu da mamaki a fuskokinsu suke tambayar wanda ya biya musu, da hannu suka nuno shi, Nusrat da Hidaya suka juya a tare yana zaune kan kujera ya hard'e k'afafuwansa idanuwansa gaba d'aya suna kan fuskar Nusrat wanda hakan yasa Nusrat in saurin kautar da idonta daga kanshi don tayi mugun tsanar kallo a rayuwarta shiyasa ta d'auko nik'af inta zata saka amman fafur Hidaya ta hanata sakawa, hijabin ma cewa tayi wallahi baza ta saka ba don dole tayi rollin da mayafin doguwar rigar da ta saka wacce Hidayan ce ta bata, sai tayi masifar kyau musamman yanzu da akai musu gyaran jiki da na kai da fuska.

Hidaya ce ta k'arasa gurinsa don jin dalilinsa na biya musu wa'yannan mak'udan kud'i don ba k'aramar siyayya sukayi ba, siyayyar da sukaima ina jin lefan wata ne a yanzu.

Gaisawa sukayi a mutumce kafin ta amayar masa da tambayar da tazo da ita, duk da ta lura da yadda idanuwansa ke kan Nusrat duk da ta juya musu baya.

" Na biya muku kud'ine saboda nauyinku da ya hau kaina a yau yau d'innan, Sunana ISHAQ, k'addarar had'uwata da 'yar uwarki ce ta kawo ni nan, babu k'arya 'yar uwarki ta kama mini zuciya ba kad'an ba nima ina buk'atar a bani damar da zan kamo tata, kuma ina jin da taimakonki ne hakan zai faru ."

Murmushi Hidaya tayi tana jin dad'i a ranta, don a kallo d'aya da tayiwa Ishaq ta yaba da shi.
"To amma tun kan ka samu shiga shine ka d'orawa kanka wannan d'awainiyar kud'in ai sunyi yawa muma da kudinmu muka zo."

Murmushi yayi wanda ya k'ara fito da zallar kyahunsa da k'uriciyarsa a ransa yace, tabbas wannan da ta san waye shi to da ba ta ambaci wannan kud'in da ya biya musu a kud'i ba, ba ta san mall inma gaba aya a k'ark'ashinsu yake ba, amman dai ba yanzu yake son su san shi waye ba sai komai ya dai daita.

"Kada ki damu, na riga na gaya miki a yau d'innan nauyinku ya dawo kaina, damar aikata hakan kawai nake buk'ata, da fatan zan samu?"

" To bazan ce ba amman zan gwada taimakawa."

Wani k'awataccen murmushi ya saki kafin suti exchang in number ya d'ebo rafar 'yan dubu ya bata tak'i amsa, babu yadda baiyi ba amman tak'i amsa don haka ya hak'ura zuwa lokacin kuwa Nusrat ta gaji da tsaiwa ta fice daga gurin, jikin motarsu taje ta jingina tana bin mutanen da suke shiga suna fita da kallo, sai ga Hidayan da Ishaq in sun fito a jere suna hira, tun da suka tunkaro gurin da take a tsaye idanuwansa suke kanta, ta kuma had'e fuakarta guri guda tana k'in kallar gurin da suke tahowa, shikuwa ko wani kallo da yake mata mutuwa yake da soyayyarta da tayi mishi kamun farat daya a kuma kallo d'aya had'uwa d'aya, Hidaya na bud'e motar tayi saurin bud'ewa ta shiga don a takure take da kallonsa, yayin da Hidayan ta bud'e boot ana zuba musu siyayyarsu, yana tsaye yana binta da kallo ba tare da yace mata kanzil ba har aka gama zuba musu kayan sukai sallama da Hidaya taja motar yana tsaye yana karb'ar sabon yanayin dake bak'untar zuciyarsa abinda bai tab'a ji game da wata yarinya ba sai akan Nusrat bazazzagiya.

Suna tafe babu wanda ya tofa komai sai can Nusrat ta numfasa tace.
"Amman saurayin nan naki ya fiya kallo wallahi."
"Saurayina ko saurayinki?"
"Saurayinki mana, naga daga zuwa tambayarsa kika shantake kuna shan hira."

"In saurayina ne to akan wani dalili zai ta kallonki?
Ke yake so, saboda kema ya biya mana wa'yannan kud'in."

"Ni kuma?"
Ta tambaya had'e da zaro idanuwa."
Chapter 38 · 0% Book details