← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 69

Sashe 66

Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun a ranar da suka wuce da Baba ya dinga kiran wayarta ba ta shiga sai a washe gari ya sameta,shine yace ta dawo haka domin yana buk'atarta kusa da shi ainun,ita kuma ta nuna masa baza ta iya tahowa ba tunda dama ba kaita akayi ba aure kawai aka d'aura,kuma Hajjaju tace sai komai ya nutsu za'a zo a d'auketa,yace tunda an riga an d'aura aure,kawai ta tawo shi yana buk'atarta ga Khalil nan zai zo ya d'auketa,ita kuma fafur da Khali in yazo tak'i binsa,shine yayi zuciya ya k'yaleta,duk da azabtuwar da rashin nata yake k'arawa zuciyarsa, bai san da labarin cewar yau d'in za'a kawo ta ba,tun safe da yaje ya dubo jikin Asghar ya dawo ya haye samansa bai k'ara sakkowa ba,sai da Hajjaju ta kirashi a waya da daddaren bayan 'yan rakiyarta sun tafi akan ya sakko tana son ganinsa,tunda ya fara sakkowa daga benan yaji zuciyarsa tana wani irin numfasawa jikinsa ya bashi Nusrat ce kafin idanuwansa su sauka a kanta tana zaune kusa da Hajjaju kanta lullub'e da mayafi,wata sanyayyar ajiyar zuciya ya saki kana ya zauna a saitin kujerar dake kallon wacce suke zaune,har lokacin idonsa yana kanta yana jin yadda zuciyarsa ke yamutsawa tana samun nutsuwa,tun da ya fara sakkowa zuciyarta ta fara dokawa kafin hancinta ya shak'o mata turaransa mai sanyata nutsuwa,wani irin dokawa zuciyarta take da k'arfi tana jin son ganin kyakkyawar fuskarsa da rayi missed kwana biyu.Nasiha Hajjaju tayi musu sosai kafin ta tashi tayi musu sai da safe tayi shigewarta d'aki,tana jin kewar Nusrat d'in,duk da a cikin gida d'aya suke,dad'inta d'aya ma tace a tawo da Yusra su dinga kwana tare don ba ta jin za ta iya kwana ita kad'ai yanzun,Yusra kuwa murna kamar me za ta zauna cikin gida d'aya da Yayarsu za kuma ta dinga shak'ar irin iskar da take shak'a.

Cinyoyinta da jikinta ciwo suke mata sosai,kusan kwana hud'u suna abu d'aya,ita tsoro ya hanata sakar masa jikinta,shi kuma tausayi da raunin da zuciyarsa tayi a kanta ya hana ya mata ta k'arfi,da ya d'auki hanyar za ta fara kuka tana zafi,yana dannawa za ta kauce har cewa take ya bata maganin bacci tasha in yaso sai yayi a haka,yace ina kika tab'a jin inda akayi hakan?Sai a kwana na biyar Allah ya bashi sa'ar maidata cikakkiyar mace,kasancewar duk ta raba zafin,sai abin yazo mata da sauk'i.
Wanka suka fito a tare zuciyar Aashiq fara k'al kamar takadda,yana jin yadda so da k'aunar Nusrat d'in ke k'ara samun guri a zuciyarsa yake zama,ita kwa Nusrat dad'inta d'aya ta wuce gurin,don tasha muguwar azaba,bacci kwa ishashshe ba ta samunta,wani zubin sai ya hak'ura ya k'yaleta tana tsaka da bacci za tajisa yana yayyamutsata,kan na shanunta kuwa da cinyoyinta wani irin azabar ciwo suke mata,tare suka shirya bayan ya busar mata da gashinta ya taje ya had'e mata shi guri d'aya,suka sauko k'asa don yin Break,sun san su Hajjaju sunyi nasu sun gama su kad'ai zasui budirinsu, Yusra ta d'ebo kayanta daga gidan Kawu Iliya,daga shi har Aunty Hafsa ba suji dad'in tafiyarta ba,sai dai ba suce da ita komai ba,tunda sun riga da sunsan shak'uwa da k'aunar dake tsakaninta da Yayarsu ko sun hanata tafiya ma baza ta sauraresu ba. Rayuwa suke mai dad'i da nutsuwa,a kullum jin son junansu suke yana k'ara k'arfi yana neman tik'ewa,ya fahimceta ta fahimcesa sai suke bin juna yadda suke suna kuma samun fahimtar juna,sun kuma sabawa da juna wanda rabuwa baza tazo musu da sauk'i ba,sun riga da sun zamo duniyar junansu. Duk wani abu da Aashiq yasan zai sanya Nusrat farin ciki shi yake,burinsa yaga dariyarta ko farin cikinta,shiyasa yake k'ara gudu cikin jininta wanda ba ta isa ta dakatar da hakan ba don ya zamo jini da jijiyarta,ya kuma yin babakere cikin zuciyarta ko guri d'aya bai bari wanda wani zai samu damar shiga ba,yabi ya cika ko ina amman a hakan kullum k'ok'arin yin abinda zai k'ara shiga zuciyarta yake,bayan bai bar wani fili ba,shiyasa wani zubin takanji kamar zuciyarta zata fashe saboda k'aunar Aashiq, gidansu gaba d'aya ya saka aka rushe aka d'ora sabon gini,phart d'in Baba da ban na Iya da ban,na Baffa Shamsu da ban,sai nasu da ban,ko da sun zo kwana gida, a phart d'in Baba Umma ke zaune ke jinyar k'afarta,da kullum take k'ara baya ba gababa,sai 'yar k'anwarta ce ke zaune ke jinyarta.
Yusra kawai suke jira takaddunta su fito su tafi Lakshdweep,acan dukkaninsu zasu cigaba da karatu yadda zasu fi saurin gamawa suja ragamar company da hannunsu,don ayyukan sunwa Asghar yawa musamman yanzu da yake kamar wani mara lafiya don abinda Baffansa yayi ya tab'asa yadda bakwa zato,duk da Aashiq d'in yana tayasa da wasu abubuwan,damuwar Nusrat yanzu d'aya ce Shukhura,sai yaushe ne za ta waiwayesu?a kullum ne sai tayi kukan rashinta kusa da su,tana so ta dawo garesu ko zata samu damar cika alk'awarin da ta d'aukarwa Mama na kula da su,shiyasa a kullum take jin ciwon rashin sanin me yake faruwa cikin rayuwar Shulhuran,kulkum kukanta da adduarta Allah ya dawo da Shukhura cikin rayuwarsu,rashinta yana mugun tab'ata musamman a 'yan kwanakin nan da take yawan mafarkin Mamansu tana kuma jaddada mata alk'awarin da ta d'aukar mata.

A matse Shukhura take ta kammala exxam d'in da ta rage musu ta taho zariya,burinta da nutsuwarta ta sanya Nusrat da Yusra cikin idanuwanta, don tun kwanaki Hidaya ta gaya mata cewar Nusrat d'in ta bar gidansu ta koma zariya,ta rasa me ya hau kanta ta manta da su,tayi watsi da rayuwarsu,ta manta su d'in jininta ne,Umma kawai take kalla kamar mahaifiyarta Nimha 'yar uwarta,a ranar da suka gama exxam d'in ta,matsawa Mustapha sai ta tafi zariya,babu yadda baiyi da ita ta bari ya kammala aikin da yake gabansa sai su tafi tare tak'i don kuka ta sakar masa bazai gane yadda take jin zuciyarta da ranta ba,hakan da ya gani ne yasa ya cewa Najib direbansa ya kaisu,don babu yadda zaiyi amman zaiyi kewarta ita da Amna,'yar da ta haifa kenan wacce taci sunan Mama,har ta yayeta k'aramin ciki ne yanzu a jikinta,yadda taga gidan nasu ya sauya sai ta shiga wasi wasin ko an siyar da shi ne,don ta kwana biyu rabonta da zariyan,fitowar Baba daga cikin gidan ne ya tsayar da tunaninta,binsa take da kallo kamar wata sokuwa,kafin tace. "Baba" tana fitowa daga motar d'auke da Amna a hannunta,kafin ta murza idonta da d'aya hannunta kar taje gizo yake mata. Waigowa yayi yana kallonta kafin shima yace. "Shukhura."

Tayi murna da farin cikin ganin Babansu yana raye bai mutu ba,inda suka shiga labarin bayan rabuwa,anan take jin cewar Nusrat tayi aure,wasu hawaye ne masu zafi suka biyo kuncinta,tana jin zafi da rad'ad'in yadda ta rasa abubuwa masu muhimmanci cikin rayuwar 'yan uwanta,ko dawowar Baban nan yaci ace ta sani,yaci ace wani ya kirata ya sanar da ita,amman da yake burin Umma kawai tayi ta turo mata kud'i sai ta manta da ita,ko Nimha ma yaci ace ta kirawota ta gaya mata,anan ta bar Amna tana ta zubawa Baba surutu shi kuma ya biye mata,yana jin ina ma Maimuna na raye tazo taga jikarsu mai kama da ita sak,ba iya sunanta taci ba har kamannin nata ta d'ebo,duk da yaga jikoikinsa na gurin Nimha sai yake jin wannan d'in ta daban ko dan ita d'in jikarsa ce shi da Maimunansa? D'akin Umma ta shiga dake ta fama da k'afarta da kullum cikin d'orata ake tana gocewa gashi tayi wani irin kumburi na ban mamaki,tana shiga d'akin kawai ta rufe Umma da duka ko ta ina,ko lura da ciwon k'afarta ba tayi ba ta dinga tattake k'afar, don yadda take jin zuciyarta babu abinda baza ta iya aikatawa Umman ba, ta saka tayi asarar abubuwa da dama wanda ba ta isa ta mayar da su ba, zuwan Yusra kawai take tunawa sanda Mamansu na asibiti, ihunta da Babaya jiyo ne ya nufo d'akin da hanzari,don har Asma'u me jinyar Umman Shukhura ta had'a tana jibga,da k'yar Baba ya janyeta yana tambayarta abinda ya faru. "Gata nan Baba,ta gaya maka da bakinta abinda tamun ta raba ni da 'yan uwana."
Chapter 66 · 0% Book details