← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 69

Sashe 53

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jiki a sanyaye ya fito daga kicin in, bayan ya ajiye key in kan teburin cin abincin da ke kicin in, ganin ya fara taka matattakalar benensa yasa Nusrat sakin ajiyar zuciya me nauyi me kuma k'aramin sauti kafin ta juya ta nufi bedroom insu itama, ji yayi kamar wanda aka tasa daga bacci, kamar wanda akewa kira yabar abinda yake aikatawa ya koma wani, ji yadda yake jin ya muzanta saboda 'yar k 'aramar yarinyarnan tasan abinda yake aikatawa, ina ga mahaliccinsa, shin ya manta yana kallonsa a duk sanda ya d'aga kwalbar giya ko ya shak'i cocaine, ya manta da in ya b'oyewa mutane bai isa ya b'oyewa mahaliccinsa ba, kaico kaico ina tunani da hankalinsa ya tafi ya manta da duk wa'yannan, bazai iya tuna da yaushe ne ma hannunsa ya fara tab'a kwalbar giya ba, inama inama inama baya za ta dawo da ya gyara kuskuran da yayi a baya, da bai gurb'ata rayuwarsa da shan kayan maye ba, da bai bari tunaninsa ya kunce masa ba har ya manta da Qur'ani shine maganin damuwa ba abin gusar da mayen da zai cutar da kai wata rana.

A wannan dare ganawa yayi da Ubangijinsa sosai yana istigfari da neman dai daito cikin rayuwarsa kafin ya d'auki Qur'ani ya fara karantawa bai san sailin da bacci yayi gaba da shi ba har ya kusan makara a sallar asuba, sai dai ya tashi da matsanancin ciwon kai wanda ko masallaci bai barshi yaje ba sai anan yayi sallar a daddafe kana ya koma gado ya kwanta don zazzpab'i ya fara rufeshi.

Bayan sunyi sallar asuba komawa tayi baccinta saboda ba da wuri suke karyawa ba shiyasa take komawa bacci sai k'arfe takwas ta tashi ta hau aiki,yanzunma k'arfe takwas in ta tashi, zuwa sha d'aya da rabi ta kammala komai har wanka tayi kana suka zauna a dining yin break fast, har suka kammala Aashiq bai sakko ba, da wuya kuma har su kammala bai sakko d'in ba wani zubin ma yakan rigasu zama akan dining in, kallon Nusrat Hajjaju tayi had'e da fad'in ‘’Ki shirya mishi nasa ki kai masa, ina jin dai ba lafiya ba.‘’
"Tom"Tace kafin ta d'auko babban tray ta had'a masa break fast in nasa a kai, had'e da tea in da ta dafa masa da garin maganin da Asghar ya kawo mata jiya, ta tace shi tsaf ba za kace da garin magani aka dafasa ba, kafin ta d'auki tray in ta haura sama, akan dining ta ajiye kana ta fara gyara falon duk da ba wani datti yayi ba kafin ta k'arasa jikin k'ofar bedroom in nasa ta fara knocking, gajiya tayi da tsaiwa don ko alamun motsi ba ta jiyo ba bare kuma gyaran muryar da yakan yi mata wani zubin in yana toilet, d'an bud'e k'ofar tayi a hankula tana huhhurga idanuwanta ta inda za ta ganshi ba taga komai ba don haka ta k'arasa bud'e k'ofar ta shigo a hankula sai da ta kawo tsakiyar d'akin kana ta hangoshi a tsakiyar luntsumeman gadonsa ya rufa da bargo gaba d'ayansa juyawa tayi da niyar barin d'akin kafin taji muryarsa cikin yanayi na ciwo yace.
"Taimaka ki had'an ruwan wanka."
Juyowa tayi har lokacin yana rufe bai bud'e fuskarsa ba, kamar ta tambayeshi bashi da lafiya sai dai ta ja bakinta tayi shiru ta nufi toilet in nasa.

Sai da ta had'a ruwan ta bar d'akin kana ya yaye bargon ya fito sai had'a zufa yake da alama zaxzapb'in ne ya sauka, wanka yayi ya yo brush kana ya fito, sai da ya goge ruwan jikinsa kafin ya shafa mai da turarukansa masu k'amshi da matuk'ar tsada, kana ya fito don a gaggauce yake komai cikinsa ya fara kiran ciroma idan ba gizo irin na hancinsa ba har k'amshin girkin Nusrat in yake jiyowa daga d'akin, baiyi tunanin samunta a falon ba amman yana bud'e k'ofar cikin idonta idanuwansa suka samu masauki zuciyarsa ta matse guri d'aya, ganin tray da yayi akan dining yasa shi nufar can, ashe dai hancinsa ba k'arya ya jiyo masa ba, a hankula ta mik'e ta bi bayansa, tana gama serving insa ya kalleta yace. "Thanks" Ko kad'an ba tayi zato ba ba tayi tsammanin jin wannn kalmar daga bakinsa ba, murmusshi ne ya kubcewa fuskarta don haka tayi saurin juyawa don kar ya gani sai dai kaish ta makaro don ya riga ya gani har yayi sanadiyar saukar da murmushin a tasa kyakkyawar fuskar yana bin bayanta da kallo cikin wani yanayi mara misaltuwa wanda umarni daga zuciyarshi ba daga gareshi ba.

Bedroom insa ta nufa tana jin yadda zuciyarta take matsewa guri guda, akan sofa ta zauna sai da ta dai daita nutsuwarta kafin ta tashi ta hau gyaran d'akin, shi kuwa bayan ya gama break in falo ya dawo ya zauna yana danna wayarsa kafin yaji cikinsa ya fara wani irin yamutsawa da murd'awa can yaji wani abu ya fara taso masa kamar amai da hanzari ya nufi bedroom in nasa, ta gama gyaran d'akin kenan za ta fito ya banko d'akin ya shigo d'akin a gigice toilet ya nufa a bakin toilet in ya zube ya fara kelaya wani bak'ik'k'irin in amai cikin muguwar azaba, tun yana yi da k'arfinsa a kuzarinsa ya k'are cikin fitar hayyaci yake cewa.
"Me kika bani naci,me nayi miki,wa ya turo ki,me yasa kika zab'i kasheni ta wannan hanyar?"

Wani mugun tashin hankali ne ya ziyarci Nusrat ta fara girgiza mishi kai kafin hawaye ya fara wanke mata fuska cikin wata gigitacciyar tsawa ya kuma fad'in.
"Ki gaya mini wa ya turoki ki kasheni?"
Wani irin rawa jikinta ya fara yi kamar mazari ta fara karkarwa

Cikin sauk'i idan kikayi yaye.

1-Ki sami hulba ki shafa akan nonon

2-Al suzab,al kazbara,gishiri,ki hadasu guri d'aya kina sawa a abinci kina ci,zai d'auke insha Allah.
[6/8, 6:01 PM] Rabi: 41
Asghar ne ya bud'e k'ofar ya shigo, ganinsa da Nusrat tayi yasata sakin ajiyar zuciya amman hawayen bai bar zuba akan fuskarta ba.

Mantawa yayi bai kawo mata rubutun da za ta bashi ba, bayan yasha shayin, tunawar da yayi ne yasa shi tahowa ya kawo mata, da yayi knocking Hajjaju ce ta taso da kanta ta bud'e masa, bayan sun gaisa tace da shi ya hau saman ya gano mata lafiya, tun d'azu ta tura Nusrat to itama ta jita shiru, tsawar da Aashiq yayiwa Nusrat ce tasa yasan suna cikin bedroom in dalilin da yasa kenan ya nufo bedroom in kai tsaye.

Bata rubutun yayi kana ya nufi gurin Aashiq in da ya jingina da k'ofar toilet in yana mayar da numfashi, taimaka masa yayi ya gyara jikinsa, kana ya kamosa ya kwantar da shi akan gado ya koma ya gyara toilet in, bayan yacewa Nusrat ta juyo rubutun a cup ta kawo, da k'yar ya karb'i rubutun yasha da yak'i sha yace k'arasa shi zasui, sai da Asghar in ya lallab'a shi ya nuna masa in yasha shine zai samu sauk'in ciwon da yake ji, yana shan rubutun ba jimawa bacci yayi awan gaba da shi.
Kallon Nusrat Asghar yayi yace.
"Kiyi hak'uri, zafin ciwo ne ya saka shi yi miki wannan tambayar, kije k'asa ki sanarwa Hajjaju zazzab'i yake fama da shi, yasha magani ya samu bacci, ni zan zauna da shi."
Gyad'a mishi kai tayi kana ta fice daga d'akin.

。。。

Kwanansa hud'u yana fama da ciwo, Asghar da Nusrat ne masu jinya duk ya shagwaggwab'esu don akwai shi da raki indai yana ciwo sai dai in babu wani kusa da shi, don Asghar cewa Ramla yayi ta tafi gida shi kuma ya zauna yake kwana da shi, don Nusrat ba za ta iya da shi ba,ko da kwa ace matarsa ce, a kwana na biyar inne ya tashi ras da shi kamar bai ciwo ba sai dai 'yar ramar da yayi fuskarsa tayi fayau.

Daga wanka ya fito ya shirya cikin k'ananan kaya na shan iska, Asghar tun jiya da daddare da yaga jikin nasa yayi d'an dama yaje ya d'auki matarsa suka huce gida, falo ya fito ya zauna yana sauke idonsa kan agogo yaga har sha biyu saura, ko me Nusrat take har yanzu ba ta kawo mishi break ba? "Mtsssss" Yaja tsaki had'e da dak'una fuska sai kuma yaji k'arar bud'e k'ofa ya zubawa k'ofar ido, da sallama ta shigo a bakinta duk da tasan bai zama lallai ta sameshi a falon ba, ganinsa zaune a falon yasa ta d'an dakata tana zubawa fuskarsa ido kamar yadda ya zubawa tata idanuwan, don a rashin lafiyar nan da yayi ya riga ya sallamawa idanuwansa yabi umarnin da yake bashi.

"Barka da safiya,ya k'arfin jiki?"

Me makwan ya bata amsa sai ya shagwab'e mata fuska yace.
"Da alama yau so kike ki k'arasani shiyasa kika hanani abinci, gashi yanzu ma kin taho hannunki haka."

"Naga jikin naka yayi sauk'i ai, shiyasa nayi zaton za ka sauko, da yake Hajjaju ma tana son ganinka."

"Ai sai na gaya mata kin kusa kashe mata jikanta."

"Daga taimako, kuma nima bani akai na saka maka,da ace nasan zai wahalar da kai haka da ban saka ba"
Tasowa yayi yana nufo inda take a tsaye yayi k'asa da muryarsa had'e da fad'in "Saboda kin damu da ni?"

Ba za ta iya cewa eh ba ko a'a don haka tayi saurin bud'e k'ofar ta fice,had'e da fad'in "Ka fito yanzu su Baffa suna jiranka" Da d'an k'arfi yadda zai jiyo, bin bayanta yayi da murmushin da ya fito daga can k'asan zuciyarsa wanda rabon da yayi irinsa tun akan Faleesha, d'an dukan kansa yayi had'e da tambayar.
"Me ke damunka neAashiq?"
Kafin yasa kai ya fice.

(To nima dai bani da wannan amsar,sai dai kuci gaba da biyo alk'alamina zai baku amsa.)

。。。
Chapter 53 · 0% Book details