← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 69

Sashe 48

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba Hadiza ce da kanta tayi sarving nata ta fara cin abincin a hankula kafin suji k'arar door bell, Baba Hadiza ta nufi babban falon don bud'e k'ofar.
Yara ne su uku, mata biyu namiji d'aya sai kuma budurwa kamar Yusranta suka shigo, Baba Azumi ce ta kalli 'yar budurwar had'e da fad'in.
" Ba dai har an tasheku ba?"
Dak'una fuska tayi kafin tace.
"Kai Baba duk dad'ewar nan da nake ganin munyi."
Takai k'arshen maganar tana sauke idonta kan Nusrat kafin ta kalli Baba Hadiza.
"K'aruwa muka samu."
Baba Hadiza tace mata, murmushi ta saki had'e da k'arasawa gurin Nusrat in tace.
"Sannu Aunty, sunana Fa'iza, nice autar gidannan, wa'yannan yaran da kike gani arosu mukayi nan da anjima zan wulla ko wacce gidansu."
"Aunty nice nan auta sunana Aalisha Baby."
"Wallahi Aunty nice nan Auta sunana Falisha Beauty."
"Ni kuma nine babbansu sunana Yaya Aliyu, Aunty da ni kad'ai zaki dinga zuwa shan ice cream ko duk nafi Aalisha da Faliisha hankali."
Murmushi tayi tana jin wani sanyi a ranta had'e da mamakin Yaa Aliyu da alamu Falisha da Aalisha zasu girmeshi amman sai yaci girman yace shine babba tunda su daga jin Faiza tace itace Auta suka ara suka yafa.
"Ni kuma sunana Nusrat, naji dad'in kasancewata a cikinku."
Takai k'arshen maganar tana sauke idonta kan Faiza.
"Muma munji dad'in zuwanki sosai da sosai, bara mu cire uniform."
"Godiya nake, a fito lafiya."
"Allah yasa Aunty."
Daga haka taja hannun su Falisha zuwa ciki."

"Haka kuke da karamci?"
Ba ta san lokacin da bakinta ya jefowa Baba Hadiza wannan tambayar ba, murmushi Baba Hadiza tayi had'e da fad'in.
A kanshi aka rainemu Nusrat dole ne mu kasance muna yinsa.

_"A hali na hauka na tsinci kaina daga wannan bola zuwa wannan bola nake rayuwa, babu wanda ya tausaya mini ya kalleni a matsayin yar adam sai shi, shi ya d'aukeni ya kaini asibiti akayi mini magani har na samu kaina, ko da na warke Nusrat ban san ni d'in wace ce ba, ban san komai akan kaina ba, haka ya d'auko ni ya kawoni cikin gidan nan ya bani ci ya bani sha had'e da sutura, ya kuma bani farin ciki, wannan farin cikin sune wannan ahalin_"
Takai k'arshen maganar tana ajiye hoto a gabanta window size, kana taci gaba.

_Falisha, Nabila, Ramla, Rabi'ah, Farida, Faiza, Baba Azumi, Baba Hadiza ni kenan, sai kuma k'anwarsa uwa d'aya uba d'aya Aalisha._
_Wa'yannan sune farin cikin da Aashiq ya bamu, domin sun d'aukemu ni da Baba Azumi tamkar mu muka tsuguna muka haifesu, mun sosu sun somu, mun k'aunacesu sun k'aunacemu, rayuwa muke me cike da farin ciki da annushuwa, dukkaninmu marayu ne don bamu da kowa ba mu san kowa namu ba, Aashiq shine KATANGARMU domin yayi mana katanga da k'unci da damuwa, da kuma rayuwar k'ask'anci da wulak'ancin da muka taso a cikinta, da badan shi ba da tuni muna can muna garari a cikin duniya amman sai ya had'emu guri d'aya ya bamu farin ciki wato junanmu muka zamo ahali d'aya, wanda har daga k'arshe rik'on k'anwarsa ya dawo hannunmu._
_Faiza 'yar Baba Azumi ce ta cikinta, Nabila, Ramla,Rabi'ah,Farida duk mun aurar da su, Falisha 'yar wajen Rabi'ah ce, Aalisha kuma ta gurin Nabila, Aliyu shi kuma na Farida ne, Ramlah ce ita kuma sai yanzu Allah ya kawo rabon tana goyan 'yan biyu Safa da Marwa._

"Allah ya,biyashi, ya kyautata rayuwarsa kamar yadda ya kyautata tamu gaba d'aya, amman Falisha da Aalisha fa?"
Cewar Nusrat kenan yayin da Baba Azumi da Baba Hadiza suka hada baki gurin cewa."Amin ya Allah" Kafin tambayarta ta dakesu, dukkaninsu sai da idanuwansu suka kad'a kafin suce.
"Allah yayi musu rasuwa."
"Allah yayi musu rahama, kuyi hak'uri"
Sam ba taji dad'in yanayin da taga sun shiga ba sai taji dama ba ta tambayesu su ba, ta hak'ura da iya abinda suka sanar mata......[6/8, 6:00 PM] Rabi: 35
Rayuwarta a cikin gidan, rayuwace me matuk'ar dad'i da nishad'i, ta samu kwanciyar hankali had'e da nutsuwar zuciya, don tana matuk'ar jin dad'i da mutane gidan haka suma suna jin dad'in zama da ita, ba su,tab'a samun matsala da kowa ba gashi har ta d'ibi kusan wata guda a cikin gidan.
Kowa sonta yake hatta su Rabee'ah da suka zazzo kafin su tafi sai da shak'uwa ta shiga tsakaninsu mai k'arfi Faleesha da Aaleesha kuwa dama sun mak'ale mata ko da yaushe suna tare da ita indai ba makaranta suka je ba.
Ta karb'ewa Baba Hadiza da Baba Azumi girki, itace take had'a musu girkuna kala kala masu matuk'ar dad'i, ada Baba Azumi ta sakar mata girkinne don ta san Aashiq ba ya nan, don ba ta son a samu matsala, da kuma taji irin d'an d'anon girkin Nusrat in sai taji ko da ya dawo za ta iya kai mishi, may be ma yafi buk'atar irin d'an d'anon, don d'an d'anon girkin Nusrat in ya tafi da su babu k'arya.

Tun a washe garin da tazo gidan ta ari wayar Baba Hadiza ta kira Yusra, farin ciki gurin Yusra ba'a magana don a kwanakin nan Allah ne kad'ai yasan halin da zuciyarta take ciki game da Yayar tasun, ta sanar mata abinda ya faru da ita da kuma inda take zaune a ciki a yanzu, tun a ranar Yusran taso zuwa amman ta dakatar da ita akan ta bari tukunna ba yanzu ba, ba ta so hakan ba kuma tayi niyar gayawa kawu Iliya shima ta haneta don tasan muddun ta gaya mishi to zaice ta dawo gidan nasa da zama kuma nauyin zai mishi yawa don yanzu samun nashi ya d'anja baya ba kamar daa ba.

Damuwarta Shukhura da Yaa RJ, har yanzu soyayyar 'yar uwartata tana zaune daram a cikin zuciyarta kullum da mikin rashinta cikin rayuwarsu take kwana take tashi, sai dai ba tayi k'asa a guiwar kaiwa Allah kukanta ba, sam ba ta gajiya kullum da kai mishi buk'atarta tasan kuma zai amsa mata lokaci ne baiyi ba, tana fatan zuwan lokacin da ranta da lafiyarta domin ta samu damar cikawa Mama alk'awarinta a kanta.
RJ kuwa damuwarta a kanshi ba tasan wani hali yanzu yake ciki ba, don tayi amannar yana yi mata so ba na wasa ba, rashinta kuwa gareshi bazai shafawa zuciyarsa lafiya ba, amman kullum tana nema musu sauk'i gurin Ubangiji akan ya sassauta musu abinda suke ji cikin zuciyoyinsu game da juna don ta riga ta haramtawa RJ kanta ko da kuwa ya gano inda take a yanzu, duk da da wuya hakanma ta kasance don babu wata k'ofa da zai gano hakan sai dai in idan ita taso hakan.

" Nusratt"
Taji muryar Baba Hadiza na k'wallo mata kira, amsawa tayi had'e da fitowa daga cikin d'akin da sauri.

"Kiranki akeyi kinga har ta ma katse."
Takai k'arshen maganar had'e da mik'o mata wayar, ba ta kai ga yin magana ba wani kiran ya kuma shigowa, don haka tayi saurin yin peking.
"Yayarmu gani a bakin estate in."

"Innalillahi, me yasa Yusra ba kya jin magana ne? Nace ki bari ni zanzo gurinki, yanzu ya kike so nayi miki?"

"Yi hak'uri Yayarmu, wallahi na kasa samun nutsuwar zuciya ne."

Numfashi ta ajiye, had'e da jin Yusran sosai cikin ranta kafin tace.
"Bara na gwada na gani ko zaki iya shigowa."

Ba ta jirayi me zata ce ba ta sauke wayar daga kunnenta had'e da kallon Baba Hadiza tace.
"K'anwata ce tazo, ko da taimakon da za'a mun ta samu shigowa?"

"Too, bari dai na gayawa Baba Azumi sai ta sanarwa da Aashiq in."

A kitchen ta tadda Baba Azumin ta sanar mata ita kuma ta d'auki waya ta kirashi sabili da ba ko yaushe yake so a shigo masa sashen nasa ba dama Baba Azumin ce kawai me shiga saboda kai masa abinci shima iyakarta falo kawai.
Tana gaya mishi yace.
"Khalil zaiji da komai.
Don haka ta koma ta gayawa Baba Hadizan ita kuma ta sanarwa da Nusrat in, dama duk ta k'agu taji Yusran za ta iya shigowa in ba za ta iya shigowa ba to ita tabbas za taje ta sameta.

Tsakanin ita da Yusran ba zan iya tantance muku wanda yafi wani murna ba, sai bayan sun gama zumudin ganin juna kana Yusra ta d'auko wani d'an madai daicin plas tana k'ok'arin bud'ewa tace.
"Masoyiya yau Aunty Hafsa tayi mana tayi mugun dad'i aikwa nace sai na kawo miki."

"Wake da shinkafa?"
Cewar Nusrat, kafin Yusran tace.
"A'a d'aya masoyiyar"
"Awara"
Cewar Nusrat tana dariya yayin da Yusran ma tayi dariya had'e da mik'a mata plas in, hannunta har rawa yake yi gurin aukar guda aya takai bakinta had'e da lumshe idanuwanta.
"Allah ya yi miki albarka Yusra, kin matuk'ar sanyani farin ciki, kinsan rabon da naci awara tun da na baro gidan Aunty Maryam, Allah ya jik'an Daddy ba don ya mutu ba, tun da ya san ina son awara kullum sai ya taho min da ita, ban san a ina yake siyowa ba amman sun iya, jabar jabar za ki ganta da k'wai a jiki gwanin dad'i.
"Allah sarki Daddy, ai wallahi yana matuk'ar sonki."
"Kedai bari Yusra, ba a cewa komai. Baba Hadiza Baba Azumi ga awara don za ku iya ganin plas."

Dariya Baba Azumi tayi had'e da cewa.
"Ai ba kice kina son awara ba da kwa nayi miki tun zuwanki Nusrat."

"Yo Baba Azumi na ganku a cikin uwar daular nan ina zanyi tunanin kunsan wata aba awara, bare kuma yadda ake yinta?"

"Ni kwa na iya awara 'yarnan idan na miki awara sai kunnanki ya cire don dad'i, sana'ata kenan a daa"

Tsalle tayi daga zaunan da take had'e da fad'in.

"Yauwa Baba Azumi shiyasa nake sonki, kiyi mini ta sati na saka pridge nai ta sank'amar kayata."

"Idan kin barta tayi satin ba."

Cewar Yusra.
"Yanzu ta kwano ba za ta iya barinta tayi sati ba?"
Fad'in Baba Azumi tana kallon Yusra.
"Yayarmu ce fa, Yayarmu da awara kuma ai sai Allah, duk ranar da Mamanmu tayi mana baifi muci uku uku ba duk ita take tashi da ita.
Nusrat dai gefe ta ja tana cin awrarta ta bar Yusra da su Baba Azumi suna ta hira.
Chapter 48 · 0% Book details