← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 69

Sashe 55

Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da matsanancin ciwon kai ta tashi,don haka Hajjaju ta hanata yin komai, ta k'wallowa Aashiq kira.
"Kai Turaki,ka sauko aiki yau ya sameka Nusra babu lafiya kai zaka had'a mana break."
Yana juyota don tunda yayi sallah bai kpma ba, yanzunma yana zaune a falo yana jin labarai, murmushi yayi ya tashi ya sauko, bayan sun gaisa ya nufi kicin in, Hajjaju na fad'in.
"Sai a ramawa kura aniyarta, kaima kazo kai jinya,don Nusra da Asaghar sunyi matuk'ar k'ok'ari a kanka da baka da lafiya."

Tea kawai ya dafa, sai k'wai da ya soya musu, Hajjaju za ta kira Nusrat in, yace bari ya kai mata d'aki, duk da shi bai yadda ciwon kan take ba.

Tana k'udun dune cikin bargo, har ya shigo ya ajiye tray in hannunsa ba ta motsa ba.
"Da alamu baccin bai isheki ba, bari nazo mu kwanta don nima tunda nayi sallah ban koma ba."

Da hanzari ta yaye bargon ta diro daga kan gadon tana rarraba ido, dariya ya kwashe da ita sosai, zuba mishi idanuwa tayi, tana ganin yadda yake dariyar tun daga k'asan zuciyarsa ta fito, ba ta tab'a ganinsa yana dariya haka ba, dariyar tayi mstuk'ar k'ara masa kyau, ganin irin kallon da take masa yasa ya tsaya da dariyar shima ya zuba mata nasa idanuwan, sunaiwa juna kallon cikin ido, ko wanne yana d'iban sak'on dake ciki yana kuma bashi mazauni cikin zuciyarsa.

。。。。

Dukkaninsu ba zasu ce ga lokacin da wata k'arfarfar shak'uwa da soyayya ta shiga tsakaninsu ba, soyayya suke irin ta turawa, sun saba da rungumar juna kiss duk ba komai ne a gurinsu, sai dai idan aka cire kiss da huggin in ba su k'ara komai akan hakan ba, sai kuma bacci da suke cikin juna, tun Nusrat ba ta saki jiki da hakan ba, har tausayi da soyayyarsa ta saka ta saduda.

Sun san ba dai dai suke aikatawa ba,kuma suna gudun wata rana shaid'an yafi k'arfinsu sai dai duk da hakan sun kasa dainawa, a duk lokacin da sukai yunk'urin dainawar sai su gaza inda Nusrat ta naima musu mafita d'aya kawai suyi aure, sam Aashiq ya nuna hakan ba mai yuyuwa ba ne, inda suka gabza gagarumin fad'a, fad'an da ko yini ba'ayi ba zuciyoyinsu suka gaza suka neme juna.
Tabbas yasan ta fishi gaskiya a ko ina,ya za'ai su dinga abubuwa irin na ma'aurata bayan ba auranta zaiyi ba, shak'uwarsu k'ara k'arfi take tana gudun da ba su san bigiren da zata ajiyesu ba, yana jinta acan k'asan zuciyarsa itace farin cikinsa,rayuwarsa,ita ta fara gino Katangar farin cikin da ya dad'e da rusheta a babin rayuwarsa,bai tab'a nuna rauninsa ga kowa ba sai a kanta,zai shiga jikinta yayi kuka ta rarrasheshi ta sanya mishi nutsuwa a zuciyarsa, to ta yaya zaiyi sakacin da zata bar rayuwarsa?domin auranta yana nufin barinta cikin rayuwarsa har abada, anan kwa sai dai ya zamo mara adalci,don idan adalci zai mata ya fita daga cikin rayuwarta ya barta ta auri wani, sai dai yasan zuciyoyinsu duka ba zasu iya ba, don shi akan ya barta ta auri wani sai dai inkwa bazai zamo me adalci ba.

Hajjaju kanta ta san da soyayya tsakanin Nusrat da Aashiq, sai dai ko kad'an ba ta san da rayuwar turan da suke ba, don ba sa yi a gabanta, ko kwanan da suke tare ba ta sani ba, da yake tana da nauyin bacci, idan tayi bacci Nusrat in take salallab'awa ta tafi,ana kiran sallar asuba sai ta dawo, ko da ta farka ba ta ganta ba, sai tace ruwa taje sha ko toilet ta shiga, sosai Hajjaju taji dad'in soyayyar tasu saboda ganin yadda tarayyarsu ta fara dai daita rayuwar Aashiq in, don yanzu da ka ganshi kasan yana tare da nishad'i, yaje ya samu Baffa akan ya shirya karb'ar aikinsa, inda hankalinsu yayi mugun tashi,sai dai ba su nuna masa ba sai murna da farin ciki da sukayi da hakan, musamman ma da suka san ba wani abu zai iya tab'ukawa ba tunda ba wani cikakken ilimi yayi ba.
Yana karb'ar aikin ya fara sauya komai,duk wani abu da bai mishi ba ya fara gtara sa, ma'aikatan da ba su dace ba ya koresu,ya dakatar da na dakatarwa, don dakatarwar har kan Aasad ta biyo, bashi da wani aiki sai kwasar kud'in company yana abinda yaga dama, su kansu su Baffa matsayin iyayansa ya duba ya barsu akan kujerarsu don ba su cancanta ba, da fara aikinsa komai ya fara dai daita, abubuwa suka fara bunk'asa, ma'aikata sai murna suke da farin ciki, an fara biyansu yadda ya kamata, dama na can Abuja Asghar ya tsaya a kansa tsayin daka.

Zuciyoyin su Baffa da Aasad ba'a magana don Aashiq ya sauya tunaninsu yayi abinda ba su tab'a tunani ba, don ba su san lokacin da ya k'ware a aiki har haka ba, sun fara tunanin abinda ya dai daita rayuwarsa don ta nan zasu bi su ruguza shi gaba d'aya, duk da Aasad ya gaya musu akwai wata yarinya da ya ajiye yana tunanin karuwarsa ce yana tunanin ita ta daidaita komai, sun dai ce zasu bincika koma mene ne dai zasu lalubo.

。。。

Kallonsa tayi da raunannun idanuwanta had'e da fad'in.
"Ta ya'ya rayuwa za ta tafiyar mana a haka?Mu fa ba waliyai ba ne a ko da yaushe shaid'an yana tare da mu, kuma mun riga da mun san ba dai dai muke aikatawa ba, ina gudun kada shaidan yasa mu aikata abinda zamu zo mui da na saninsa daga baya, musamman ma ni, nice rayuwata za ta ruguje ta lalace,ko da ace kai ka aureni akwai ranar da bazan wuce gori a gurinka ba,don haka ka nema mana mafita, na gaji da wannan rayuwar da muke aikatawa"
Takai k'arshen maganar tana fashewa da matsanancin kuka, dafe kansa yayi da yake jin kamar zai bar gangar jikinsa saboda tsabar ciwon da yake masa, ga kukanta da yake kuma har gitsa sa gashi tak'i yadda ya tab'ata,cikin raunanniyar murya yace.
" Ni kaina ina tsoron wannan ranar ta riskemu,tunda ba mu muka halicci kanmu ba,har cikin zucuyata ba na son abinda muke,amman me na kasa dainawa,bani da wani buri da ya wuce na jiki cikin jikina a duk sanda idanuwana suka sauka akanki,ina so na daina amman na kasa,ki gaya mini ta ya zan iya dainawa?"
"Ba za ka iya dainawa ba mafita d'aya ce kawai muyi aure"

Ji yayi kansa yana mugun juyawa saboda kalmarta ta k'arshe da ta sauka cikin kunnuwansa, Aure aure ya shiga nanatawa a zuciyarsa kafin ya furta kalmar."No" Da d'an k'arfi,yana girgiza kansa. "Bazan iya ba,bazan iya ba,bazan tab'a bari k'addarar da ta samesu kema ta sameki ba,bazan iya,jure rashinki ba,domin rashinki na nufin rasani har abada."
Kama kafad'unta yayi yana sanya tsumamman idanuwansa cikin nata yace.
"Ina sonki Nusra,bazan iya jure rashinki ba zuciyata ba za ta iya ba,ke d'in jinin jikina ce tsokar jikina,bazan tab'a iya kwatanta rayuwa babu ke ba,don haka kibar batun aure tsakaninmu,k'addara ta dad'e da yimin ginin Katanga tsakanina da aure,kalmar aure ma bana son jinta Nusra don dole nake furtata da bakina a yanzu."

Zare hannuwansa tayi daga kafad'unsa tana ja baya tace.
"Zan bar duniyarka a yau d'innan,ka manta da wace Nusrat,ka cireni daga cikin tunaninka,domin baza ka sake ganin ko me kama da ni ba." Tana kawowa nan ta juya ta fice daga d'akin da gudu tana cigaba da kukanta, domin rayuwa babu Aashiq cikin rayuwarta masiface a gareta sai dai ya zamar mata wajibi ta jure dukkan wani yanayi da zata shiga muddun tana son tsira da mutumcinta, da kuma samun yafiyar Ubangijj kan kuskuran da sukayi a baya, tana jin lokacin komawarta gida yayi.

Tana fita, shima ya fice daga gidan gaba d'aya, iska yake buk'atar shak'a ba irin ta cikin gidan ba,yana jin lokaci yayi da zai bar rayuwarta haka, tunda ta zab'i rabuwa da shi gara ya barta ta tafi d'in,don muddun yana d'ora idonsa a kanta bazai daina kusanta kansa gareta ba, gara tayi nesa da shi d'in tunda ko yaya ne in ya tuna tana shak'ar iskar da yake shak'a zai samu sauk'in wani abun.

Kuka take sosai tana had'a kayanta a akwati, kallonta Hajjaju tayi tace.
"Tafiyarki ba mafita bace a gareku Nusra, nasan akan maganar auranku kuka samu sab'ani ko?"
Gyad'a mata kai tayi,tana share hawayenta.
"Aashiq yak'i auranki ne don yana tunanin kema rasaki zaiyi kamar yadda ya rasa matansa na baya sau hud'u yana aure a daren da aka kawo amaren suke mutuwa, wannan dalilin ne yasa yake k'in aure, amman ni ina ji a jikina wannan karan za'a dace insha Allah, zaki iya auransa?"
"Kowa zaman jiran mutuwa yake Hajjaju,idan na mutu lokacina ne ya cika, ban jin yadda nake jinsa a raina zan iya rayuwa da waninsa ba, don haka a shirye nake don na auresa."

Bari muje ga labarin Aashiq na baya...
Chapter 55 · 0% Book details