← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 69

Sashe 10

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun kan ta k'arasa soro k'irjinta ke dukan uku² shikuwa Mustapha alamun tafiyar da ya jiyo ne yasa shi k'urawa k'ofar da za ta fito ido, sai da ta janyo mayafinta ta rufe fuskarta kafin ta tako a hankali zuwa gurin da akai masa shimfid'a da tabarma zuciyarta na harbawa da gudun gaske, can gefe da shi ta samu ta zauna ta sunkui da kanta k'asa kafin tace.
"Ina wuni.?“
"Nima ban ganshi ba, tun da dai ba ajiyarsa kika bani ba, idan kwa kina son na amsa miki to ki tabbata kin yaye rufin da ya Katange mini kyakkyawar fuskar da nake da muradin kallo a ko da yaushe. “
K'asa ta kuma yi da kanta ta na murmushi.
"Please nidai a taimaka mini, yau kusan sati guda rabon da na ganta, tun a ranar da ta samu babban guri a zuciyata, idanuwana suka aminta da ita, suka tabbatar da itace sanyinsu kuma haskensu.“
"To aini kunya nake ji."
Ta fad'a kamar a shagwab'e.
"Idan kika sShukhuraki cikin nawa za ki daina jin kunyar. “
'Cif, na ma kasa bud'e mayafina na ganshi, duk da zuciyata da take ta azalzalata na gansa shine har zan saka idona cikin na, hod'ijam aikam dai sai dai kar na daina jin kunyar'
Muryarsa ce ta dawo da ita daga d'an k'aramin guntun maganar zucin da ta tafi.
"Zan fa zo da kaina na cire mayafin gaba d'aya wallahi idan har ba ki d'aga sa ba.“
'Cif saboda kai d'an ikka ne haka kawai ka ciren mayafina, hod'ijam aikam dai da kaga tsigalewa.'
K'irjinta ne ya buga, zuciyarta tai wani irin harbawa yayin da ta jisa ya matso dab da ita.
'Laa kaddai ciren mayafin zaiyi kuwa, na shige yau na had'u da mara kunyar mutum.'
Da sauri ta yaye mayafin da ke fuskarta, wani kyakkyawan murmushi Mustapha ya saki da yayi sanadiyar motsawar zuciyar Shukhura, wani fitinannen kyahu ta gani a tattare da Mustaphan wanda ba za ta iya bayyana muku shi ba saboda tsabar rud'ewa da cikar kyahunsa.
Gira d'aya ya d'age mata had'e da fad'in.
"Na miki ne? “
Lumshe idanuwanta ta yi don jin bak'on yanayin da ke sauka a ilahirin jikinta, ta d'au tsayin lokaci a haka yayin da shi kuma yake morewa kallonta son ranshi.
Hira suka d'an tab'a kad'an, k'ofofin zuciyar Shukhura sun bud'e gaba d'aya suna d'iban sak'onnin da ke samun babban matsuguni a cikinta, da ya tashi tafiya ya dubeta yace.
"A taimaka mini a tura mini hotunan da zasu dinga d'ebe mini kewa. “
Ya fad'a ya na me mik'o mata kyakkyawar wayarsa kamar shi, ta fuskanci yadda yake me kyau haka komai nasa yake me kyau.
"Aini bana da hoto ko d'aya.“
"Ko a wayar Yayarmu ne a d'an samo mini mana. “
Don a d'an hirar nan da sukai ta ambaci Yayarmu ya kai wajen sau nawa, anan ya gane da wacce take zaune kusa da ita yai tunanin 'yan biyune itace Yayarmun, kuma ya fuskanci akwai soyayya me matuk'ar girma a tsakaninsu.
"Yayarmu ba ta da waya ai. “
"Kawai dai rowa za ki mini, tom shi kenan a gaishe mini da su Mamarmu da Yayarmu da kuma k'annenmu. “
"Tom shikenan zasu ji insha Allah, nima a gaisar mini da so Hajiya, da kuma Hajiya Inna.“
Dariya ya yi had'e da fad'in.
"Hajiya Inna za ta ji da kyau. “
Tunowa da ya yi darun da ta saka da Hajiya ta sanar mata su Shukhura ba 'yan biyu bane, Hajiya Inna har da kuka don ita har ga Allah ta saka ran samun tattab'a kunnenta 'yan biyu da zasu dinga sanyata farin ciki, sai da Hajiya ta lallab'a ta tace ai ba dole sai 'yan biyu ne ke haifar 'yan biyu ba, sai kiga ma 'yan biyun basu haifa, ita kuwa idan da rabo sai kiga ta haifa mana, Hajiya Inna tace.
"To Allah yasa, amma 'yan biyunne suma suna tafiya da gado, shiyasa na fi samun tabbacin da 'yan biyu ce za ta haifa mana 'yan biyu.“

Zaune suke suna fuskantar juna da wani kyakkyawan bafulatani hannuwanta ya rik'o yace.
"Yarinyata hak'ik'a ke haske ce a cikin rayuwar TURAKI ke za ki masa Katanga da damuwar da yake ciki a yanzu, za ki zame masa alkhairi, farin ciki, kuma madubin rayuwarsa.
Hak'ik'a Turaki ya na cikin matsananciyar damuwa, kuma ina da tabbacin kece kad'ai za ki iya fiddashi daga ciki, kece za ki d'ora murmushin da ya dad'e da barin kan fuskarsa, ina mai kuma tabbatar miki ke haske ce cikin rayuwarsa domin kece kad'ai za ki yaye duhun da ke lullub'e da shi. “
"To ta ya'ya kake ganin zan zame masa haske bayan ban sanshi ba ban san a ina yake ba, ban kuma san a ina zan same sa ba. “
"Nima ban sani ba, amman kuma ina so ki mini alqawari guda d'aya. “
"Wani alqawari ne ka fad'a ina jinka, zan cika maka shi domin ina maka kallo tamkar mahaifina. “
Shafa kanta ya yi had'e da fad'in.
"Na yi matuk'ar farin ciki yarinyata, Allah ya yi miki albarka.“
"Aminnn, ina jinka gaya mini alqawarin.“
"Kada ki bud'e k'ofofin zuciyarki ga kowa bare har ki basu muhalli, har sai lokacin da zai bayyana gare ki sai ki bashi gurbi a ciki ki kuma rufeta gaba d'aya, idan kwa ba haka ba akwai wani abu da zai muku Katanga a tsakani. “
"To amma. “
"Ba na so kice komai, tun da kin riga kin amsa mini tun a farko. “
Shiru tayi, ta na son ta sanar da shine ta riga ta yiwa wani wannan alqawarin, gashi kuma ya katseta, yanzu ya za ta yi, meye mafita gareta?
"To meye alak'arka da shi, kuma meye sunansa na gaskiya? “
"Kafin na amsa miki tambayar zan sanar da ke ba za ki sake ganina ba daga yau, kuma ansar wannan tambayar da zan baki itace maganarmu ta k'arshe.
D'ana ne shi, amman kuma mutuwa tai mana Katanga a tsakani tun shud'ad'd'an zamani, sunansa na gaskiya ALIYU ana kiransa da Aa............

Girgizata Shukhura ta yi had'e da fad'in.
"Yayarmu.“
Wanda hakan ya yi sanadiyar farkawarta daga baccin da take wanda tai mafarkin nan a ciki.
"Mtsss kin kama kin tashe ni, gashi ban samu ya fad'a mini sunan da ake kiransa da shi ba yadda in ya bayyana gareni zan ganesa, gashi yace daga yau bazan kuma ganinsa ba. “
Ta fad'a ta na me jin haushin yadda Shukhura ta katse mata mafarkinta ba tare da an gaya mata sunan da ake kiransa da shi ba, to kuma da yake ce masa Turaki waye ke kiransa da hakan?
Oho ta bawa kanta ansa.
"Kiyi hak'uri, Mama ce tace na taso ki ki k'arasa wanke-wanken yankewa na yi a hannuna in omon ya shiga zafi yake mini kuma bakwan ta kusa da kikace a tashe ki, to amman kuma waye kike kiran ba'a gaya miki sunan da ake kiransa da shi ba? “
"Mafarkin da na gaya miki ina yi ne Shukhura, gashi kuma yace daga yau ba zan sake ganinsa ba, bansan ta inda zamu had'u da Turaki ba Shukhura kuma ban san da wata alama zan ganesa ba. “
"Yayarmu na gaya miki fa ki watsi da lamarin mafarkin nan na ki mafarki fa ba gaskiya ba ne. “
"Wani mafarkin gaskiya ne Shukhura, don na ji ance wasu malaman sunce duk mafarkin da za kayi shi da daddare ka sake yinsa bayan sallar asuba gaskiya ne, wannan dalilin ne nake jin nima nawa gaskiya ne, kuma ina jin hakan a jikina.“
"Wai Shukhura Ina Yayar takun take ne.”
"Gani nan Mama. “
Nusrat ta fad'a had'e da ficewa daga d'akin Shukhura ta bita da kallo.
Washe gari Mustapha ya dawo ya kawowa su Shukhura ita da Nusrar wayoyi sababbi fil a kwalinsu sai walwali suke da shek'i, murna gurin Shukhura da Nusrat ba'a magana yayin da Umma bak'in ciki kamar ya karta, ta sanya Nimha a d'aki tace.
"Kin gani ko, sun fara tura ki a gefe tun kan arzik'in ya ratsasu, yanzu in da da kara ai har da ke za'a kawo wayar. “
" Ni ban ji komai ba Umma, nima Saminu yace k'arshen watan nan zai siya mini. “
"Au yanzu yarinyar nan ba ki sallami Saminun nan ba, yanzu ki rasa wanda za ki mak'alewa sai matsiyacin da babu abinda zai iya tsinana mana.“
Turo baki gaba ta yi ta na had'e rai tace.
"Wallahi ni Umma shi nake so ba abin hannunsa ba, idan har zai bani soyayya da farin ciki ya gama mini komai, kuma k'arshen satin nan zai turo magabatansa gurin Baba. “
Ta na kawowa nan ta fice daga d'akin don ta san maganar da za ta fito daga bakin Umman ba mai dad'i bace.
"Amman ke dai anyi gantalalliyar yarinya, to wallahi tun wuri kije ki sami Babanku ki sanar masa ba kya sonsa don wallahi muddun rai ba za ki auri matsiyacin yaron nan ba, dudu nawa ne albashinsa da zai iya rik'eki, aike wallahi zubin matan manya ne da ke, amman da yake ba ki san ciwon kanki ba kin lik'ewa wanda babu d'igon arzik'i a tattare da shi, banda haka da kin samo mana wanda zamu shiga cikin dukiya mu kwantar da kai a cikinta a kuma daina mana d'agawa da dukiyar da babu tabbas d'in za'a ji dad'inta.“
Chapter 10 · 0% Book details