← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 69

Sashe 49

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da fatan munyi sallah lafiya, Allah ya karbi ibadunmu yasa muna da rabon ganin wasu shekarun cikin k'oshin lafiya Allahuma amin
[6/8, 6:00 PM] Rabi: 36

Sai bayan sallar la'asar Yusra ta tashi tafiya Nusrat ta yo mata rakiya, sunzo babban falo wani sihirtaccen k'amshi ya ziyarci hancinansu a hankula Nusrat ta ciri kanta had'e da d'orawa gurin da k'amshin ke sirarowa idanuwanta .

A hankula yake takunsa cikin nutsuwa da kamewa, idanuwansa akan Nusrat ya fara sauka don haka suka gauraya guri d'aya da nata, rabon da ya sanyata cikin idanuwansa tun a asibiti, don sam ba ya son alak'arta da idanuwansa duk da har yau tak'i barin cikinsu amman idan ba su ganta ba yakan ji sauk'in abun.
Ba ta tantance wanda ya taimaketa har take zaune a k'ark'ashinsa ba sai a yau d'in, ba ta mance fuskarsa ba shine wannan kyakkyawan da sukayi arangama da shi har sau biyu a asibitin gogel.
A lokaci guda duk suka zare idanuwansu daga na juna amman ita akan bak'in sandan da ke hannunsa ta sauke idonta, shi kanshi sandan abin kallo ne abin kuma burgewa don da ganinsa kasan zaiyi matuk'ar tsada.

Yusra ce da ta ankara da fitowarsa tayi saurin tsugunawa had'e da fad'in.
"Ina yini"
Ko gurin da take bai kalla ba yasa kai had'e da bud'e k'ofar ya fice.
Wani k'ululin bak'in ciki ne ya kamata ta sauke idonta akan Nusrat tana mata kallon tambayar.
"Dama haka yake?"
"Nima ban sani ba Yusra, ko damar yi masa godiya nima ban samu ba, tun zamana a gidan wannan ne karona na farko da na ganshi, amman da alamunsa zaiyi jin kai."
Nusrat tace da ita haka, jinjina kai kawai tayi suka saka kai suka fice.

Yana k'ok'arin shiga mota yaji an k'walla masa kira.
"Yayaa"
Cak ya tsaya daga k'ok'arin shiga motar da yake, domin ji yayi tamkar muryar Aaleesha duk da yasan gizo ne kawai na kunnuwansa domin kuwa ta riga tayi tafiyar da babu dawowa a cikinta, waigawa yayi don ganin me kirann nasa, akan Yusra idanuwansa suka sauka dake had'owa da sassarfa don tayi saurin cimmasa, idan ba gizo irin na idanuwansa ba ma sai yaga har d'iban kamanni suke da Aaleeshan.
Gurin da yake ta nufa kai tsaye had'e da tsugunawa tana 'yan dube dube kamar me neman wani abu, idan ya,matsa sai ta matso tana duba har tsakiyar k'afafuwansa, cikin kamammiyar muryarsa yace.
"Ke lafiyanki kuwa?"
Don daa har yaransa sun harzuk'a sun yo kanta, kallo d'aya yayi musu suka koma yadda suke.

"Lafiyana qalau, murmushinka kawai nake nema ko Allah xai bani sa'ar laliboshi a duk inda ka b'oyeshi."

Wani bazataccen murmushi ne ya sauka akan kyakkyawar fuskarsa, wanda gaba d'aya yaransa suka saki baki suna kallon ikon Allah, har da Asghar wanda tare ma zasu fita ya fito daga cikin motar yana ganin ikon Allah, rabon da irin wannan murmushin ya sauka akan fuskarsa tun kafin mutuwar Aaleesha ne.

"Ko kai fa wallahi har ka k'ara kyau sai naga zubin dimple inka kamar irin na Yayarmu, Yayarmu yi murmushi mu gani."
Takai k'arshen maganar tana waigowa gurin da Nusrat in ke tsaye tana kallon ikon Allah, wanda shi kuma Aashiq hakan ya bashi damar shigewa cikin mota ya zauna."
"Ai ban gama da kai ba, ni sunana Yusra k'anwar Nusrat ce uwa aya uba aya, duk duniya idan ka cire iyayan da suka kawomu duniya to bani da tamkarta, ina sonta ina kuma son duk wanda ya sota, duk wanda ya k'aunaceta tamkar ni ya k'aunata, da ba dan ka ceci rayuwarta ba da bai zama lallai na kuma d'ora idanuwana a kanta ba wanda ban san halin da zuciyata za ta kasance ba kuma, na gode godiya wacce bakina bazai iya fad'in adadinta ba, Allah ya saka maka da gidan aljanna, ya duba gabanka da bayanka ya kuma shiga cikin lamarin rayuwarka.

"Amin,thanks"
Yace da ita yana k'ok'arin rufe motar, duk da a ransa yarinyar ta matuk'ar burgeshi saboda k'aunar da takewa 'yar uwarta.

"Ba ka gaya mini sunanka ba"

Rintse idanuwansa yayi don ya fara gajiya, rabon da yayi doguwar magana irin haka har ya manta lokacin, a gajarce yace da ita.
"Aashiq"

"Nice name, kana k'anwa da ni?"

Jinjina mata kai yayi

" Thanks, yanzu bari na shiga motar na biku, don ka gayawa wa'yannan k'artin securityn ni k'anwarka ce yanzu bani da KATANGA da estate innan duk sanda na so shigota."

Gurin da Khalil yake a tsaye kawai ya kalla, yayi saurin zuwa gurin da Yusran ke tsaye had'e da fad'in.
"Ki shiga waccan motar, nine zan kaiki har gida."
Yakai k'arshen maganar yana nuna mata motar.
"Thanks Yayanmu."
Duk da a lokacin ma Asghar ya riga ya ja motar zasu fice.

Nusrat cewa tayi za tabi Khalil in suje su ajiye Yusran a gida, bai hanata ba yace ta shigo suje in, suka shiga tana tayiwa Yusra fad'an zaro zance kamar wata babbar mace, don yau ta k'ure lissafin Nusrat in, don ko ita ba za ta iya zaro maganganun da tayi a yanzun ba duk da maganar tata cikin hikima tayita da wayo da basira yanzun ma cewa tayi.
"Yayarmu kiyi hak'uri, matsayinki a zuciyata yayi nisan da baki bazai iya fad'arsa ba, hakanne yasa nake ganin girma da kimar duk wanda ya girmamaki, k'anwar mahaifinmu tayi miki tuggun da k'anin mahaifinmu da kakarmu su kaki amsarki, shine ya taimakeki ya ceto rayuwarki ta hanyar kaiki asibiti, sannan ya baki matsuguni me kyau ba tare da yasan ke d'in wace ce ba, daga kuma ina kika fito, a zahirin gaskiya wannan abin da yayi miki yasa kimarsa da mutuncinsa baza su tab'a barin idanuwana, ina kuma jin sonshi tamkar Babban Yayanmu, tabbas da ace a gidan nake a zaune to zan sauyashi zan kuma dawo da murmushi akan fuskarsa."

Sai da khalil in ya tsaya a bakin babban get in yayiwa securityn bayanin Yusran kana suka fice tana gaya mishi unguwar da zasu je.

"Wace ce wannan yarinyar?"
Cewar Asghar yana juyo da kallonsa ga Aashiq in don jiran jin amsar da zai bashi.
"Nima ba nace ba, yayarta ce ke zaune a nan gidan."

Mayar da kansa yayi ga tuk'in da yake, duk da a cikin estate in suke ba wani guri zasu fita ba, don ya san daga haka bazai kuma d'ora komai ba ko da kuwa ya kuma jefo masa wata tambayar, don k'aidarsa ce tambaya aya yake amsawa itama kuma a gajarce, shiyasa yau in kowa yayi mamakinsa.

Gidan su Aashiq suka fara zuwa wanda mahaifiyar mahaifinsa ce ke zaune a cikin gidan Hajiya Zuwaira wacce suke kira da Hajjaju, macece wacce ba ta fiya son mutane na rab'arta ba idan ba jininta ba, suma d'in ba kowa ba, hakanne yasa take zaune ita kad'ai a cikin gidan sai masu yi mata hidima, sai dai Aashiq in kullum zaizo su gaisa idan bai samu zuwa da safe ba to zai zo da yamma, wani zubin kuma yakan dawo nan d'in da zama sai dai ya dinga lek'awa su Baba Azumi, tana matuk'ar k'aunar jikan nata haka shima yana k'aunar kakar tasa.

Sun sameta ba ta jin dad'i guiwoyinta sun matsa mata da ciwo wanda hakan ya d'aga hankalin Aashiq sosai.
"Kema Hajjaju kin fiya kafiyane wallahi, ki yadda a fita da ke k'asar waje yadda za'a fi bincikar guiwar taki sosai a gano kan matsalar."

"Uhmm uhm nidai Turaki ka barni anan, idan wa'adina ma yazo a binneni a k'asata, don kak'i yadda ne ma ni da gogel zanyi tafiyata a binneni a mahaifata."

Baice komai ba saboda kayan takaici da yayi masa yawa sai number Dr Sa'ad da yake kira saboda shine family doctor insu, k'wararran likita ne ya karanci ko wani fanni na likitanci.

Ya d'an bata taimako had'e da wasu magun gunan da zai taimaka mata wajen rage zafin ciwon da take ji, kana yayi mata allurar bacci saboda har da zazzab'i a jikinta, ana yi mata allurar ba jimawa bacci ya d'auketa, inda likitan ya buk'aci da kar a barta ita kad'ai a samu wani ya zauna tare da ita, inda ya kira wata daga cikin masu mata hidima ta zauna da ita su kuma suka fito.

Tazarar zuwan jinin haihuwa da haila shine:
Idan jini haihuwa yazo miki kuma kafin ya cika kwanaki 60 ya auke sannan ya dawo bayan k'asa da kwana 15, hukuncin wannan jinin, jinin haihuwa ne ya dawo miki anan zaki kula sosai ki lissafa kwanakin da kikayi a baya sai ki d'ora da sabon da yazo miki har zuwa kwana 60 iya adadin kwanakin da jinin haihuwaa ke daauka yana zuwa.
Idan kuma bayan kwana 15 ko sama da haka ya dawo miki to hukuncin wannan jinin jinin haila ne yazo miki wato kin fita daga jinin haihuwa.

Abin lura anan shine tazarar jinin haihuwa da haila shine kwanaki 15, idan bai kai haka ba to jinin haihuwa ne ya dawo idan kuma yakai kwanaki 15 ko sama da haka jinin haila ne yazo.
Allah ne mafi sani.
[6/8, 6:01 PM] Rabi: 37
Gidan su Asghar suka shiga wanda yake jikin na su Aashiq in, inda mahaifiyar Asghar in Hajja tayiwa Aashiq in tarba ta mutumci kamar ko da yaushe idan ya shigo gidan, ba su samu Baffa mahaifin Asghar in a gida ba don haka ba su wani jima ba suka fito suka shiga gidan su Aasad wanda shima yake jikin na su Aasghar, sai wani daga jikin d'aya b'angaran shi kuma na Baffa Ibrahim ne, sai dai shi ba ya ciki ya koma can gogel da zama tare da iyalinsa, babu yadda Aashiq bai yi dashi ya dawo ba yak'i, kuma har yau yak'i fad'in dalilinsa na barin estate in, sai dai Aashiq in yakan ziyartarsa akai akai.
Chapter 49 · 0% Book details