Sashe 39
Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read
"K'warai kuwa, harma na bashi dama gobe zaizo insha Allah."
"Kinyi kuskure Hidaya,na bashi damar da kika yi, zuciyata ta dad'e a rufe saboda alk'awarin da na karb'a har guda biyu, gara d'aya a mafarki ne d'ayan kuma a gaske ne ina kuma son cikashi, kada ki zama silar da zan karya alk'awari don Allah, zuciyata tana da rauni."
"Wani alk'awari, wa kuma kikawa?"
Sai da ta fara murza zoben azurfar da ya saka mata kafin tace.
"Yaa RJ"
Ta fad'i hakan tun daga k'asan zuciyarta, wata muguwar faduwar gaba ce ta ziyarci Hidaya wacce ba ta shiryawa ba har ta kusa bugawa wani mai adai daita ba shiri taja wani burki kuuuuuuu kike ji, cike da tsoro Nusrat ta rintse idanuwanta tana salati kafin ta bud'esu akan Hidaya da ta had'a uwar zufa lokaci guda tana k'ok'arin gangarawa gefe tayi parking tana mayar da numfashi.
Kenan Yaa RJ son Nusrat yake?
Sai yanzu take tuno maganarsu ta rannan da yake tambayarta.
"Nikwa Hidaya ina Nusrat?"
"Tana nan lafiya, amman ta kwana biyu ba tazo mana ba."
"Amman dai ba tayi aure ba ko?"
"Eh ba tayi ba, na Shukhura dai akayi."
"Alhmdlillh, Alhmdliillh amman naji dad'i sosai."
"Yaa RJ cewa nayi ba tayi aure ba fa amman kake ta murna haka."
Kawai sai ya basar a zuwan ya zaci cewa tayi duka sunyi aure, da kuma hirar su da take ce masa Nusrat in ta dawo gidansu da zama taga yadda yake nuna farin cikinsa a fili, har ya dunga zumud'in dawowarsa a ranar ma ya sanar mata bayan sallah zai dawo insha Allah."
"Hidaya wai lafiya, me ya faru ne?"
"Wallahi kaina ne ya fara juyawa Yayarmu, da kin iya jan motar ma ke zaki jamu."
"Wayyo sannu, mu d'an tsaya kiji dai dai tukunna."
D'aga mata kai kawai tayi tana jingina da kujera ta lumshe idanuwanta tana jin yadda kanta ya fara sarawa a gasken, fuskar Yaa RJ ce take mata yawo a idanuwanta,gaba d'aya zuciyarta ta gama mutuwa a sonsa da k'aunarsa, ya riga ya jima da raunata mata zuciya gaba d'aya ya ya za tayi idan ya tabbata zuciyar RJ Nusrat take so, me hakan yake nufi?
To tunda har ya sanyata yi masa alk'awari sonta yake Kenan, da babu soyayya me zai sanya yace tayi mishi irin wanan alkawari me girma?
Sai a yanzu duk k'wak'walwarta take tariyo mata yadda yakewa Nusrat in idan tazo gidansu shiysa kenan tun a lokacin Momy take nuna ba ta son alak'ar Nusrat in da RJ?
To koma dai meye a yadda take jin soyayyar RJ tana huda ko wani sassa na jikinta ko kad'an ba ta jin za ta iya barwa Nusrat in Rjnta....
[4/26, 8:43 PM] Rabi: BEBE'ARTH
KTG 24
Ana sallar magariba suka shiga gida, Momy ta hausu da fad'a musamman Nusrat tunda ta san zata d'ora dinner shine taje ta biyewa Hidayan sukai dare haka, hak'uri ta bata had'e da nufar kichen in don ta d'ora dinner in, a gaggauce tayi musu jalof in couse-couse sai su piece, grean beans,carrot da kidney da ta saka a ciki yayi sha shar da shi sai zuba k'amshin curry da spices yake, mango juice ta had'a ta bar Hibba ta jajjerasu akan dinning ta haye sama don a matse take audigar jikinta duk ta takura mata so take tayi wanka ta canja wata, ga mararta kad'an kad'an tana mata ciwo, yaune dama ta tashi garau amman jiya da shekaran jiya kamar baza tayi ba saboda azababban ciwon mara har sai da aka kira doctor in gidan ya duba ta.
Tana shiga bayi ta fad'a ko lura da Hidaya da ke kwance a gado ba tayi ba, tsabar wanka ne kawai a gabanta.
Hidaya kuwa gaba daya ta zurfafa cikin tunani, hotunan RJ ne take ta kalla, wanda ta saka ya turo mata su ta email, kallonshi take zuciyarta tana kuma ruruwa da zazzafar k'aunarsa wacce ta riga ta gama mata illa tun k'uruciya, tasan Mommy baza ta tab'a bari wata alak'a ta shiga tsakanin Nusrat da RJ inba, inma ta shiga akwai hanyar da zata bi ta sanya sabon almakashinta ta datseta, saboda itace take gaya mata RJ nata ne akwai alk'awarin aure tsakaninsu, tana gama makaranta za'ayi bikinsu, to amman Daddy fa?
Tabbas Daddy idan yasan RJ in yana son Nusrat zai iya goya mishi baya ya aureta hakan yana nufi zasu had'a kishi da Nusrat kenan?
Kai ina bazai yihu ba bama zai tab'a yuyuwa ba kawai dai za ta san duk yadda za tayi Nusrat in ta saurari Ishaq yadda maganarsu za tayi k'arfi tunkan dawowar RJ.
"Hidaya kanne har yanzu?
Ki tashi ki watsa ruwa kiyi sallah sai kici abinci kisha magani"
Maganar Nusrat da ta fito daga wanka jikinta yana ta d'igar ruwa ta katseta daga tunanin da ta zurfafa a ciki, d'aga kai tayi ta kalli Nusrat in zuciyarta tana mata wani irin ciwo kafin ta amsawa Nusrat in da ka alamun taji me tace ba tare da ta bata amsar tambayar da tayi mata ba, itama,ba ta damu da hakan ba saboda ta san a hali na ciwo take sai kawai ta hau kimtsa jikinta.
Ice cream in da suka siyo kawai tasha ta hayewarta gado, don yau ba ta jin cin abinci, wayar Hidaya da ta ajiye ta fita ta d'auka da yake ta san key in ta bud'e ta hau buga gem, can kuma sai ta lalubo number Auncl Iliya da ta saka tayi saving tun a washe garin zuwanta ta kirashi ya had'ata da Yusra, ta danna mishi kira, ringing d'aya zuwa biyu taji muryar Yusra tana fad'in.
"Yayarmu"
"Yusrata ya kuke, ya su Auncle Iliya da Aunty Hafsan?"
"Lafiya lau Yayarmu, Aunty Hafsa ma ta haifi mace shekaranjiya."
"Masha Allah, Allah ya raya, basu nayi musu barka."
"Amin, tom bara na kai musu."
Auncle Iliya ta fara bawa suka gaisa tayi masa barka kana ta bawa Aunty Hafsa itama suka gaisa tayi mata barka daga bisani Yusran ta karb'a suka cigaba da hirarsu, anan take gaya mata Auncle Iliya ta sanyata a makaranta private me kyau, kuma yace bayan suna zai siya mata waya k'arama da zasu dinga yin waya da Nusrat in, Farin ciki sosai Nusrat in ta shiga, ta dinga kwararawa Auncle Iliya Addua, sai taji zuciyarta ta nutsu guri d'aya da Yusran ta samu muhalli me kyau, a yadda Yusran take gaya mata daga Auncle Iliyan har Aunty Hafsa mugun ji suke da ita.
Sun dad'e sosai suna hira cike da so da k'aunar junansu, syna jin kamar sunyi shekaru masu yawa rabonsu da juna, har Hidaya ta shigo suna wayarsu ta jinjina kai a ranta tana jinjina soyayya da shak'uwar da ke tsakanin Nusrat da Yusra, wanda su sam babu irin wannan shak'uwar tsakaninta da 'yan uwanta, amman kuma tana mamakin duk shak'uwar Nusrat da Shukhura a baya amman yanzu duk basa k'aunar ai musu zancen juna ta rasa dalili, duk kuma tayi musu wannan tambayar babu wanda ya bata amsa, haka rannan da suka had'u da Shukhura a Buk (Itama can take zuwa tana karantar lunguistic, medicine yaso nema mata Mustaphan amman bata samu ba.)tace mata Nusrat ta dawo gidansu da zama amman sai ta basar da zancen nata ta nuna kamar ba taji me tace ba, itama Nusrat in babu yadda ba tayi da ita akan tazo suje gidan Shukhuran tana Kuntau forestry amman fir tak'i, da ta d'auko zancen Shukhuran zata had'e mata fuska, kuma abin yana mugun damunta don tasha kamata da hotunansu su uku ko su hudu har Mama tana kuka tana meyasa Shukhura ta zabi yin KATANGA a tsakaninsu, duk ranar da tayi irin kukan nan kwana take tana sallah tana nemawa iyayanta rahama da kuma dawowar Shukhura cikin rayuwarsu.
Suna gama wayar ta kashe ta mik'awa Hidaya dake zaune ta k'ureta da ido ta zurfafa a tunani, muryar Nusrat ince ta dawo da ita daga tunanin.
"Gashinan, naji alamun an kiraki ki duba kiga wa ya kira."
Karb'a tayi had'e da yin murmushi tace.
" Soyayyar da Shak'uwar dake tsakaninku da Yusra tana birgeni ina jin inama nima da Hibba haka muke."
Murmushi Nusrat in tayi had'e da fad'in.
"Idan hakan yana birgeki lokaci bai k'ure miki ba, kafin barinki gidannan ki jaho Hibba jikinki ki nuna mata soyayya, to tabbas zata sake da ke za kuma tafi girmamaki da nuna miki soyayya."
"Zan gwada"
Ta fad'a a tak'aice had'e da mayar da hankalinta kan wayar don ganin waye ya mata miss call, Ishaq ta gani, tana k'okarin bin kiran ya kuma kira, picking tayi had'e da kwanciya akan gadon tayi rigin gine, yaya sukaje gida shine abinda ya tambayeta ya kuma ce mata kada ta manta ta turo masa Addres in gidan nasu tace masa insha Allah baza ta manta ba, suna gama wayar ta tura masa tana k'udirewa a ranta ko ta yaya ne sai ta cusa Nusrat din cikin rayuwarsa yadda zata bar mata Rj inta ita kad'ai.....
Ina fama da rashin chargi shiyasa zaku dinga jina shiru.
[4/26, 8:43 PM] Rabi: BEBE'ARTH
KTG 25
Washe gari da Ishaq yazo masaukin bak'i Hidaya ta sanya aka kai shi, kana ta tura Hanne me aikinsu ta kai mishi juice da ruwa da d'an abin motsa baki daga bisani ta nufi gurin nasa ta bar Nusrat tana kintsawa bayan ta lallab'ata da dad'in baki akan taje ta saurareshi taji da me yazo, in yaso sai ta sanar da shi abinda ke ranta.
Gaisawa sukayi cikin mutumci, kana ta sanar mishi Nusrat in tana shiryawa ne kafin ta zayyana mishi cewa ko da Nusrat in ta sanar masa akwai wanda taiwa kanta alk'awari to ba haka zancen yake ba, kawai dai tana tsoron maza ne saboda wani da ya yaudareta ana gab da bikinsu yace ya fasa, to amman ya bita a hakan, in yaso sai yace yana son su k'ulla abota, duk yadda dai zaiyi yayi ta anshi abotarsa ita kuma za ta dinga taimaka masa a hankula sai dai Nusrar in ta tsinci kanta cikin soyayyarshi, yayi na'am sosai da shawarar da ta bashi ya dinga zuba mata godiya yana k'ara ganin girma da kimarta.