← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 69

Sashe 58

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falisha,Nabila,Ramla,Rabi'ah,Farida,dukkaninsu sun bud'i ido ne sunga suna rayuwa ba tare da sun san waye yayi silar zuwansu duniya ba,junansu kawai suka sani,tare suke tashi su fad'i,daga wannan kango zuwa wannan kango suke rayuwa,suna rayuwa ne gwanin ban tausayi domin sai sun fita sunyi bara sannan zasu samu abinda zasu sakawa cikinsu,an nemi keta musu haddi kusan sau nawa Allah ne kawai yake kub'utar da su, a yawon bararsu suka had'u da Baba Azumi,itama barar take fitowa da k'aramar 'yarta,Faiza,mijinta ne ya gudu ya barta,bayan shi yayi silar zuwanta garin ba ta san kowa ba yayin da aka koreta daga gidan hayar da take ciki, ya zamto sai tayi bara za ta samu abinda zasu saka a bakinsu ita da 'yarta, had'uwarsu sai suka zamto tamkar wani ahali,sukewa Baba Azumi kallon mahaifiyarsu, har suka dawo kwana cikin kango d'ayap babu wanda ya kallesu da idan rahama ya tausaya musu,ya nuna suma 'ya'yane ya tsaya dominsu sai Aashiq.
Tsautsayi ne yasa ya kad'e Faleesha,yayin da suka d'auketa suka kaita asibiti,satinta guda kafin ta san inda kanta yake,kafin ta samu ta farfad'o,bayan taji sauk'i suka d'aukota don kaita gidansu,inda tayi musu kwatancan kwangon da suke ciki, suna ganinta da gudu suka rugo suka rungume juna, ko wacce da hawaye a fuskarta,sunji tsoro sosai,har sai da suka ji rayuwar sam ba dad'i rashin Falisha tare da su, ta d'an girmesu sai suke mata kallon yayarsu, yayarsu d'ince ma don basu da kowa sai junansu.
"Munji tsoro,ashe zaki dawo garemu?"
Cewar Rabee'ah,yayin da Ramla tace.
"Dama Baba Azumi tace mana zaki dawo."
"Zan dawo,mutuwa ce kawai za ta hanani dawowa gareku."

"Oga ina tunanin fa marayu ne yarannan."
"Idan suna buk'atar kyakkyawar rayuwa,kace da su su shirya zaka dawo ka tafi da su."

Basu da wani zab'i illa na bin Khalil yakaisu duk inda zai kaisu, sun gaji da gaske har cikin zuciyarsu da bin kwangaye ana korarsu wasu na neman keta musu haddi.
Hajjaju sam ta nuna baza ta zauna tare da su ba,akwai gidaje da yawa dake cikin estate in ba ta hana ya kaisu can ba, haushi yasa shima ya koma can da zama yayin da Aaleesha ta biyosa,don rayuwa a inda babu Yayanta ta kan jita kamar ba rayuwa ba, tafi son ta shak'i irin iskar da yake shak'a
Cikin kwanaki kad'an rayuwarsu ta sauya,farin ciki ya gudana a zukatansu kafin Baba Hadiza ta shigo rayuwarsu,suka mayar da kansu Ahali guda,don dukkaninsu junansu zasu nuna su kira danginsu.
Tun a gani na farko da Falisha ta yiwa Aashiq zuciyarta ta fara doka masa,kafin ta fara karb'ar sabon yanayi a kansa,saboda samun kusanci da shi take shishshigewa Alisha,idan Alishan za ta gyara masa d'aki tare suke yi,abinci ma in zata kai mishi tare zasu kai,psai dai ko kallo ba ta isa a gurinsa ba,yayin da soyayya da k'aunarsa suke k'ara k'arfin gudu a zuciyarta har ta kasa jurewa ta ajiye ajinta a gefe tare da kunya da akan san 'ya mace da ita da kawaici ta tareshi akan tana son kusancin zuciya da tasa zuciyar kai tsaye yace da ita.
"Kinyi kuskuren barin zuciyarki ta so kusanci da tawa,don abune wanda ba za ta samu ba,don ni da aure tuni k'addara ta saka almakashinta mai k'arfi ta datsa tsakaninmu."
"Ni ina sonka,ina son kasancewa da kai,ina son tafiya tare da kai,ina son tayaka jin rad'ad'inka da sauke hak'k'inka,amman duk da haka kana ganin kuskurena,ka bamu matsuguni,mabuk'ata ka ciyar da su,marasa muhalli ka basu,ka d'aukeni a matsayin marainiya ka bani muhalli a zuciyarka nima don Allah."

Idan aka bashi labarin akwai lokacin da zuciyarsa za ta bud'ewa wata ba shakka zai k'aryata hakan,sai gashi bai san lokacin da har ta bud'ewa Falisha ba,ta fara motsawa da doka mata,yayin da sanyayyar soyayya ta fara gudana a tsakaninsu duk da yana jin tsoro,yana jin tsoron abinda ya samu su Maryam ya faru da ita,har aka fara shirin bikinsu a tsorace yake,ba kuma abun yace ya fasa ba,tare aka had'e bikin nasu da na,Ramla da Asghar,da suka had'e kansu suma,Rabee'ah,Farida,Nabila su kuma a cikin yaran Aashiq ne sukai wuf da su, sai na Aalisha da Aasad, ta kammala karatun nata,inda ta karanci fannin jarida,dama Aashiq ne ya hana auran nasu sai ta gama karatunta,tunda shi bai samu damar hakan ba,ba suji komai ba tunda Falishan mace ce,kuma hannunsu za ta dawo,tunda Aasad ne zai aureta sai yadda sukayi da ita.

Maganin Infection
1-Zuma,garin tafarnuwa,garin zogale,garin habbatussauda,kustul hindi,ki had'asu guri guda ki kwab'a da zuma,kina shan 2spn sau uku a rana,insha Allah zaki rabu da shi.
2'Ya'yan zogale,kina shan guda d'aya kwana7
3Bagaruwa garin hulba zaki had'asu ki tafasa kina zama a ciki sau 4 a rana 7days.
4-Man habbatus sauda,kina sha kina inserting.Manzon Allah (S.A.W)yace."Habbatul baraka ta isheku magani akan komai banda tsufa da mutuwa."
[6/20, 7:53 PM] Rabi: 46
Bayan an d'aura auransu Aashiq zamewa yayi ya komo gida,tun kan ya k'araso yake kiran wayar Falaisha yace ta sameshi a d'akinsa,daran jiya ne sam bai rintsa ba saboda azabar ciwon mara,har zuwa safiya ma sam bai rabu da azabar da yake ji ba,abar tasa ma tak'i kwanciya bare ta risina masa,bai jin zai iya kaiwa har dare a haka,tunda an d'aura ta zamo halaliyarshi ai an gama magana.
Tana shirin fitowa daga bedroom in,saboda ba ta ganshi a ciki ba,suka ci karo shi kuma zai shigo,hannunta ya rik'e suka k'arasa ciki a tare ya zaunar da ita bakin gado kafin ya nufi gaban mirro yana ajiye hular da ke hannunsa,had'e da cire agogon hannunsa ya ajiye,kana ya zare babbar rigar da Asghar ne ya matsa masa sai ya saka,saboda anko sukayi duka su ukun.Kanta yana k'asa har ya gama cire kayan jikinsa tsaf yayi saura daga shi sai gajeran wando kafin ya k'arasa ya sakawa k'ofar key,gabanta ne yayi wani irin fad'uwa ta d'ago ta kalleshi,da sauri ta kuma yin k'asa da kanta,a ranta tana fad'in."Maza sam basu da kunya wallahi"Ga k'arfaffan jikinsa da ya kuma tsoratar da ita tunda ba tab'a ganinsa tayi a wannan yanayin ba.
Tausayi da k'aunarsa sun raunata mata zuciya,ba za ta iya hanashi kanta ba,don haka ta jurewa komai,duk da taso ya bari a kaita saboda kunyar mutane,amman yanayin da ta ganshi sai taji ta shiryawa jin kunyar ko waye matuk'ar za ta nemawa mijinta lafiya tunda ba zina taje tayi ba.
Duk da kasancewar a buk'ace yake,bai bari notin kansa sun kunce ba yabi da ita a hankali yadda ba za ta wahala sosai ba.

Wayar Aasad ce a hannun Alisha tana dannawa,hotuna suka gama yi ya mantata a hannunta ya tafi,message ne ya shigo wayar daga saman ta fara karantawa.
"Akwai matsala fa,tsafin nan bazaiyi aiki akan Falisha ba." Sai gashi kamar an jefosa yazo ansar wayar,bashi tayi tana tattauna message in a ranta kafin ta tashi tabi bayansa, tana fita yana shiga mota,a hannun Khalil ta anshi key in motar Aashiq ta shiga tayi saurin bin bayanshi.

Gidansa da ba kowa ne yasan da zamansa ba ta nufa,acan yake sharwoliyarsa da 'yan mata kala kala,bai lura da message in da aka turo masa ba har yaje gidan,Alisha kuwa daga nesa tayi parking in motarta bayan ta hango gidan da aka bud'e masa ya shiga da motarsa,sai da ta bari ya d'an jima da shiga kana taje tayi knocking in gate in gidan,ganin mace ce yasa me gadin bai hanata shiga ba,kai tsaye kamar ta san kan gidan ta kutsa kanta ciki.Yana shiga Baby ta taho da gudu ta shige jikinsa,rungumeta yayi tsam a jikinsa don yana samun yadda yake so a gurinta,shiyasa ya killaceta yake amfani da ita shi kad'ai,babu wani sirrinsa da ba ta sani ba,hatta auran da aka d'aura masa ta sani,ta kuma san auran manufa ne ahiyasa ba ta d'aga hankalinta ba,duk da tana kishinsa sosai,a dai dai lokacin wayarsa tayi ringing ya cirota daga aljihu,Baffa K'arami ne ke kiransa da sauri yayi peaking.
"Kana ina ne,ba kaga message in da na turo maka ba?"
"Ban lura ba gaskiya."
"Ok,cewa nayi akwai matsala,tsafin bazaiyi aiki akan Falisha ba,yanzu yaya zamuyi?"
"Za'a samu wanda zasu kasheta a daren da aka kaita itama,na tabbata daga kanta babu wata mace da za ta k'ara gigin auransa."
"Tom shikenan,na bar komai a hannunka"
Ji yayi kamar k'arar rufe k'ofa,yana waigawa Alisha na barin gurin da gudu,ta riga ta gama jin wayar da yayi,ta kuma ganshi rungume da mace,bai san sanda yayi wurgi da Baby dake jikinsa ba yabi bayan Alisha da gudun tsiya,wani irin gudu take cikin tashi hankali tana kuka har ta isa bakin motarta ta shiga ta jata da gudun gaske, Aasad na ganin ta shiga mota shima ya dawo ya shiga tasa motar hankalinsa a matuk'ar tashe yabi bayanta,wani irin gudu take na fitar hankali,ji takeyi kamar tayi tsuntsuwa ta ganta gaban Yayanta,ba ta tab'a da na sanin fita babu waya irin yau ba, ji takeyi kamar ta cire zuciyarta ta wullar ta d'auki wata sabuwa ta saka a k'irjinta,don zuciyarta tayi kuskuran son Aasad,sam bai dace ta soshi ko kad'an ba,duk da yanzun ma jin muguwar tsanarsa take wacce ba tasan ainihin daga inda take fitowa ba,burinta kawai a yanzu auransa dake kanta ya sauka a yau d'in da aka d'aurasa,idonta ya rufe gudu kawai take shararawa ba ta lura da daf in da ta taho ba kawai ta kutsa kai,aikwa ta daki motar tata ta hantsila ta kuma hantsilawa.

Jina jina aka d'auki Alisha aka nufi asibiti da ita,sai dai kan a k'arasa ma ta cika,hankalin Aasad ya tashi fiye da na da,don yana matuk'ar k'aunarta ita ta fara bid'e zuciyarsa kuma ita kad'ai zuciyar take nunfasawa,biyotan da yayi ma da ace ya kamata to ba wani abu zaiyi mata ba,d'auketa zaiyi har sai yasa an rufe bakinta kafin ya saketa,ashe ma ita duniyar za ta bari gaba d'aya, amman hakan baisa imani ya shiga zuciyarsa ba saboda an zareshi.
Chapter 58 · 0% Book details