Sashe 33
Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read
Azaba iri iri suka gana masa bayan sun gama bincikeshi ba su samu abinda suke so ba,kuma shi sam ya nuna musu bai san akan abinda suke magana ba don haka ogansu ya basu umarnin su kashe shi kawai ta yadda zargi bazai biyo kansu ba suje su wullar da shi a bakin shagonsa.
Wuya suka shak'e masa har sai da suka tabbatar ya daina numfashi kana suka sanyashi a mota suka zo suka wullar da shi anan bakin shagonsa, bayan sahun mutane ya auke gaba aya, to ko da Nusrat da Baffa Shamsu suka zo anan bakin shagon suka tarar da shi a yashe, Baffa Shamsu ya d'aukesa suka nufi hospital da shi Nusrat kuwa sai kuka take don sam ta kasa control in hawayen nata.
Kusan asibiti hudu sukaje babu gado sai a Gogel Hospital suka samu aka anshesa nan da nan aka bashi taimakon gaggawa anan suka gano doguwar suma yayi, sai da Nusrat taji wannan bayani na likitoci kana ta samu sanyi a ranta, amman duk da haka k'in bin Baffa Shamsu tayi tace yaje ita za ta k'arasa kwana da Baban, amman don Allah ya lek'a mata Yusra ba dad'i itama take ji ba.
Sai da garin Allah ya waye kana Baba ya farka, ya riga ya fidda tsammanin cigaba da rayuwa cikin duniya, ya saddakar a cikin kabari zai bud'i idanuwansa sai gashi ya bud'esu cikin duniya, sai dai bakinsa yayi mishi nauyi, kamar 'yar baiwa yake gani a kwance a k'asa amman baijin zai iya kiran sunanta, d'ankwalinta ta shimfid'a tayi sallar asuba sai a lokacin gwanin iya sata ya saceta ta takure cikin hijabinta.
Zuwan su Baffa Shamsu ne ya farkar da ita daga baccin da take kuma ta farka da mugun ciwon kai, akan Baba idonta ya fara sauka, duk sun bi sun zagayeshi kowa da tambayar da yake jefo masa bayan sannun da suke masa shi kwa sai binsu da ido kawai yake, murmushi ne ya sauka akan fuskarta sai taji ciwon kan da ta farka da shi yana raguwa a hankula tashi tayi ta k'arasa gaban gadon tana cewa.
"Sannu Baba,bara na kirawo likitan."
Jinjina mata kai yayi wanda babu wanda ya samu hakan daga gareshi sai ita kad'ai.
"To gwanar iya sai ki dinga nuna kamar kinfi kowa damuwa da shi, duk soyayyar da zaki masa baza dai ta huce wacce ni uwar da na kawo shi duniya nake masa ba, don haka kya iya dakatawa don tuni Shamsu ya tafi kirawo likitan tun da muka fuskanci ba ya magana."
Ba ta saurari zancen Iyan ba kawai tayi ficewarta, sauri kawai take zubawa sai ji tayi sunyi karo da mutum zuciyarta ce tayi wani irin harbawa har sai da ta danne k'irjinta tayi baya tana k'ok'arin tsugunawa ta d'aukowa mutumin sandansa da ya fad'i hannunsu ya sauka kai a tare d'agowa tayi tana me kallon fuskarsa yayin da shi kuma ya d'auki sandarsa ba tare da ko d'agowa yayi ya kalleta yayi gaba abinsa, fuskarshi kawai da ta kalla taji gabanta yayi wani mugun fad'uwa, a hankali kuma kyakkyawan murmushi ya bayyana a fuskarta can k'asan zuciyarta kuma taji tana fad'in.
"Kai kyakkyawa da shi, kamar yadda sandansa yake mai kyau."
Ganin tahowar Baffa Shamsu da likitan yasa ta juya ta koma d'akin har lokacin wani annuri ne ke fita akan fuskarta wanda ita kanta ba ta san dalilin zuwansa ba.(Nikwa nace bare kuma ni, ban sani ba ko masu karatu sun sani?)
"Zaiyi magana insha Allahu, yana buk'atar hutu ne sosai, don haka kamata yayi dukkaninku ku koma gida, muna da masu kula da marasa lafiyarmu don haka bama buk'atar d'an jinya ko d'aya, idan da matsala zan kirawo wayarka."
Yakai k'arshen maganar yana sauke idonsa akan Baffa Shamsu ma'ana da shi yake kenan yayin da Baffa Shamsun ya jinjina masa kai had'e da cewa duk su tashi su tafi, yayin da Nusrat tayi rau rau da ido za tayi kuka tacewa Baffa Shamsu.
"Wallahi duk sauran d'akunan naga da masu jiyya, shine zaice mu mu tafi, duk kulawar da za'a bashi ai ba ta kai wacce zamu ba shi ba."
"To ai su ba mu san irin ciwon nasu ba, shi ba kiji yace yana buk'atar hutu ba ?"
"Kai ka tsaya ma kana mata bayani me kafiyar tsiya ba a banza ba kika rasa mashin shini ai, naga in zaman jinyar nema nice zan zauna tun da mijina ne, ko kuma a bakacin uwarki zaki zauna tun da naga kishi kike tayata bayan rai."
"Me ya kawo maganar nan kuma Mamn Nimha, ku shige dan Allah muje."
"Kyaleta Shamsu ta wanke min ita tass, yarinya ta d'auki bak'in hali ta d'orawa ranta, kaga fa yadda ita da Yisra suka d'auki karan tsana suka d'orawa Shukhura don kawai yarinya 'yar albarka tana kula da mu, tafi son ta tare kawai a gindinsu saboda bak'in halin tsiya to ke wa ya hana ki fito da naki mijin."
"Allah dai ya kyauta, Iya don Allah ku muje ance ba ya son hayaniya kuma neman tayar da hayaniyar kuke."
Babu wanda ya kuma cewa komai suka d'unguma suka fita.
"Yayarmu ya jikin Baban, naga kuma dukkaninku kun dawo?"
Yusra ce da ke suyar waina ta jefowa Shukhuran wannan tambayar, tashi tayi jikin nata da d'an dama, to ganin an riga an hada komai na wainar miyarma tun jiya da daddare Yayartasun tq hadata to shine take yinta dalilin da yasa ma ba ta bisu asibitin ba kenan ta bari idan wainar ta k'are ta bi bayansu sai kuma gasu sun dawo.
"Da sauk'i jikin nasa, eh likatanne yace mu taho wai basa buk'atar 'yan jinya."
"To su kuma haka tsarin asibitin nasu yake, ko kwa akanmu suka fara yin hakan?"
"Wa ya san musu to Yusra."
Tana kawowa nan tai shigewarta d 'aki ziciyarta sam babu dad'i, kallo Yusran ta bita da shi tana jin kamar da akwai wani abu dake damin Yayartasun, sai kwa ga Amima tazo siyan waina kafin layi yazo kanta suna dan taba hira da Yusran sai kwa Yusran cewa tayi.
"Nikwa Amima akwai wani abu da ya faru da Yayarmu ne na ganta wani iri?"
Aikwa Amima ta kwashe komai ta gayawa Yusran, bak'in ciki yazowa Yusra wuya ta bud'e murya tace.
"To dai dad'in abin kowa yasan Katanga akai mana tsakaninmu da 'yar uwarmu saboda tsabar son abin duniya, kuma Allah yana nan ba ya,bacci bazai tab'a barin zalincin da akai mana ya tafi a banza ba, uwarmu kuwa da aka ambato tana kwance a kabarinta mun bar mutum da Allah don shi kadai zai mana maganinsa, miji kuwa ba ta isa ta bawa kanta ba sai ranar da Allah ya kawo mata shi, kuma muna nan da rai da lafiya na tabbata wata rana sai kun shiga inuwar Yayarmu, zuciyarta da ban take ba irin tamu bace ni da Shukhura don wallahi na tabbata Shukhura ta dawo hayyacinta ba za ta tab'a yafe muku ba amman Yayarmu kuwa duk abinda kukai mata ba shi zai hana watarana ta tsamo ku daga rana ta sanyaku cikin inuwarta ba."
Daga Iya har Umman duk suna jinta tana ta bambami babu wanda yayi tari alamun yana jinta, don Yura iskokan nata ma sunfi na Shukhura tsaf zuciya za ta jaho ta canja musu kamanni in suka kulata.
Bayan sallar azahar Yusra tacewa Yayarsu ta tashi ta rakata gurin Baba itama ta ganshi in yaso sai su dawo, tashi tayi ta shirya don itama hankalinta gaba d'aya yana kan Baban, nik'af inta ta sanya kana suka fito suka rufe d'akinsu suka tafi, ko da sukaje zasu shiga d'akin da Baban yake sai aka hanasu shiga ganin hakan yasa Nusrat ta nufi office in likitan, ta kai hannu za ta b'urd'a handle in k'ofar taji wata kakkausar murya na fad'in.
"Wannan allurar kawai zakai masa itace za ta k'arasa shi har lahira."
Da sauri ta d'auke hannunta daga kai jikinta yana wani irin rawa, tayi saurin barin gurin a gigice.
Dama haka asibitinnan yake kashe mutane suke yi, ko wa kuma zasu kashe?Shine abinda zuciyarta ke ta tambayarta kuma bata da me bata amsa, gaba d'aya nutsuwa ta bar gangar jikinta, Yusra sai tambayarta take meke faruwa amman ce mata take kawai ki bari bana cikin hayycina Yusra.
"To kenan baza muga Baban ba."
"To dai gashi sun hanamu ganinsa Yusra, ni bansan asibitinn me suke nufi da mu ba wallahi."
Takai k'arshen maganar kamar za ta kece da kuka, Yusra kuwa bayan wata nurse ta bi ta had'ata Allah annabi akan ta taimaketa taga mahaifinta, nurs in ta rasa yadda za tayi da Yusra duk ta inda ta b'ullo mata sai ta goce, k'arshe dai wasu kayan ta bata irin wanda nurs in ke sakawa tace ta saka sai ta shiga babu wanda zai hanata, godiya Yusran tayi mata ta karb'a ta saka, kasancewar tana da tsayi da girman jiki babu wanda zaice shekarunta goma sha uku kacal, har tazo ta shige Nusrat ba ta lura ba saboda gaba d'aya hankalinta yana kan office in likitan so take taga shi da waye zasu fito daga ciki.
Sun samu labarin Baba bai rasu ba don haka suka shiga binciken wani asibiti aka kaishi daga k'arshe suka gano yana nan gogel hospital, shine ogan nasu yayiwa likitan waya akan kar ya bar kowa nasa yaje inda yake, wannan dalilin ne yasa aka koresu zuwa gida yanzu kuma aka hanasu ganinshi, ogan nasu kuma yazo da kansa gurin likitan saboda kasancewar asibitin a k'ark'ashinsu yake kuma likitan ya saba mishi irin wannan aikin idan buk'atar hakan ta taso, shiyasa suka k'ule cikin office insa suna tattaunawa wanda tsautsayi yasa Nusrat ta jiyowa kunnuwanta abinda ya rikirkitata.