← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 69

Sashe 36

Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read

Biyar da rabi dai-dai suka isa kano unguwar Naibawa, Nusrat sai kallon unguwar take yadda duk ta bi ta canja mata a 'yan shekarun da ta iba ba tazo ba, duk da dai ta jima sosai don tunkan ta bar secondary rabonta da zuwa hutu, unguwa ce ta masu hannu da shuni gidaje ne ga sunan wannan yana wane wannan, gidan Aunty Maryam inma an gyare shi sosai da sosai ba kamar yadda ta sanshi a baya ba da alamu kud'i sun kuma ninkuwa kenan.
A cikin jerin d'akunan dake k'asa Aunty Maryam in tace Nusrat ta shiga ciki da kayanta da Driver ya shigo da su, tana shiga toilet kawai ta fad'a ta d'auro auwala a gaggauce saboda la'asar d'in da basu samu sunyi ba bcs a hanya ta riskesu, abin sallah ta shimfid'a kana ta kalli gabas had'e da tattara dukkanin wata nutsuwa tata.
Bayan ta idar da sallar ta hau k'arewa d'akin kallo, tsaf yake baya buk'atar gyaran komai sai d'an abinda ba'a rasa ba, bcs kullum masu gyara falon sai sun gyara har da d'akunan da babu kowa a ciki saboda wani zubin mutan gidan sukan amfani da shi da kuma gudun yin bak'o katsaham, tana shirin kishingid'ewa kenan saboda kwankwasonta da ya d'an rik'e sakamakon zaman motar da tayi, tunda yau sha rabonta da yin doguwar tafiya irin haka, dama dai doguwar tafiyar tata iya kacinta kano ba dad'i ba ragi,kuma gashi dama Nusrat in ba gwanar zama bace, haka kawai dai ba abinda take a ganta a zaune gaskiya kam da wuya, muryar Aunty Maryam ce ta katseta daga kishingid'ar da taso yi sakamakon k'walla kiran sunanta da tayi, amsawa tayi had'e da mayar da hijabinta da ta cire ta fita.
A tsaye ta tarar da ita tana jiran fitowar tata, don haka tana fitowa ta kalleta had'e da fad'in.
‘‘Yauwa cewa nayi ki d'an shiga kitchen ki sama mana abinda zamui dinner da shi, Hibba kuje ki nuna mata inda komai yake, zanje na watsa ruwa ne.‘’
‘’Ok Mom‘’
Hibba dake kwance a kushin tana kallo, don Hibba mayyar kallo ce, ta amsa mata da hakan, kallon Nusrat in tayi tace.
‘’Muje Yayarmu‘’

Jalof in taliya tayi wacce tasha su piece, grean beans,carrot, da kuma sadin, sai zuba k'amshi take saboda spices in da tayi amfani da shi, da taurinta sosai da kuma ruwanta ta juyeta a cikin wata k'atuwar warmas, bcs kan azo ci zata k'arasa dahuwa a ciki, idan kwa ta barta ta dahu to zata k'ara dafewa ne kan azo ci, tana cikin had'a cole slow Hibba ta shigo kicthen in tace.
"Mom tace, ki had'a juice ta manta ba ta gaya miki ba, mu kinsan gidannan ba ma cin abinci sai da juice gashi kuma dukkaninmu ba ma shan me gas, Aunty Hidaya ce kad'ai me sha, itama kuma coc kad'ai take sha shiyasa Dad yake ajiyewa saboda ita, shi kuma saboda ulcer insa ne ya daina sha, don a gurinsa Aunty Hidaya ta koyi shan coc, amman tunda ulcer taci k'arfinsa ya hak'ura."
"Yanzu duk wannan bayanin Aunty Maryam d'in tace kizo kimin?"
Dariya tayi had'e da girgiza mata kai, kafin tace.
"Nice dai kawai na baki labari, yauwa na ma manta karfa kiyi wanke-wanke muna da me wanke-wanke."
Tana kawowa nan ta juya da gudu tunawa da tayi ana ta huceta a film in da take kalla a tashar tauraruwa, Nusrat kuwa a ranta tace dama bata da niyar yin wani wanke-wanke don a rayuwarta abinda tafi tsana kenan ta gwammace ta huni tana girki akan tayi wanke-wanke sau d'aya, don da basu da me wanke-wanken kuwa sai dai Hibba tayi don ba ta jin za tayi, sai dai kuma idan Aunty Maryam ince tace tayi shine za tayi don ba yadda za tayi.
Tana gama had'a coleslow in ta had'a ginger juice kana ta jere su akan dining had'e da dukkan abinda za'a buk'ata kana ta shige d'akinta a lokacin an jima da kiran sallar magariba, wanka tayi da ruwa mai zafi sosai had'e da d'auro alwala ta gabatar da sallarta ta magariba, kana ta zauna jan carbi, jin an murda k'ofar zaa shigo yasata d'ora idanta akai don ganin me shigowar, Hidaya ce, da gudunta ta taho ta rungumeta.
"Amma naji dad'in zuwanki Yayarmu sosai da sosai, sam Momy bata gayan tare zaku taho ba, yanzunma shigowata kenan Hibba take gayan."
Murmushi Nusrat in tayi had'e da fad'in.
‘’Har haka kuke kaiwa a makaratar baku dawo ba?"
"Kedai bari, wataranma ina huce haka, donma yau babu cushewar ababan hawa sosai, muna da nisane tsakaninmu da Buk d'in, kuma Exxam in yau ta cajan kai sai shida na fito, yanzun ma a gajiye na dawo likis wanka kawai nake bukata sai Hibba tace min dake aka taho."
"Sannunki to kije in kika huta ma had'u, tunda dai burinki ya cika an taho da ni."
Dariya Hidayan tayi kafin tace.
"To ke me kike anan ne? Dakin baki ne fa."
"Aunty Maryam ce tace na shigo nan d'in ai."
"Kinji Momy da wani zance, babu fa kowa a k'asan sai su Abdul da Abbas mu duk muna sama, d'ebo kayanki mu koma d'akina."
Wani mugun sanyi Nusrat in taji a ranta, don tun d'azu take tunanin yadda zata kwana ita kad'ai a cikin wannan d'akin, amman kuma duk da haka sai ta kalli Hidayan tace.
"Kidai fara gayawa Aunty Maryam in muji me zata ce."
Tsaki Hidayan taja had'e da d'aukan d'aya daga cikin jakar katan Nusrat in tayi gaba tana fad'in.
"Malama ki taso, nasan zaki takura idan kika kwana ke kad'ai a cikin d'akin nan, kin manta idan kika zo a cikin d'akina kike sauka, wannan ma bansan dalilin da yasa Momyn tace ki shigo nan d'in ba."
"To ai wancan zuwa nayi na tafi, wannan kuwa zuwa ne na bansan ranar tafiyata ba."
Hidaya dai tayi gaba don bai zama lallai taji me tace ba, Hibba tacewa ta biyota da jakarta da littattafan da ta watsar akan kushin ta haye staires da jakar kayan Nusrat in, sai da ta fara shiga d'akinta ta ajiye kana ta nufi d'akin Mom in tasu, akan sallaya ta tarar da ota da alamu jira take a kira sallar isha ta gabatar da ita kana ta shirya tarbar Dad insu don ga komai nata nan ta fito da shi ta dora a gefen gado.
"Momy Sannunku da dawowa, ya hanya?"
"Yauwa Hidaya, sai yanzu, ya paper?"
"Alhmdlillh Mom, ashe tare kuka taho da Yayarmu?"
"Eh saboda girki na taho da ita, ga azumi yana tahowa ."
"To amma Mom me yasa kika ce ta zauna a d'akin k'asa?"
"To wani d'aki kike so na bata, kinsan dai babu wani daki da ya rage a samannan idan kuma ba ni kike so na fita ba bata nawa ba."
"Wa Ni na isa?cewa nayi ta dawo dakina, kinsan ba ta saba kwana ita kad'ai ba."
"Babu matsala, tunda kinga zaki iya hakan, ni bara nayi sallah."
Takai k'arshen maganar tana k'ok'arin mik'ewa jin hakan yasa Hidaya tashi ta fita daga dakin..

#NWA
#KTG
[4/26, 8:43 PM] Rabi: BEBE'ARTH

Wattpad@Rashuna

®️NAGARTA WRI.ASOCIATION

KATANGA...

In baki siya ba ya kamata ki mallaki naki a hannu kar garab'asar ta wuce ki, in na gama free page zaki siyeshi akan 300 ne,kuma in kin siya yanzu zaki samu damar karanta CIN AMANA kyauta, kada ku bari wannan garabasar ta wuceku, kada ku manta akwai abin amfani a ciki.

Masu tambayata document in na gama, shi kuma zaku sameshi akan 500kacal.

...............21

"Kinsan ban fiya son jalof in taliya ba in ba a lokacin da aka gamata zanci ba."
Cewar Dad in Hidaya yayin da Aunty Maryam ke saving insa.
"Afuwa nake nema Daddynsu, kasancewar yamma tayi shiyasa nace tayi sassauk'an abu."
Hade fuskarsa yayi kafin ya tambayeta.
"Waye yayi?"
"Nusrat ce"
"Wace Nusrat in?"
"Nusrat d'in Yaya Audu."
"Kai, amma wallahi kin mugun kyautawa, meyasa baki hado da Yusran ba?"
"Wallahi nima da har da ita naso tahowa, to d'an uwan mahaifiyarsu ne ya d'auketa."
"To ai shi kenan tunda mun samu Nusrat d'in."
Daga haka yayi bismillah ya fara cin abincinsa don har ta gama saving nasa ta yiwa kanta, kana Abbas da Abdul kowa ya zuba yadda yake buk'ata, sunyi nisa da fara ci kafin Nusrat da Hidaya su fito, Hidaya ce tayi saving in Nusrat kana taiwa kanta suka fara ci ba tare da ko tari sunyi ba saboda dokar Daddy ce ba'a magana yayin da ake cin abinci.
Chapter 36 · 0% Book details