Sashe 15
Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ringin d'aya Shukhuran ta d'aga da murnarta tace.
"Hello Ma.......“
Cak taji maganarta ta tsaya ta kasa furta Maman da take buk'atar fad'a, Mama ji tayi gabanta ya yanke ya fad'i a hankula ta furta.
"Innalillahi wainna ilaihir raji'un.“
Kafin taji saukar kukan Shukhura a kunnenta.
"Shukhura lafiyarki kuwa?“
Cikin kuka tace.
"Nima ban san me ke damuna ba, daku na kwanta a raina da ku kuma na tashi, tun da mukai sallar asuba nake son kiran wayarku amman na k'asa, sai na ji ana rad'a mini a kunnena wai ke ba mahaifiyata bace, Umma ce mahaifiyata ko kuma ace su Yayarmu ba 'yan uwana bane Nimha ce kad'ai 'yar uwata, na san Yayarmu ta damu sosai amman wallahi ko muryarta ba na son jin, ina cikin damuwa zuciyata ta na mini zafi, da na san haka auren zai zo mini da babu abinda zai sakani yinshi. “
Ta na kawowa nan ta fashe da wani matsanancin kuka, Mama kuwa Innalillahi kawai take ambata a zuciyarta, yayin da Nusrat duk ta na jin abubuwan da Shukhuran ta fad'a, had'a kanta tai da guiwa ta fashe da kuka me ciwo, 'yar uwarta da take sonta fiye da son da takewa kanta yau itace ta furta ba ta son jin muryarta, me yake shirin tunkaro rayuwarsu ne, waye me buk'atar rusa Katangar farin cikin da suka dad'e da ginata a zuciyoyinsu?
Majina Shukhura ta jaa taci gaba da cewa.
"Mama kicewa Umma me mukai mata take son rusa rayuwarmu gaba d'aya, in wani abu mukai mata sai mu nemi yafiyarta, na san dai itace ta shiga tsakaninmu saboda da sassafe ita na fara kira na gaisar, bayan ko anan cikin gidan ba kullum nake gaisheta ba. “
Numfasawa Mama tayi tace.
"Umma ba ta isa ta miki komai ba Shukhura, ki saka hakan a ranki, babu wani abu wanda yake faruwa a rayuwa face dole sai da wani zare da ya haddasa hakan, kuma bama iya ganin zaren, shi wannan zaren shi ake kira ZANEN K'ADDARA.
Dan haka kada ki kuma danganta abinda ya same ki da wani d'an adam, duk abinda ya sameki to ki tabbata yana cikin k'addararki, ki kuma kai kukanki ga Ubangiji domin shi kad'aine zai baki ikon cinye jarabawar da yai miki har ya yaye miki abinda ke damunki, yanzu kije kiyo auwala ki d'auki qur'ani ki karanta za kiji sanyi a ranki, maza jeki, Allah yayi miki albarka, ki kuma daina wannan kukan.“
Muryarta can k'asa tace.
"Tom“
Mama ta kashe wayar ta lumshe idonta kana ta bud'esu akan Nusrat da ke gurshek'an kuka......
Jiya ba ku jini ba, chargi ne ban samu ba wutarmu ta lalace, gobe da jibi ba lallai ne ku jini ba saboda muna hidimar biki.
300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.
Allah ka k'arawa
mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.
#N.W.A
#Team KTG
#Son so fisabilillah[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*
28/8/2020
Wattpad@Rashuna
*KATANGA*
_Ina matuk'ar godiya ga Allah (S.W.T) da zai ba ni ikon kawo muku wannan littafi mai suna KTG, ina fatan yadda zan fara cikin yalwatacciyar lafiya na kammalashi haka, Amin summa Amin_
_Sak'on gaisuwa ga 'yan uwa da abokan arzik'i, da kuma dukkanin masoyana na kusa da nesa, ina kuma fatan za ku bani had'in kai cikin wannan littafin, kalma d'aya kawai zan gaya muku, alk'alamin ya fi mashi tsini, kuyi k'ok'ari kui nitso ku ninkaya cikin wannan sabon alk'alamin mai suna *KATANGA*_
_Hak'k'in mallaka:_
*RABEE'AH SHU'AYB NABABA*
(RASHUNA)
____________
*ONE*
_Bismillahir rahamanir rahim._
*SHIMFID'A*
Malam Ahmadu an haifeshi a garin Zaria, asalin malantarsa ya gadota ne a gurin mahaifinsa Malam Buba, kasancewar kuma tun ya na yaro mahaifiyarsa ta rasu, tare ya rayu da mahaifinsa har sai da ya yi aure da matarsa Asabe sannan Allah ya karb'i ran malam Buba, daga nan Malam Ahmadu ya ci gaba da jan ragamar mahaifinsa ta malamta.
'Ya'ya uku Allah ya azurtasa da shi, Abdullahi, Maryam sai autansa Shamsu, Abdullahi shine ya gado mahaifinsa amman kuma ba a iya malamtar ya tsaya ba ya na da shago a kasuwa da yake sayar da kayan awo.
Malam Ahmadu shine ya zab'awa Abdullahi mata, 'yar amininsa ce k'ud da k'ud da Allah ya karb'i ransu shi da matarsa shekarun baya da suka wuce, kasancewar gidan nasu gidan yawane, kuma auran zumunci akayi tsakanin mahaifan nata, haka take ta watan gari riya a cikin gidan sai uwar bauta da take musu, tausayinta da duba maraicinta da amuntakar da ke tsakaninsa da mahaifinta hakanne yasa ya nemawa Abdullahi auranta, Abdullahi baiyi musu ba kasancewar ya yaba da d'abiunta kuma ta na yawan burgeshi a duk sailin da zasu had'u hakan yasa ya karb'i tayin auranta da hannu bibbiyu.
A gurin Asabe wacce yanzu suke kira da Iya aka fara samun k'alubale, inda ta yi tsalle ta dire akan d'anta ba zai auri 'yar makafi ba, kasancewar mahaifanta duk makafi ne, shikuwa Malam Ahmadu yace ta yi kad'an ta hana wannan auran, idan har taga ba'ayi sa ba to tabbas babu ransa a Duniya.
Abdullahi da Maimuna sun aminta da juna sosai ya yin da suka fad'a zazzafar soyayya nan da nan magabata suka shiga lamuran nasu, a lokacin ne kuma wanda yake neman auran Maryam me suna Yusuf ya fito, a kano yake a zaune aiki ne ya kawosa zaria, tun ganin farko da yaiwa Maryam ya aminta da ita, bai fara zuwa zance ba sai da Malam ya yi masa izini, daga bisani kuma yace ya turo magabatansa.
An tsayar da ranar auran Abdullahi da Maryam lokaci guda .
Anan cikin gidan, Malam Ahmadu ya yanki gefe ya yiwa Abdullahi gini, d'akuna uku ne maka² abinsa a wadace, ya yi musu kuma k'ofar gurinsu da ban, sannan kuma ya had'a masa lefe dai-dai da zamanin da suke ciki.
Ansha shagalin biki kafin a kawo amarya sashinta, ita kuma Maryam aka kaita unguwar Sabon gari.
Lafiya lau zaman Abdullahi da Maimuna yake babu wata matsala ko d'aya, Malam ya d'ebo soyayyar duniya ya d'orawa surukar tasa, kullum in zai shigo gida da abinda zai aika mata da shi, ya yin da Iya kuwa ta bi ta tsaneta, ko kad'an ba ta sakar mata fuska kyara da tsangwama shine tsakaninsu.
Wata d'aya da bikinsu Allah ya azurtata da samun juna biyu, tattali da kulawa fiye da wacce take samu ada Malam yake mata, idan ya fita duk abinda ya san me ciki na sha'awa shi yake siyo mata, Iya kuwa tayi ta sababi a tsakar gida ta na masifar ga d'iyarsa can ta na da juna biyun amma ba ya ta tata ya tare a bayan sirika, ya taka k'afa ma yaje ya gano d'akinta baije ba don tsabar tab'ewa da lalacewa, ci kanki kuwa Malam ba yace mata sai dai yai ta murmushi idan ta na yi ya nai mata uzurin k'wak'walwarta ta goce.
Cikin Maimuna na shiga wata tara cif, ta haifi kyakkyawar yarinyarta sankace ciya, da hak'oranta guda biyu na k'asa, tsakanin Abdullahi da Malam ban san wanda ya fi wani farin ciki ba, Malam fad'i yake an haifar masa jika 'Yar baiwa, mutane kuwa da wanda Maimuna ta sani da wanda ba ta sani ba sai tururuwar zuwa barka suke, wasu ma don suga hak'oran ne kawai yake kawo su, don duk wanda yazo sai ya d'aga bakin ya gani, sai dai kawai Maimuna ta yi murmushi.
Iya kuwa ko lek'owa taga jikarta ba ta yi ba, illa ma bak'in ciki da take kamar ranta zai fita, saboda yadda taga malam ya na rawar k'afa ya samu jika 'Yar baiwa, don har ya siyo raguna biyu tik'a² ya tirkesu bakin nan yak'i rufuwa, Iya kuwa tace.
"Inma za ka daina farin ciki ka daina, shawara nake baku ku d'auki 'yar nan ku kaita bakin ruwa don wallahi 'yar aljanu ce ba 'yar baiwa ba. “
Murmushi kawai Malam ya yi baice da ita komai ba don ya san bak'in ciki ne ya taru yai mata yawa.
Ansha shagalin suna yadda ba kwa zato, yarinya taci sunan babar Malam AYSHA, Maimuna tace a dinga kiranta da NUSRAT, yayin da Malam ya d'ebo soyayya,tattali gami da kulawa ya aza akan 'Yar baiwa.
Wata d'aya tsira Maryam ma ta haifi 'yarta mace taci sunan babar Yusuf RABEE'AH suke kiranta da HIDAYA.
Watan Nusrat uku a duniya Iya ta matsawa Ahmadu number sai ya k'ara aure, wata bazawara ce nan mak'otansu da take shigo mata, mijinta mutuwa ya yi kuma mai bala'in kud'i ne, siyayya take yowa Iya sosai da haka ta siyeta, don dama burinta kenan ta tirsasa d'an nata ya aureta, don ta tareshi da buk'atarta ya yi mata kaca² hakanne yasa ta biyo ta gurin Iya.
Don a samu zaman lafiya Malam yacewa Abdullahi ya aureta, itama ya bi zab'inta,ko a samu k'iyayyar da takewa Maimuna ta ragu, don fad'i take yaiwa mahaifinsa biyayya amman ita saboda bai d'auketa a bakin komai ba ya watsa mata k'asa a ido ta ya ya kwa za ta k'aunaci Maimuna?