← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 69

Sashe 69

Katanga Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Wai ke Yusra jik'aki zanyi ne na shanye,duk wanda yazo da sunan yana sonki sai kice,ba kya so?"
Nusrat ce ta jefowa Yusra wannan tambayar,yayin da Yusran tace. "Ni da zaki jik'ani ki shanye d'inma da na huta kullum da tunanin yin nesa da ke." Takai k'arshen maganar tanawa Ashna da Ashfaq wasa da sukayi b'ul b'ul da su kamar ba 'yan wata hud'u ba,harara Nusrat ta zabga mata kafin tace. "To shikenan zan bawa Ya'u ke,kinga kin huta gani gaki" Direban Yusra ne Ya'un,yana mugun sonta,shiyasa basa shiri kullum cikin zaginsa take. "Ba sai an bawa Ya'u ba gani ina so,babu wani tunanin yin nesa da Yayarmu." Cewar Asghar yana shigowa ciki. "Hala da wasa kake don ba da ni za'ayi wannan d'anyan aikin ba,da wani idon kake son na dubi Ramla?"
"Da idon da kike dubana kullum." Cewar Ramla itama tana shigowa ciki,ganin haka yasa Yusra ta d'auke Ashfaq da Ashna ta silale ta bar falon,da gaske Asghar yake yana son Yusra sai dai Nusrat,ta kafe ba za ta bashi ba,sai da Ramla ta sanya baki ta kuma gaya mata cewar tun haihuwar Safa da Marwa da tayi ta samu matsala a mahaifarta wanda da wuya ta k'ara d'aukar ciki,Asghar yana son Yusra ba ta isa ta hanashi sonta ba ko da ta hanashi auranta,kuma zai iya auro mata wacce ba ta sani ba ba ta san halayyarta ba gara Yusra ko ba komai k'anwarta ce,Nusrat ta nuna ba ta son su samu sab'ani ne don akan Yusra za ta iya sauka akan ko wani mataki, kar azo ana wallahi tallahi,sai da suka had'u su biyun suna bata baki,da k'yar tace za taji ta bakin Yusran idan tana sonshi za ta amince,idan ba ta sanshi baza ta masa dole ba,godiya suka yi mata don suna da yak'inin cewar Yusran baza tak'i ba, don yasan tunin dama ya dad'e da fara gina kansa gurin Yusran shiyasa tak'i saurarar kowa.

Wanka suka fito manne da juna,yana mata rad'a a kunne,kafin yace."Ashe dai yarona ne ya k'ara miki dad'i,shiyasa a kwanakin nan nake jinki har k'wak'walwata." Kaucewa tayi tana masa hararar wasa kafin tace. "Ko da yaushe dama hakan nake,kai kanka ka sani." Bakinsa yakai kan idanuwan nata ya mata kiss kana yace. "Na sani,ke d'in ta dabance,kullum kamar k'ara miki zsk'i ake,kina kaini duniyar da nake jin tamkar mu dauwama ko da yaushe a cikinta." Kafin tace wani abu suka ji muryar Shukhura tana k'walla mata kira. "Yayarmu" Kamar zata fasa gidan. "Innalillahi,shi kenan zaki mini wuyar gani" Cewar Aashiq yana dak'una fuska,had'e da matseta cikin jikinsa kamar Shukhuran ya gani zata k'waceta,dariya Nusrat d'in tayi,yace. "Au dariya kike?Wallahi da gaske nake idan Shukhura na nan ganinki wahala yakemun,sai munzo kwanciya,sai kuma ki fara wash na gaji." Yakai k'arshen maganar yana kwatanta tadda take,dariya ta kuma yi, da k'yar dai ta samu ya saketa ta sako doguwar riga ta fito,har lokacin Shukhura ba ta hak'ura da kiran sunanta ba,transfer suka karb'o sun dawo zariya da aiki daga ita har Mustaphan,murna Nusrat ta shiga taya ta,don tasan saboda ita ne ta nace sai da suka komo zariyan,anan Shukhuran take gaya mata tana da ciki,kema Yayarmu naga kamar ciki ne da ke? Nusrat tace."Ke dai ban san ta ina kike hangar ina da ciki ba Shukhura?" "Jikina ne ya bani kinsan ni dake Yayarmu abu d'aya ne,Allah ne yayi baza mu zauna a mahaifa d'aya ba." "Nidai duk randa Aunty Shukhura tazo Yayarmu daina saurarata kike duk tabi ta k'wace min ke." Cewar Yusra,yayin da Shukhura tace."Kuma babu yadda za'ayi da ni ba,munma dawo zariya da zama,Yaa Aashiq ma nan ya ganni ya k'yakeleni." Dariya Nusrat ta saki tana jin so da k'aunar k'annanta na k'ara gudu cikin jini da jijiyarta,hira suka shiga yi duka su ukun,yawanci duk hirar Mama suke,suna yi suna hawaye,sun yanke zasu gina masallatai da makarantu,Allah yakai ladan kabarinta,yayi mata sakamako da gidan Aljanna sakamakon irin tarbiyar da ta basu wacce itace suke rik'e da ita har yanzu,kuma da ita zasui amfani akan 'ya'yansu suma su gina musu irin KATANGAR da ta gina a tsakaninsu.

ALHAMDLILLAH

Kuskuran dake ciki Allah ka yafe mana,ya kuma had'amu cikin ladan gaba d'aya.

Irin wannan KATANGAR nake son ginawa zuri'ata idan Allah ya nufa zan haifa,domin irinta ce mahaifiyarmu ta gina tsakanina da 'yan uwana,Allah ya biyata da gidan aljanna.

Bintu Abba ina matuk'ar godiya,domin ke d'in ta daban ce,kinmin halacci,nima zan miki halacci,daga KATANGA kin gama siyan littafina zaki dinga karantashi kyauta,kuma da kuka sanya kud'inku kuka bani lokacinku na gode.

NAGARTA WRITERS ASOCIATION Baffa K'aramihttps://www.instagram.com/tv/CfLq0VxgK_u/?igshid=YmMyMTA2M2Y=
Chapter 69 · 0% Book details