Sashe 27
Katanga Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kayan toshi ma da aka kawowa Shukhura k'arara Umma ta nuna bak'in cikinta a gurin, duk da Saminu ma ya yi dai² k'ok'arinsa amman ta raina ta na ta tsine masa albarka, ta na kiransa me kantar talauci, azumi kawai take jira ya k'are ayi sallah ta dugunzuma neman mafita, cikin k'udurar Ubangiji akai sallah lafiya aka gama lafiya, aikuwa ta shiga can cikin k'auyen zariya acan ta samo wani malami, ya shaida mata kud'in aikinta dubu ashirin idan har ta kawo dubu ashirin d'innan to tabbas wannan aure bazai tabbata ba, jiki na rawa ta dawo gida ta sayar da kayan gadonta gaba d'aya ta koma ta kai masa yace to yanzu ta koma taje ta kawo masa k'asar da Mustapha ya taka, idan ta kawota to tabbas da kansa zai zo yace ya fasa wannan aure, shi kuma Saminu za mu juyar masa da ra'ayi da kansa zaice ya fasa auran Nimha, kinga daga nan sai mu juyo da hankalin Mustapha kan Nimha.
Farin ciki sosai Umma tai da jin jawabin Malamin, aikuwa ranar da Mustapha yazo ta k'asa ta tsare ta na jiran shigowar Shukhura ta yi sauri ta fice ta d'ebo k'asar da Mustapha zai taka, aikuwa ta na ganin shigowar Shukhuran ta yi saurin ficewa ta 'yebo washe gari taje ta kaiwa malamin aikuwa yace ta na kwance za ta ji kyakkyawan labari...
300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.
Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.
Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.
#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *KTG*
Wattpad@Rashuna
https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_
____________
*TEN*
KWANCI TASHI
Gurin Ubangiji ba wuya, su Shukhura har sun yi candy, sati d'aya da yin candynsu aka kawo lefen su.
Akwatina 6 haka Saminu yaiwa Nimha, kuma ya yi iya k'arfinsa kayanta babu kushe ko d'aya, Shukhura kuwa akwatina goma sha biyu dank'are da kaya na alfarma, sark'ok'in daham kuwa zasu kai 6 a ciki, nan da nan hankalin Umma ya k'ara tashi, ta fuskanci wannan malamin kawai kud'inta yake ci dole ta canja shik'a.
Wani k'ungurmun boka ta kuma samowa shi ya sanar mata.
"Duk wanda yace miki wannan aure bazai tabbata ba to tabbas yai miki k'arya, kud'inki kawai yake ci, wannan aure muk'addari ne daga Ubangiji kuma babu makawa sai ya faru, don haka kije ki rungumi k'addarar da tazo miki da hannu bibbiyu.“
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu babu wata mafita? “
" Babu wata mafita indai akan hana auran nan ne, sai dai wani da ban kuma, don wannan ba makawa sai ya tabbata. “
Shiru Umma tai hankalinta in yai dubu ya tashi, yanzu dole ta koma ta d'ebi cin kashi gurin kishiyarta, haka za ta zauna ta na kallon Shukhura na d'agawa da fariya ta na auren me kud'i, komai ta yayibo ta kaiwa uwarta ta na zaune kamar jaka, 'yarta kuwa sai dai ta yayibo kantar talaucinsu ta juye mata, ina bazai yuyu ba da sake, to kuma ta ya ya?
Koma ta yaya ne ta bawa zuciyarta amsa daga bisani ta kalli bokon za tai magana ya dakatar da ita da hannu d'aya.
"Kud'in aikinki dubu d'ari biyu, za ki kawo mini dubu hamsin da bak'ak'en kaji guda shida, idan aiki ya tabbata sai ki ciko dubu d'ari da hamsin, amman idan har kina so aikin ya kama jikinta sosai sai idan babu ran mahaifiyarta. “
'Ta yadda da ingancin aikin bokan nan, tun da har ya san abinda ke zuciyarta, to amman kuma ta ya ya mahaifiyarta za ta rasu bayan ranta ba a hannunsu yake ba?.'
Maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi.
"Zan tura mata ciwon da zaiyi sanadiyar mutuwarta, daga nan ba ki da sauran Katanga tsakaninki da Shukhura, ke za ta dingaiwa kallon mahaifiyarta, amman kafin nan sai an fara raba tsakaninsu da me gidanku, a kuma rufe bakinsa, babu case ga wannan tsohuwar matar idan har kina sakar mata abin Duniya. Su kuma 'yan uwanta za'a raba soyayyar da ke tsakaninsu, saboda ta na matuk'ar son su fiye da son da takewa kanta.“
Farin ciki ne ya dabaibaye zuciyar Umma, ta dinga sharara masa godiya, suka rabu akan za ta dawo ta kawo masa abinda ya Buk'ata.“
Akwatinan Nimha ta kwashe da wasu kaya daga ciki taje ta sayar ta kai masa kud'in da kajin da ya buk'ata, ya bata wani ku'ullikan magani, d'aya ta zuba a cikin abincin da Mama za ta ci, d'aya ta zuba cikin ruwan turaren da za'aiwa Shukhura kamu da shi, d'aya cikin abincin da Baba zai ci, sai laya da za ta saka a bayan gadon Shukhuran, babu wanda zai lura da layar sai ita da ta saka da kanta, sauran abubuwan kuma shi zai ji da komai.
Shirye²n biki su Mama suke hankali kwance, don yanzu saura sati guda a fara shagul gulan biki, duk da Mama ta fara fuskantar wasu sauye² daga Baba hakan baisa ta tayar da hankalinta ba, da Allah ta dogara shi kuma taci gaba da mik'awa buk'atunta, don a 'yan kwanakin nan wasu mugayen mafarkai take mara dad'in ji ko kad'an, kawai ta na danne damuwarta ne saboda yaranta, don wani abu da Shukhura kuma ta tsira shine, duk dare sai ta sanyata a gaba ta na kuka ta na rok'onta akan a fasa wannan bikin, ta na jin kamar wani babban al'amari zai tunkaro su idan har akayi wannan auran, sai dai ta lallasheta da nasihohi masu ratsa jiki, don babu damar tunkarar Baba da wannan maganar, bare ya dube su, don ita kanta Mama yanzu ba ta buk'atar auran, to Baban gaba d'aya yanzu ya sauya musu da Nusrat kad'ai yake zama ya yi hira, hakan ya kuma tayar da hankalinsu gaba d'aya amman a haka suka daure suka cigaba da shirye shiryen da ba'a rasa ba.
Ranar juma'a akai kamu anan cikin gidan, Iya ce ta kama duka amaren guda biyu, yayin da taiwa Shukhura amfani da turaren Nimha, taiwa Nimha da na Shukhura wannan kuma duk tsarin Umma ne.
Ranar juma'ar da daddare akai Dinner d'in gidan su Mustapha, da Baba yace Shukhura ba za ta ba, da k'yar Nusrat ta lallab'a shi ya barsu suka je, kuma diner d'in ta k'ayatar da dukkan wanda ya halarci gurin.
Washe gari asabar sukayi walima anan cikin gidan don Baba ya hana DJ kuma walimar ta yi gwanin ban sha'awa.
Washe gari lahadi kuma aka d'aura auran.
Safiya Abdullahi Ahmad da angonta
Mustapha Faruoq Fanda
Zainab Abdullahi Ahmad da angon ta.
Saminu Yusha'u Hamza.
Tun da aka d'aura auran Shukhura da Nusrat ke kuka, gaba d'ayansu suna jin wani miki a zuciyarsu ya na musu ciwo amma ba su san dalili ba, Mama ce tai k'ok'arin rarrashinsu duk da itama ba ta jin dad'in jikinta, amman saboda mutanen da ke shigowa ana kallonsu shiyasa ta rarrashesu, su d'aki falle d'aya bare tace su shiga ciki suyi kukan nasu babu wanda ya gansu, ta san dai kukan rabuwa suke, wannan kuka kuwa dole su yishi, sun taso tamkar 'yan biyun da suka zauna a mahaifa d'aya, suna matuk'ar son junansu ko kyauta za'a yi musu sun fi son ayi musu a tare, idan kwa aka bawa d'aya to tare zasui amfani da shi, musamman Shukhura da ki mata kyauta gara kiyiwa Nusrat za ta fi matuk'ar farin ciki, hakan da Mustapha ya gani ne yasa komai zai yiwa Shukhura sai ya yi musu tare da Nusrat , wataran ma Nusrat d'in kad'ai yakewa kyauta don kawai yaga farin cikin sahibarsa.