← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 69

Sashe 31

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga wannan rana ya zamto kullum sai an k'arawa Mama jini leda uku, saboda zazzafan zazzab'in da take fama da shi, shi yake k'one mata jinin.
Duk kud'in hannun Nusrat sun k'are, duk wani abu da za'a amfana da shi a d'akinsu ta siyar saboda siyan jini, hatta wayarta ma ta siyar ta Mama ce kad'ai a hannunta, gashi har ta kai yau babu kud'in da za'a siyi wani jinin, ga Shukhura tun zuwan da sukayi d'in nan ba ta dawo ba, ta kirata yafi sau a k'irga ita da Mustaphan babu wanda ya d'aga bare ya biyo.
‘’ Yusra ungu d'ari biyun nan, ki hau mota maza kije gidan Shukhura ki gaya mata halin da muke ciki tun kafin azo buk'atar jinin nan.‘’
‘’Tohm‘’ tace tana karb'an kud'in ta tashi ta fita.
‘’Yayarsu.‘’
Taji Mama na kiranta da muryarta da ba ta fita sosai yanzu, matsawa tayi sosai kusa da ita, ta kamo hannunta had'e da fad'in.‘'Sannu Mama’'
‘’Kiyi hak'uri Yayarsu, ki kula da rayuwar Yusra, Allah ya azurtaku da miji na gari yayi muku albarka baki d'ayanku.‘’
‘’Amin, ki daina irin magan ganun nan, insha Allah zaki ji sauk'i mu koma gida ‘’
Murmushi kawai tayi mata, murmushin da ita kad'ai tasan ma'anarsa.

Allah Allah take Yusra ta dawo tun kafin a buk'aci jinin nan, tun da ta riga tayi amannar ko Shukhuran ba ta biyota ba za ta bayar da wani abu a kawo musu, amman ga mamakinta sai taga Yusran zik'au sai magana mara dad'i da tazo mata da ita, cewar Shukhuran tana bud'e k'ofarta taga Yusran ta mayar ta rufe, babu bugun da ba tayi ba tana kuka tana magiyar ta bud'e had'e da gaya mata halin da suke ciki amman tak'i ta bud'e, Innalillahi take ambata a zuciyarta tana jin wani mugun rad'ad'i tun daga can k'asan ruhinta, tashi tayi ta fita daga asibiti ba tare da ta san ina ta nufa ba, kawai dai taga ta tari me napep tayi mishi kwatancen gidan Shukhuran, tana zuwa me gadi yake sanar mata yanzu aka fita da Shukhuran asibiti, sakamakon farfasa kayan gidan da tayi.
Jiri taji yana neman kayar da ita, da sauri ta jingini da bango tana dad'a ambaton innalillahi.
Me yake shirin faruwa da su ne, wata k'addara ce ta kutso cikinsu ba tare da sun shirya mata ba ?Babu babu babu me bata wayannan amsoshin.
Ko ina ta samu jefe k'afafuwanta take ba ta da ko biyar da ta rage mata wacce za ta hau mota ta mayar da ita asibitin, ga wani bak'k'k'irin d'in hadari da ya,had'o ta gabas ana ta iska da walk'iya, iskar sai kokarin cire mata hijabi take, ba ta damu da hakan ba ita dai duk inda ta samu jefa k'afafuwanta take, har ruwa ya saukko taci gaba da tafiyarta cikin ruwan wani me adai daita ne ta bashi tausayi ya tsaya a gabanta yace ta hau, godiya tayi masa ta shiga har lokacin k'irjinta wani irin zafi yake mata da tiriri ga gabanta da,yake ta mugun fad'uwa ko kad'an innalillahi ba ta bar lab'b'anta ba, tana shiga d'akin da suke Yusra ta taho da gudu ta rungumeta tana kuka.
‘’Yayarmu, Mama mama mama ta rasu‘’
Kawai ji tayi tana fad'ar Innalillahi wainna ilaihir raji'un da k'arfi wanda sai da d'akin gaba d'aya ya amsa, kafin ta sauke idonta kan gadon da Maman take an lullub'eta gaba d'aya har fuskarta....

200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.

#NWA
#KTG
[4/26, 8:42 PM] Rabi: BEBE'ARTH

Wattpad@Rashuna

KATANGA...

...............15

Wani rugugi da hargagi take ji a cikin kwanyarta kafin ta runtse idanuwanta tana karanto dukkanin addu'ar dake bakinta, a hankali taji 'yar nutsuwa na shigarta ta mik'e daga zaman borin da tayi tana rarrashin Nusrat tayi shiru, kafin ta tashi ta fara cuku cukun karb'ar gawar, bayan ta kira Baba ta sanar masa ga sunan zuwa taje ta taro mai taxi, da mai taxi din da wasu samari ne suka taimaka aka sanya gawar cikin motar.

Mutane dank'am suka tarar a k'ofar gidansu, mutuwar ta riga ta gama fasuwa.
Babane da kansa ya yiwa Mama wanka ya had'ata, ya kirawo su Nusrat suyi mata addu'a, Yusra kuka kawai take yayin da Nusrat ta rintse idanuwanta tana mata addu'a da zazzak'ar muryarta da ta cika gidan gaba d'aya kafin tace da Yusra.
‘’Mama ba ta cancanci zubar hawayenki a yanzu ba, ki rakata da addu'a shi tafi buk'ata.‘’
Share hawayenta tayi ta fara yiwa Mama addu'ar a ranta tana ganin k'arfin halin Yayar tasu ko tace k'arfin imani da tawakkali.

Sai da akayi sallar magariba saboda ta riga ta kawo kai kana a kazo fitar da Mama gidan rud'ewa yayi gaba d'aya ana binta da addu'a masu had'awa da kuka suna yi, Yusra kuwa guri ta samu tana kuka da birgima tana fad'in
‘’Kada ki tafi ki barmu Mama, ki dawo garemu dan Allah.‘’
Sai a wannan lokaci Nusrat taji idonta ya fara ruwa, abinda take buk'ata kenan ko za taji sanyin abinda ya dunk'ule mata a zuciya da tsakiyar kwanyarta, janyo Yusran tayi ta rungume tana bubbuga bayanta.
‘’Yayarmu yanzu Mama ta tafi ta barmu?‘’
‘’To ya zamuyi, dole muyi hak'uri mu karb'i k'addarar da tazo mana a haka, Allahn da yafimu k'aunarta shi ya karb'eta mutuwa tayi mana Katanga da ita, sai dai mu bi bayanta da addu'a shikad'ai ne abinda zamui mata gata da shi, sai dai kuka ya zama dole, dole ne muyi kuka, kukan rashi rashi mafi girma a garemu, amman na kasa ko da d'igar da hawaye, gara na zubar da hawayen Yusra akan azabar da nake sha cikin kwanya da zuciyata.‘’

Har aka share zaman makokin Mama Nusrat na fama da zazzafan zazzab'i da ciwon b'arin kai d'aya, gaba d'aya ta fige ta fita hayyacinta donma Baba yana mata rubutu na kariya da dangana to shine samun d'an lafiyarta, amman da duk ta tayarwa da Yusra hankali don itace me jinyar tata sai Baba idan ya dawo ya lek'osu ko ya kawo mata rubutu ta sha. A hankali suka fara sabo da rashin Mama da rayuwarsu su biyu a cikin d'aki sai Baba idan ya dawo daga kasuwa ya lek'osu, idan ya samu ciniki a kasuwar yakan taho musu da gurasa da nama don idan ba'ai girki a gidan ba wuni suke ba su ci ba babu ruwan wani da su, Nusrat gani tayi rayuwa ba za ta b'ille da su a haka ba in ba so suke su kashe kansu da yunwa ba, don yanzu k'irjinta ciwo yake mata alamun ulcer inta na gab da tashi, gurin Maman Ameema taje ta rok'eta akan tayiwa Baffa Shamsu magana akan ya bata 5000 za ta ja jari (Don yanzu ko Iya ce take da buk'ata sai ta biyo ta hannunta)
To sai Allah ya d'orata a kanta a washe gari tayi kiranta ta bata dubu biyar d'in godiya ta dungai mata har da 'yar k'wallar ta kafin ta nufi kasuwa.
Sana'ar wainar Shinkafa ta fara yi da miyar taushe da nama, da me k'uli-k'uli in mutum na buk'ata, ciniki take yi sosai don cika gidan ake da masu siyan waina, idan ba ranar makaranta ba ce Yusra ce ke tayata idan kwa ranar makaranta ce ita kad'ai take yi, a haka rayuwa taci gaba da gangarawa yau fari gobe tsumma, suna samu su rufawa juna asiri da wannan sana'ar wainar da take yi.

SHUKHURA

Bayan barin Yusra gidan kuka ta dinga yi tana jifa da komai na gidan kamar wacce ta zare ta fita hayyacinta a cikin wannan halin Faruoq ya dawo ya tarar da ita, kamar jira take ya dawo numfashinta ya d'auke gaba d'aya shine ya fita da ita a gigice.
Dogon suma tayi wanda ya ibeta tsawon kwana uku ba tare da ta san inda kanta yake ba kafin ta farka, babu wanda yayi gigin gaya mata mutuwar Mama saboda Baba da kansa yayi musu waya ya gaya musu kuma dukkaninsu sunje gaisuwa, sai da ta kwana biyu ta k'ara wartsakewa sosai sannan Mustapha ya d'aukota ya kawota gida a cewarsa bazai iya gaya mata mutuwar Mama ba domin baza ta tab'a iya goge wannan memoryn ba, Baba ne da kanshi ya gaya mata babu abinda tace sai kuka kawai da ta wuni tana yi a d'akin Umma don ko k'ofar d'akinsu ba ta taka ba, suma babu wanda ya nuna ya san tazo Yusra ma mugun haushinta take ji, tana ganin kamar ita ta janyo sanadiyar da suka rasa Mama.

Umma buri ya cika, kud'i sosai Shukhura ke sakar mata, duk wani abu da ta yayibo ita take kawowa, Mustapha kuwa ya bawa Saminu jari me kauri yanzu su Nimha ma fantamawarsu suke, Nimha taso yin magana ganin yadda Shukhura ta juyawa su Yayarsu baya amman ta kasa saboda itama sai da ta d'aure mata baki, amman duk da haka ita tana taimakonsu a b'oye, sabulun wanka, na wanki omo 'yan kud'i haka tana bawa Yayar tasu, duk da suma yanzu Alhamdlillah suna samu sosai cikin sana'ar wainar da suke yi, suyi girkinsu, su d'inka suturarsu, su biya kud'in makarantar Yusran su kuma kashe gararin gabansu, Yusra ba ta tab'a bari a ci musu mutumci duk wanda ya tab'a Nusrat sai dai idan ba ta gidan, a haka rayuwa ta dunga tafiya tana gangarawa gashi har yanzu shekara guda da k'asa ta rufewa Mama idanu, a wannan shekara babu ranar banza da za tazo ta fad'i ba tare da sun nemawa Mama rahamar Ubangiji ba, tsakaninsu da Shukhura kuwa har yanzu sai kallo, ko jiya da tazo yiwa Umma da Baba sallama zasu koma kano tana ta laulayin ciki ba tace musu ba suma ba suce mata ba.....

200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK
Chapter 31 · 0% Book details