Sashe 35
Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read
A dai-dai lokacin su Yusra suka k'araso, saurin janyota tayi had'e da kallon mutumin tace.
"Yi hak'uri don Allah, mahaifinmu ne ya rasu a rud'e take gaba d'aya."
Lumshe idanuwansa yayi kawai had'e da amsa sandansa a hannun d'aya daga cikin yaransa da ya tsuguna ya auko masa daga haka yayi gaba abinsa.
"Nifa wallahi bazan koma cikin asibitin nan nima su kashe ni a banza ba, bani da k'arfin yin shariah da su amma insha Allah hakkin ran mahaifinmu sai ya tab'a kaf wani me motsi a cikin ahalin GOGEL."
Wata muguwar tsawa yaransa da basui nisa ba suka daka mata zasu juyo shima ya daka musu tashi tsawar, k'wafa kawai sukayi suna harararta kana sukai gaba, Mmn Amima tace.
"Bata hijabin ta saka mubar asibitin nan tun kan ta b'allo mana ruwan da baza mu iya toshewa ba, tun da mun samu ta farfad'o su rike takaddar sallamarsu."
"To haka kawai a daki mutum a hanasa kuka, ai bazai yuhu ba wallahi, daga yau ko akuya naga wani zai kaho asibitin nan sai na hanashi don wallahi asibitin k'arasani ne ba wani gogel hospital."
"Munji to, anshi hijabin ki saka mu tafi, ni bansan yaushe kika zama rigimammiya ba wallahi."
Hijabin ta ansa ta saka ba tare da ta kuma cewa komai ba tayi gaba.
Da Hidaya ta fara yin tozali kafin Nimha ta hangota ta taho da gudu suka rungume juna suka zube a gurin had'e da fashewa da wani irin kuka,Yusra ma bin sahunsu tayi suka had'a kawuna suna sharb'ar kuka, Aunty Maryam ce duk tazo ta d'ad'd'agasu tana basu baki kallon Aunty Maryam Nusrat tayi da jajayen idanuwanta da suka kumbura tace.
"An kaishi ne?"
"Wani irin an kaishi, abinda har ya kwana a gidansa na gaskiya, don Allah ki daina wannan kukan kinga ko kad'an baki samu damar yi masa addua ba kuma addua yafi buk'ata ba kuka ba kinji ko?"
D'aga mata kai tayi a ranta tana mamakin kwana tayi kenan ba tare da tasan inda kanta yake ba kafin idanuwansu su gauraya da na Shukhura tana kusa da Umma duk da carbuna a hannunsu, kautar da idanuwanta tayi ta nufi cikin d'akinsu.
Ana share makokin Baba Aunty Maryam tace da Nusrat ta had'a kayanta da ita zata tafi, tayi hakanne saboda Nusrat in ta dinga taimaka mata da girki ga azumin watan Ramadan nan ma ya taho, saboda Aunty Maryam irin mutanen nan ne da suka k'i jinin girki gaba d'aya gashi Abban Hidaya ya tsani cin abincin waje ko na masu aiki, saboda sanin halinta da yayi yasan wataran za ta iya bawa 'yan aikin suyi masa ya kwa yi mata Allah ya isa duk ranar da ta sake ta bashi abincin 'yan aiki yaci, to wannan dalilin ne yasa bata rabo da wamars masu mugun rik'on zafi idan tayi girki tun rana to dashi zasui dinner, kuma duk abincin da take sassauk'a ne, Hidaya me d'an kama mata wani abin makaranta yanzu take zuwa wani zubin sai shida take shigowa, Hibba kuwa in ta bata girki sai yace jagwalgwalo, to wannan dalilin ne yasa tace zata tafi da Nusrat in, don tun rasuwar Mama ma taso tafiya da ita, Hidaya tace tayi mata tayin hakan ta nuna bata so, yanzun ma kuwa
Nusrat in rufe ido tayi tace baza ta bi Aunty Maryam ba, idan ta bita ta bar Yusra a hannun wa, Iya kuwa tace dole sai taje, ai su ba mutane bane da za tace a hannun wa za ta bar Yusran, yayin da itama Nusrat ta kafe kan ba inda zata matsa ta bar Yusra, sai dai in tare da Yusran zasu tafi, don wallahi in ta tafi ta barta ta kwana da sanin babu me lura da lamarinta, yunwa tayi sanadiyar rugujewar rayuwarta tunda yanzu sun riga sun zama marayu gaba da baya, to ana cikin hakane Iliya dake a cikin gida,(Ainihin gidan da aka haifi Mama, idan masu karatu basu manta ba)yazo akan a bashi rik'on Yusra yana so, kasancewar matarsa yanzu ma za tayi haihuwar fari tsohon ciki gareta, kuma yana da k'okari gurin zumunci, to ganin babu ran uwa ba uba yasa yace bara yazo ko zaa bashi rik'on Yusra ya samu ladan marainiya, kuma da yaddar matarsa yazo kasancewar kar a samu matsala tunda shi ba zaman gida zaiyi ba tare zai barsu, babu wani ja Iya tace Yusra ta had'o kayanta ta bishi, sanin Iliya yana da mugun kirki da zumunci yasa hankalin Nusrat kwanciya ta taya Yusran had'a duk wani kaya nata dake d'akin, bayan sun rungume juna sunci kukansu sun k'oshi kamar wayanda zasu rabu har abada, kana Nusrat in tayi mata nasiha sosai akan ta kula da rayuwarta ta dinga tunawa su marayu ne basu da uwa basu da uba, har bakin motar Iliya ta rakata, anan d'inma kamar ba zasu rabu ba, dukkaninsu hawaye suke zubarwa suna mugun jin rabuwar tasu a cikin zuciyoyinsu, Iliya ne ya dinga basu hak'uri yana tausarsu yayiwa Nusrat in alk'awarin kula da rayuwar Yusran, ita kuma ta buk'aci ya rubuta mata numbersa a memo, ya rubuta mata kana yaja motar suka tafi, kasancewar shi ba a nan cikin gidan yake a zaune da matarsa ba.
A sanyaye ta koma cikin gidan tana jin duniyar gaba d'aya tayi mata fad'i kamar ita kad'ai ta rage a cikinta, duk katangun da suka zagayera sun rushe gaba d'aya, a haka dai ta samu ta gama had'a kayanta tsaf saboda Aunty Maryam ta sanar da ita driver yana hanya, ita Hidaya tun ranar uku ta tafi kasanwar zasu fara zana paper.
Ko wata kusuruwa ta d'akin nasu take bi da kallo tana tuno rayuwar da suka dinga gudanarwa a cikinsa tun daga yarinta har zuwa sanda suka mallaki hankalinsu, da yadda suka tashi da ginanniyar soyayyar junansu a zuk'atansu wacce mahaifiyarsu me kyakkyawar zuciya ta gina musu, sai gashi yau an wayi gari tsakaninsu da Shukhura sai kallo, mahaifiyarsu ta tafi ta barsu gashi a yau zasuyi nida da Yusra, taya za ta iya runtsawa a yau babu Yusra babu Shukhura a gefenta?
Ta jefowa zuciyarta wannan tambayar yayin da idanuwanta ya sauka akan makwancin nasu, wani irin kuka ta fashe da shi wanda yake tahowa tun daga k'asan zuciyarta, kafin can ta tuna da takaddar da Baba yace Yusra ta bata, duk da ta karanta amman ba tayi abinda ya umarceta ba, ga abinda takaddar ta k'unsa."
" Daga gefen hagu na d'akina ki d'aga tabarma zakiga shatar wani guri an hak'a ki hak'a kiciro abinda yake ciki ki ajiye mini, kada ki kuskura wani yasan da zamansa a gurinki ki ajiye mini, ina nan zan dawo."
Ashe ba za ka daho ba Baba ta fad'i hakan da dashshshiyar muryarta kafin wani azababben kuka,ya taho mata tana rik'e cikinta da k'irjinta da suke mata mugun zafi, sai da kukan ya tsagaita mata kana ta tafi dakin Baban ta d'auko ba tayi gigin budawa taga ko meye ba ta k'ulle a bak'ar leda tana adana shi cikin kayanta, a lokacin Aunty Maryam tace ta fara fito da kayanta ga direba yazo, k'arfe uku dai dai motarsu ta d'auki hanya zuwa kano, kano ta dabo tumbin giwa ko da me kazo an fika.
(To dai Iya da Umma ga gida nan an bar muku ku kadai kuci abinda kuke so kuyi abinda kuka ga dama,
Nusrat kuma ko wacce iriyar rayuwa zaai a kano, Iya dama tace mijin kano kike hange shiyasa kika ki tsayar da miji)
200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK
In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta
Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.
#NWA
#KTG
[4/26, 8:43 PM] Rabi: BEBE'ARTH
Wattpad@Rashuna
®️NAGARTA WRI.ASOCIATION
KATANGA...
In baki siya ba ya kamata ki mallaki naki a hannu kar garab'asar ta wuce ki, in na gama free page zaki siyeshi akan 300 ne,kuma in kin siya yanzu zaki samu damar karanta CIN AMANA kyauta, kada ku bari wannan garabasar ta wuceku, kada ku manta akwai abin amfani a ciki.
Masu tambayata document in na gama, shi kuma zaku sameshi akan 500kacal.
...............20