Sashe 50
Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mahaifiyar Aasad ma ta musu tarb'a ta mutumci, kamar ko yaushe yadda kasan ta lashe Aashiq in don so da k'auna, sun samu Mahaifin Aasad in Baffa k'arami yana gida, don haka suka zauna suna tattaunawa duk da yawanci maganar da Asgar ne akan companys kafin Baffa k'aramin ya dubi Aashiq yace.
"Kai kuma sai yaushe ne zaka shirya yin aiki a companys in mahaifinka ? Duk ka bar mana nauyi akanmu, kuma kasan girma kamamu yake aikin kuma zaiwa Aasad da Asghar yawa nan gaba."
"Ban jin akwai lokaci gaskiya, saboda har yau ba na shaawar aikin."
"Duk sanda ka shiryawa hakan kujerarka tana nan tana jiranka, amman dai ya kamata ka yiwa kanka fad'a tun da yanzu ba wani aiki kake ba, kawai kana zaune ne."
"Babu takura a zaman nawa haka shiyasa."
Daga haka suka yi masa sallama suka fito, saboda kiraye kirayen sallah da aka a fara yi, masallaci suka nufa, acan sukayu alwala kana suka shiga cikin masallacin, sai da sukayi sallar isha'i kana suka fito, gidan Asghar in suka nufa wanda yake can cikin estate in,kasancewar Ramla ta riga da tasan da zuwansa tare da Aashiq in tayi masa girkin da ta san yafi k'auna ta jere musu akan dining tana jiran isowarsu cike da zumud'i don ta kwana biyu ba taga Yaa Aashiq in ba don kulle Asghar in yake mata gata a cikin estate in amman sai ta shafe fin wata ba taje gida ba, har su Rabeeah da suke waje sun fita zuwa, da ta kaiwa Aashiq in k'ara sai cewa yayi.
"Ai yayi miki da sauk'i, in nine sai bayan wata shida zaki dinga zuwa gida."
Tana jin haka taja bakinta ta tsuke don Allah na gani baza ta iya wata shida ba tare da taje gida ba, a hakanma tana jinta a takure don Allah na gani tana kewar su Baba Azumi sosai tare da shi kanshi Aashiq don ba kasafai yake zuwa ba, yau ma Asghar inne ya mata alkawarin janyo mata shi.
Suna cikin cin abincin Aashiq yace da Asghar.
"Ina tunanin Baba Azumi zan kaiwa Hajjaju ta zauna tare da ita,saboda likita yace a daina barinta ita kad'ai, in yaso nima sai na dawo gidan da zama."
"Amman ni a nawa tunanin kai mata Baba Azumi kamar baza ta so hakan ba, kasan Hajjaju ba kowa take so yana rab'arta ba, gashi kuma d'aki d'aya zasu na kwana, gara ka kai mata wannan yarinyar ina ganin kamar za ta fison hakan, may be tasu tazo d'aya."
Jinjina kai yayi kafin ya bud'i baki yace.
"Zan duba hakan mu gani."
Kiran wayar Aasad ne ya shigo wayarsa sai da ta kusa katsewa ya aga, kamar ba jiran kirannasa yake ba don yau babu ko kwalba d'aya a cikin pridge hakana ma cocaine in ba ya jin yana da ragowarta, in kwa babu su yasan babu shi babu bacci a yau d'innan."
"Gani na shigo cikin gidan."
"Ok, ka bani mintuna goma."
Daga haka ya mik'e yana sauke idonsa akan Asghar da yanayinsa ya sauya sosai, baice mishi komai ba ya mayar da idonsa kan Lamra kafin ya furta.
"Allah tashemu lafiya."
Sai da ya shafa kan twince dake kwance kan gadajansu suna bacci kana ya fice, Asghar na bin bayansa da wani irin kallo yana jin tuk'uk'i da bak'in ciki, tun da yaga kiran daga Aasad ne yasan bazai huce hodar iblis ko giya ya kawo masa ba, yayi mugun tsanar wannan d'abi'ah da ya bud'i ido rana tsaka yaga Aashiq in a ciki dumu dumu, wanda a daa yafi kowa mugun tsanarta, kullum cikin yak'i yake da masu aikatata amman sai da Aasad yasan yadda yayi ya dilmiyar da shi a ciki wanda shi kuma har yau har gobe yake fafutukar ganin ya cirewa Aashiq in sha'awar shan wani abu da ya danganci maye, kuma akan hakanne suke samun sab'ani da shi har Aasad in yayi amfani da wannan damar gurin shiga tsakaninsu.
Sai da ya fara biyawa ya duba jikin Hajjaju, har lokacin bacci take, kuma wacce ya sanya ta zauna tare da ita har ta tafi don ba anan suke kwana ba zuwa suke su tafi, don haka ya taho da niyar turo yarinyar nan ta zauna da ita, don sai yaji ya amshi shawarar Asghar in.
Ta k'ofar da ta zamto tasa shi kad'ai suka bi, ta nan aka shishshigar masa da d'ima d'iman kwalika ke kyace abin arzik'i ne a ciki, nan kwa giya ce a ciki (Barasar faransa)duk pridge in da ke sashensa aka ciccika su da barasar, kana ya ajiye mishi cocaine in had'e da fad'in.
"Kasha ka ji Ashh wannan ba irin sauran bace ta fita da ban, in ka sha biya na musamman zakamun."
Ba tare da yace komai ba ya zazzagi hodar a hannunsa ya zuk'a had'e da lumshe idanuwansa.
Biya na musamman in kuwa yayi masa kafin suyi sallama ya fice ya kulle k'ofarsa, wanka yake shirin shiga kana ya tuna da aikawa Hajjaju yarinyar nan don haka ya d'auki waya ya kira Baba Azumi ys shaida mata Nusrat in ta had'a kayanta Khalil zai kaita gurin Hajjaju.
Duk da a cikin estate inne amman sam Baba Azumi da Baba Hadiza ba suji dad'in rabuwa da Nusrat ba, musamman su da sunsan ba zuwa gidan zasuyi ba sai dai in ita tazo, don k'arara Hajjajun ta fito ta nuna ba ta son suzo gurin da take, kuma ba suji zafinta ba kasancewar Aashiq jikanta, shikuma Aashiq KATANGARSU ne bango majinginarsu baya goya marayu, sunaiwa Nusrat in fatan dacewa da samun jin dad'in zama tare da Hajjajun, ita kanta Nusrat in ba taji dad'in sauya mata gurin zama ba, ta riga ta saki jiki da su Baba Azumi tana mugun jin dad'in zama da su, sai dai babu yadda za ta yi dole ne ta bi umarnin wanda take zaune a k'ark'ashinsa don da ba dan shi ba da k'ila tana can tana garari a duniya.
Allah ya taimaka Faleesha da Aleesha bacci suke da mak'alewa zasui sai sun bita, sai dai kwa za'a sha rigima idan suka daina ganinta, Aliyu kuwa dama ya gudu gidansu, su kuwa tunda suka ga Nusrat in suka lik'e mata sukak'i tafiya...
Manzon Allah (SAW)yace.
"Sai naga wasu mata an rataye su da gashin kansu jikin bishiyar zakumi, kuma ana kwara musu ruwan zafi naman jikinsu yana kwalewa ana dawo musu da halittarsu sabuwa, sai yace su waye wannan ya d'an uwana Jibrilu?"
Sai yace.
"Sune matan da suke shan k'wayoyin magani don su kashe 'ya'yan dake cikin cikinsu don tsoron ciyarwa ko shayarwa ko tarbiya, shin basu san Allah ne yake ciyar da su ya shayar da su? Hakika Ubangiji ya fad'a cewa,(Babu wata halitta a bayan k'asa face Allah ne yake ciyar da ita.)
[6/8, 6:01 PM] Rabi: 38
Man zafi take shafawa Hajjaju akan guiwoyinta bayan ta gama yi mata tofi a kansu, k'arar door bell su kaji, a hankula ta mik'e don zuwa ganin wanda yake neman iso.
Bud'ewar k'ofar tare yazo mata da fad'uwar gaba, kafin idanuwanta su shiga cikin nasa, yana tsaye, fuskar nan tasa a kame kamar ko da yaushe sai k'yalli yake yana zuba k'amshi, gefe ta jaa don bashi hanyar hucewa kafin tai k'asa da kanta had'e da fad'in.
"Barka da dare"
Ko kallon gefen da take bai yi ba yasa kai zuwa ciki dama kuma ba ta saka ran zai amsa mata ba, tana shirin rufe k'ofar sai ga Asghar ya taho, dama tare suke ya d'an tsaya ya amsa waya ne."Barka da dare" Tace masa da murmushi akan fuskarsa ya amsa mata da. "Barkanki dai, da fatan kin huni lafiya?"
"Lafiya lau."Ta amsa mishi.
A falo ta nemi guri ta zauna tana sauke idanuwanta akan TV duk da kallo ita ba damunta yayi ba wannan sai Shukhura, Hibba ce ta fad'o mata a rai, ta tabbata uanzu in ba'ai sa'a ba tana can gaban Tvn kowa ya shige d'aki ya barta.
Asghar ma anan falon ya nemi guri ya zauna yana kallon Nusrat had'e da Nazarinta a hankula.
Tun da baiga Hajjaju a falon ba yasan tana bedroom inta don haka ya nufeshi kai tsaye, sai da ya d'an tsaya yayi nocking kafin yaji muryarta tana fad'in.
"Shigo Turaki."
Baiyi mamakin sanin da tayi shi d'in bane saboda duk wanda yazauna tare da shi to tabbas zai haddace k'amshinsa bare ita tasan yadda nocking insa yake, banda shi kuma babu me tunkaro inda bedroom inta yake to sai yanzu da Nusrat ta shigo cikin rayuwarta."
"Na sameki lafiya"
"Lafiya lau, ya naka jikin?"
"Alhmdlillah, ya guiwoyin naki?"
"Yanzu ban jin ciwon komai, wannan yarinya da ka kawomun ina matuk'ar jin dad'in zama da ita, ita take mini tofi kuma ta shafe mini da man zafi."
Bai ce komai ba,kuma tasan bazai ce d'in ba don haka taci gaba.
"Baffanka k'arami ya kawomun k'ararka, sai yaushe ne Turaki za ka cika burin mahaifinka? ba ka samu kayi hakan yana raye ba, amman yanzun ya kamata ka k'ok'arta, ina son ganin rayuwarka ta dai daita kamar kowa, ka manta duk abinda ya faru a baya kasa gaba kawai a ranka, baya ta riga ta wuce baza ta tab'a dawowa ba don haka ka daina bata damar tab'a maka rayuwarka ta yanzu, ka manta komai kayi rayuwarka a sake ka daina k'untata zuciyarka, ina son ganin auranka, ina so na ganka tare da matarka kuna rayuwar farin ciki, ina so naga 'ya'yanka Turaki, ina so ina so da yawan Abubuwa su dai daita cikin rayuwarka tun kafin tawa rayuwar tazo k'arshe don bamu da tabbacinta."
"Bazan iya ba Hajjaju zuciyata tana mun ciwo har yanzun na kasa mantawa, ina jin bazan tab'a mantawar ba, amman ki bar batun aure cikin rayuwata, k'addara ta riga ta saka almakashinta mai kaifi ta yanke aure daga cikin rayuwata."
"Ba ta yanke ba Turaki, sai dai in kaine zaka yanke, ka gwada ka kuma bata dama."