← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 69

Sashe 46

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To Allah yasa lafiya, jeki ko ta idar, sai ki taho da safayar makullin dakin a bud'e a gani"
Ya fad'a da gajiya cikin muryarsa da ta had'e da fargaba da tashin hankali, ko da Hibba ta koma dakin sai ta tarar Mommyn ba ta idar ba don haka ta d'ebo safayar mak'ullan gaba aya da ke cikin drower gado don ba ta san wanne ne daga ciki ba, tunda ba fiya amfani akai da dakin ba sai yanzu da Nusrat in ta zauna bayan sun raba daki da Hidaya.

Da Allah ya taimakesu suna gwada maullli na uku sai d'akin ya bud'e, wayam d'akin ba kowa a cikinsa, duk da kirjinsa da ke bugawa amman sai ya bawa kansa k'warin guiwar cewa Hibba.

"Kiyi knocking a toilet ko tana ciki."
Itama dama tunanin da take kenan don haka ta karasa bakin kofar toilet in tana nocking, tayi kusan sau uku amman shiru don haka kawai ta bud'e, nan dinma dai babu kowa a ciki, ban dakin ma a bushe yake da alamu an jima baa shiga cikinsa ba.
"Yaa ba ta ciki." lumshe gajiyayyun idanuwansa kawai yayi, yayin da ita kuma idonta ya sauka kan wata farar takadda da ke kan drower gado da sassarfa ta isa gurin takaddar had'e da wareta gaba aya.

"Yaa RJ
shine a farkon layin rubutun don haka tayi saurin janye idonta hade da mika masa, har lokacin idanuwansa a lumshe suke don haka sai da ta hada da cewar.
"Yaa ga takadda ta bar maka."
"Fad'i meye a ciki"
Ya fada ba tare da ya bude idanuwansa ba.

"Yaa Rj kayi hak'uri bazan iya auranka ba saboda bani da kima da darajar da ko wace mace ke bawa mijinta, Ishaq ne ya cuceni yaci amanata ya b'atan rayuwa, ciwon da na kwanta nace muku ulcer ce to ba ulcer bace laulayin ciki nake, tun da na tabbatar da ciki nake dauke da shi naji bazan iya hada ido da kai ba da Aunty Maryam da Daddy don haka kawai na yanke shawarar barin gidan tun kafin ku gano tab'ar gazar da na aikata, don Allah ku gafarce ni."
NUSRAT

Bazai ce ga yadda akai ya kawo kansa d'aki ba kawai dai ya tsinci kansa ne a ciki, kayan jikinsa kawai ya tub'e ya fada toilet hade da sakarwa kansa ruwan d'umi ya dade ruwan yana sauka a kansa kafin yayi wanka da d'auro alwala, yana gabatar da sallar ya fad'a gado a rigin gine, duk yadda yakai ga buk'atar sanyawa cikinsa wani abu, ji yayi bakinsa bazai iya karb'a ba bare har ya kaiwa cikin a yadda yake jin ransa gaba aya a jagule, zuciya da k'wak'walwarsa gaba aya a cunkushe suke ya rasa wani irin tunani ma zaiyi abu d'aya ne dai kawai ya san Nusrat ba za ta tab'a aikata abinda ta rubuta ba, ko ma dai meye yana son ji daga bakinta don haka tun asuba zai d'auki hanyar zariya yanzunma don dare yayi ne.

Gurin Momy Hibba ta nufa da takaddar a hannunta, takaddar kawai ta bata ba tare da tace komai ba.
Momy na gama karantawa ta hau tafa hannu da sallallami kafin tace.
"Dama sai da jikina ya bani babu yadda baayi da ita ba aje asibiti tak'i yadda ta kafe akan ulcer inta ce ta tashi a siyo mata magani kawai, aini yadda naga tana ta tashin zuciyar nan da amai ta kuma cinye goron d'ari nasan akwai bayani, ashe cutarmu 'yarnan tayi cikin shege ta yo mana a cikin zuriarmu, Innalillahi wa inna ilaihirrajiun."
Sai ta fashe da kuka yayin da Hidaya ta fito tana tambayar abinda ya faru Mommyn tana gaya mata, Hibba dai zare jikinta tayi ta bar d'akin sam ba ta yadda da wannan zancen ba, ta tabbata ba haka zancen yake ba, ita damuwarta ma ina Nusrat in ta tafi fatanta dai Allah yasa tana zariya sai aji komai daga bakinta."

Daa da yadda zaiyi ya cire son Nusrat daga zuciyarsa da yayi, saboda zargin da yake tayi hakanne kawai don gujewa auransa saboda ya auri Hidaya, idan sonshi ta daina yi ai ba sai ta shafawa kanta bak'in fentin da ba ya kankaruwa a jikin mutum.
Memakon yaji son nata na raguwa sai dai ma dad'uwa da yaji yana yi burin idaniyanshi kawai ya saukesu a kanta.
Yana idar da sallar asuba kamar yadda ya k'udurce a ransa ya d'auki hanyar zariya, sai dai zancen da ya samu daga bakin Baffa Shamsu duk ya gama dagula masa lissafi, har yanzu zuciyarsa ba ta gasgata abinda ake zargin Nusrat in da shi ba, shi babban tashin hankalinsa ma da aka koreta, ina ta nufa ina taje duk bai sani ba kuma bai san wanda zai sanar da shi ba, Yusra ce ta fad'o masa a rai don haka ya lalibo numberta ya danna mata kira.

"Yaa Rj kai nake lalibowa zan kira ka had'ani da Yayarmu tun jiya nake kiranta ban sameta ba."
Maganar Yusra ta sauka cikin kunnuwansa rintse idanuwansa yayi yana jin yadda kansa yayi wani mugun sarawa, ji yayi bazai iya yi mata magana cikin halin da yake ciki ba don haka kawai ya kashe wayar gaba d'aya.

。。。。。。。

Ko ina ta samu jefa k'afafuwanta take saboda yadda k'arfinta gaba d'aya ya k'are gashi dama ba ishashshiyar lafiya gareta ba, ga kuma b'acin rai da cunkushewar zuciya, da kuma tunanin rasa makoma, akwatin nata ji tayi kamar ta wullar saboda yadda yayi mata nauyi ta gaji da jansa, sai dai akwai abubuwanta masu matuk'ar muhinmanci a ciki, tun tana iya taka k'afar tata har ta kai ta kasa d'agata ma, ga hadari da ya had'o yayi murtuk gari yayi bak'ik'k'irin dama magariba ta kawo kai da alamu sallar yake jira ruwa ya sakko gaba aya, gabas yamma kudu arewa duk ta duba ba ta hango wata mafaka da za ta fake ba kafin saukowar ruwan, don haka ba ta da wani zab'i da ya huce zama a gefen titin don k'arfinta ya k'are har ankai matakin da k'afafuwanta ba zasu iya d'aukar gangar jikinta ba.

Ana idar da sallar magariba kuwa ruwa ya kece kamar da bakin k'warya, har sai da Isha ta gabato kana ya fara tsagaitawa, wanda gaba d'ayansa ruwan akan Nusrat ya sauka kuma ruwan har da k'ank'ara, ta fice gaba d'aya daga hayyacinta numfashinta sai sama yake da k'asa daga k'arshe ta tsaya cak da aiki....
[4/26, 8:46 PM] Rabi: 33

Motoci ne farare k'al guda uku a jere sai zabga uban gudu suke akan titi kamar zasu tashi sama, har sun gota gurin da Nusrat ke yashe ba ta da maraba da gawa motar da ke tsakiya tayi ribas ta dawo, a dai dai gurin da Nusrat ke yashe dreban yayi parking, yana fitowa a hanzarce rik'e da lema a hannunsa, sai dai ya tarar har ogan nasu ya fito ya nufi gurin da Nusrat ke yashe ga mamakinsa sai gani yayi yasa hannu ya ciccib'ota sai yayi saurin bud'e masa murfin motar ya sakata a ciki, sai jin saukar dakakkiyar muryarsa yayi cikin kunnuwansa yace.

"Ka saka akwatin cikin boot."
daga haka ya nufi gaban motar ya bude barin da ke zaman banza ya shiga saboda babu space in da zai zauna a bayan duk ta cikeshi.

Asibiti direct suka nufa da ita wanda sina zuwa aka karb'eta aka shiga bata taimakon gaggawa, sai da suka ga komai ya dai daita kana suka baro asibitin.

Tun kafin isowar motocin nasu securityn da ke bakin babban get in sun wangale musu, suna jiran k'arasowarsu, a guje a kuma jere suka shige suka d'auki titi d'od'ar kafin su tsaya a wani plat mension da ya gaji da matuk'ar had'uwa, ko da suka yi parking a harabar ajiye motocin babu wanda yayi yunk'urin fitowa ganin ogan nasu har lokacin bai fito ba, don drivern da ya tuk'oshi yana parking ya zaga side in da yake ya bud'e mishi k'ofa yana jiran fitowar tasa wanda sai da ya gama shan k'amshin shi kana ya fito ganin haka yasa yaransa sukayi saurin fitowa had'e da take mishi baya har zuwa asalin k'ofar da za ta sadashi da asalin cikin gidan kana suka jaa birki har sai da ya danna code jikin k'ofar ta bud'e ya shige kana suka juya kowa ya tafi yin uzurin gabansa.

Falo ne k'ayatacce wanda aka cikashi da dukkannin wani kayan k'awa na duniya, Baba Azumi ce kawai a falon, itama abincinsa ta had'o a babban tray za ta kai masa.
"Sannu da zuwa d'an uwana."
"Yauwa Baba sannu da k'ok'ari, sai dai yau ba na buk'atar abinci tea kawai zaki taimaka mini da shi me yaji."

"An gama d'an uwana."
Ta fad'i hakan tana k'ok'arin juyawa yace.
"Amm Baba Hadiza taje parking space Khalil yana jiranta."

"Insha Allah zan isar da sak'onka."

Kai kawai ya jinjina mata had'e da nufar b'arin dama inda zai sadashi da sashensa, falo ne k'awatacce wanda yafi na farkon k'awa sai dai shi wannan babu hayaniya a cikinsa, akwai dining area da 2 bed rooms a ciki, d'aya daga cikin bedroom in ya nufa wanda da shi kawai yake amfani, komai na ciki jajaye ne saboda kalar da yake auna kenan, kayan jikinsa ya tub'e had'e da shigewa toilet ya had'a ruwan wanka ya shige ciki kafin ya lumshe kyawawan idanuwansa wanda suke d'auke da dogayen eye lashers zara zara.

Tea in da Baba Azumi ta kawo masa yake sha a hankula yana lumshe idanuwansa, wayarsa da ke gefensa ce tayi k'ara a hankali ya sauke idonsa kan wayar, Bro Asghar shine abinda ke yaho akan secring in wayar d'auke idonsa yayi daga kai yaci gaba da sipping tea insa sai da yayi mishi miss call uku a jere ba tare da yayi peking ba, sai kuma wata wayar ta shigo da ban shima sai a miss call na biyu kana idonsa ya sauka yaga ba na farkon bane wannan Bro Asad ne, dole ya d'aga wayarshi don ya tabbata yau a yadda yake jinsa idan ba da taimakonsa ba bazai iya rintsawa ba, yana peking in wayar bai tsaya saurarar me zaice ba yace.
"Ka shigo." A takaice kana ya ajiye wayar ya mayar da idanuwansa ya rufe.
Chapter 46 · 0% Book details