← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 69

Sashe 57

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutuwar Aliyu ta gigita mutane da dama, Aashiq kuwa duk k'arancin shekarunsa mutuwar ta tab'asa fiye da zaton masu zato,don a lokacin yasan mutuwa ya kuma san me ake nufi da mutuwa, Ibrahim kuwa sam zuciyarsa ba ta aminta da hatsarin da Aliyun yayi ba,haka kawai yaji kamar da saka hannu a ciki,musamman yadda suka tafi tare da su Hamza ya akai suka barshi ya taho shi kad'ai,amman kawai dai sai yaja bakinsa yayi shiru.A haka rayuwa taci gaba da tafiya sun karb'i rashin Aliyu sun dangana,amman Aashiq sai da aka dinga yi masa rubutu kana aka samu ya dawo dai dai, Hamza da Bashir duniya tayi musu dad'i su suke juya dukiya yadda suke so,yayin da maaikata suka fara ganin ba dai dai ba.Bayan Zuriya ta fita daga takaba Hamza ya fito fili ya nuna yana son auranta ko don ya rik'e amanar da d'an uwansa ya bari, a cewarsa,inda Zuriya ta nuna ba za ta auresa ba sai ya biyo mata ta sama ,inda iyayanta suka tank'warata suka nuna mata muhimmancin auran nata don dole ta aminta za ta auresa yayin da kishi yasa Nuriya ta zuba mata guba a abinci wacce ta k'one mata jini gaba d'aya ta rasu,ko da akaje asibiti likitan yace zuciyarta ce ta buga,da yake sun had'a baki da Nuriya don gudun kar aji guba ce a shiga bincike asirinta ya tonu, a lokacin idan kuga Aashiq sai ya baku tausayi, d'an k'araminsa da shi ya d'an d'ana d'acin rashin mahaifa, d'acin da yake ji a zuciyarsa wanda ya tsinci kansa a irin halin da yake ciki ne kawai zai fuskanta yafi tausaya masa.
Bayan mutuwar mahaifansu shi ya zamo uwa ya zamo uwa gurin Aaleesha da shi kad'ai take yadda, tare zasu je makaranta su dawo, to sai Aasad shima tana d'an yadda da shi da yake duk makarantarsu d'aya.Aasad zuciyarsa irin ta mahaifinsa ce akwai bak'in ciki da hassada, don yana mugun jin haushin yadda kowa yake nuna k'auna da kulawarsa akan Aashiq, hatta mahaifansa da kakanninsa, gashi duk jama'ar estate in kowa yafi k'aunarsa, haka a makaranta ma yafi shi k'ok'ari da jama'a, gashi mayan k'wallo indai suna buga wasan k'wallo sai ya cinyesu, shikwa Asghar bai d'auko zuciyar mahaifinsa ba, da zuciya d'aya yake k'aunar Aashiq,k'auna irin ta jini,gani yake Aashiq in ya can canci a nuna masa soyayya da kulawa fiye da wacce ake nuna masa a yanzun.
Hajjaju,Aashiq da Aalisha take kalla taji sanyi a ranta, taga kamar Aliyunta take gani, don Aashiq bai baro komai a kammannin babansa ba.Bayan ya kammala secondary school insa ne kuma yak'i karatu sam,inda ya mayar da hankalinsa gurin buga wasan k'wallonsa, Hamza ne ya shiga ya fita ya juyar masa da hankali daga karatu, don gudun kar yayi karatu nan gaba yazo yafi k'arfinsu, sai dai abinda bai sani ba Aashiq k'waro ne a compuiter, yasan cumpuiter ciki da bayanta, kuma irin gifted in nanne suka ga abu sau d'aya sun d'aukesa har abada. A haka rayuwa taci gaba da tafiyar masa har ya fara fita k'asashen waje buga wasan k'wallo,duk da ba a son ran su Hamza ba,don sun so hana sa Hajjaju tace a barsa tunda yak'i karatun in ya zauna a gaban nasu me zaiyi, cikin nasara ya fara buga wasan k'wallonsa nan da nan yayi suna ya shahara, jikinsa yayi wani irin murd'ewa alamun k'arfi suka bayyana a garesa,kud'i suka zauna masa, sai ya zamto ba kasafai yake zuwa nigeria ba tunda suna video call da Hajjaju da Aaleesh, don Aaleesha ta fara zama budurwa kuma Aasad yana kular masa da ita yadda ya kamata, don shak'uwa ce sosai tsakaninta da Aasad in,wacce ta zarce musu soyayya ba tare da sun sani ba.

Yana da shekaru 25 amman in ka gansa ba za kace shekarunsa haka ba, ya zama cikakken namiji kyahunsa da gogewar fatarsa sun k'ara bayyana, farine tas, sumar kansa da sajansa da gemu ne kawai bak'i a jikinsa sai k'wayar idanunsa, kyahunsa ne shiga cikin idone ya zauna daram sai kayi da gaske kafin ya fita, turawa da hausawan da ke zuwa duk suna kawo kansu garesa amman bai jin zuciyarsa ta shirya bud'ewa duk da yana jin lokacin yin auransa yayi don mabuk'aci ne shi sosai a yadda ya karanci halittarsa,yana samun wacce hankalinsa ya kwanta da ita kawai zaiyi wuf da ita ya huta.

Maryam,itace k'addarar ta fara biyowa ta kanta,'ya ce gurin Baffa Ibrahim, wan mahaifiyarsa kenan kuma aminin majaifinsa, sun dai daita kansu ne a wani zuwa da yayi, dama ita can tana k'aunarsa, ai tunda su Hamza suka ji Aashiq zaiyi aure hankalinsu ya tashi, ta yaya zasu bari yayi aure su da suke son ganin rayuwarsa ta wulak'anta,idan suka bari yayi aure dukiyar da suke ganin ta zamo,tasu kenan ta tashi a banza. don haka sukayi tsafin da muddun ya auri mace a daren da aka kawota za ta rasu, ta nanne za'a fara hanasa aure daga nan sai su ruguza rayuwarsa, don vazai yuhu su kashesa ba shakku zai shiga zuciyar mutane,musamman masoyan babansa da har yau suke k'aunarsa.

A daren kuwa da aka kawowa Aashiq Maryam ta amsa kiran mahaliccinta, ya shigo yana d'oki, yana zuwa ya tarar da ita a sank'ame,tashin hankalin da ya shiga bazan iya zayyana muku shi ba, a ranar sadakar bakwanta Baffa Ibrahim ya kuma d'aura musu aure da k'anwarta Zaleeha,itama kamar yadda yazo ya tarar da Maryam haka ya tarar da ita,tashin hankalin da ya shiga zato ma ba zai tab'a baku shi ba, yayin da Baffa Ibrahim da matarsa suka karb'i k'addarar da ta samesu ta rasa 'ya'yansu hannu biyu, har sukaji inama suna da wata 'yar da ba ta da aure bayan Zaliha su k'ara masa, inda Aashiq ya hak'ura da auran ya tattara ya koma yaci gaba da harkar k'wallonsa amman sai da ya memi maganin da yake kwantar masa da sha'awarsa in ta motsa.
Huda,itace ta uku,'yace gurin Baffa k'arami (Hamza)Ita ta kafe sai ta auresa babu ta inda bai biyo mata ba akan ta hak'ura da shi amman ta k'i,inda mahaifiyarta ta goya mata baya, ita kuma hak'on dukiyar da Aashiq in yake da ita take, ganin bashi da wata mafita yasa ya gaya mata tsafin da suka yiwa Aashiq in inda karaf a kunnan Baffa Ibrahim, baice da shi komai ba ya fara nemawa Aashiq magani,sai sukayi asirin da suka mayar masa da hankalinsa k'auye,inda ya kwashe iyalinsa suka koma can da zama, ba tare da ya k'ara wani yunk'uri akan Aashiq in ba.

Ko kad'an sun kasa tank'wara Huda akan ta hak'ura da Aashiq tak'i, tace ita ko mutuwa za tayi bayan ta auresa ta shiryawa hakan...

kisamu ganyen gwaiba me dan yawa kidafa ya dafu sosai ranar da kika fara jinin haila zaki dafa seki maidashi kamar ruwan shanki har tsawon kwana hudu duk abunda ke cikin maraki insha Allah ze futa du wani datti dake cikin mahaifa da mara yana maganinshi kuma ciki ze iya shiga bayan kinyi wankan haila da yarda Allah
Kuma wanan nayishi wly kuma naga anfaninshi.

Ki sami alo vera ki matse ruwanta ki had'a da man zaitun kiyi insertin,yana maganin sanyi yana kuma matsi.yi da shi kikai tasha za'a dac[6/15, 8:32 PM] Rabi: 45
Mahaifin Baffa K'arami ne ya tsaya kai da fata sai anyi bikin Aashiq da Hudah,inda hankalin Baffa k'arami ya tashi ya shiga k'ok'arin karya tsafin da ke jikin Aashiq in,sai dai ba'a yiwa Allah dabara, kamar yadda su Maryam suka tafi haka Hudah tabi bayansu,bayan an d'aura auranta da Aashiq an kaita gidansa,yayin da Baffa k'arami yayi kuka ba kad'an ba saboda yana mugun son Hudah,hakama mahaifiyarta da Aasad,duk sun d'orawa Aashiq alhakin mutuwar Hudan,suna ganin kamar shine ya ja hakan,tunda Baffan ya sanar musu ya karya tsafin,shiyasa suka kuma k'udirar bak'ar aniya akan Aashiq in.Mahaifan Baffa k'arami kuwa ji sukayi dama suna da wasu jikokin sui ta k'ara masa har sai komai yazo k'arshe,don jinin Aliyu ba abun k'yamata ba ne a gurinsu.Aashiq kuwa tattarawa yayi ya hak'ura da auran gaba d'aya,ko auran Hudan ma don anfi k'arfinsa ne kafin kuma Faleesha ta shigo rayuwarsa.

Bayan wasu shekaru,Aashiq ya k'ara shahara a fagen buga wasan k'wallo ya tara kud'i na ban mamaki don a lokacin duniya shi take yayi,kafin suna buga wasa wani yayi masa wani irin duka ya fad'i ya samu matsala a k'ashin k'afarsa,wanda dan dole ya hak'ura da wasan k'wallo,tunda ko tafiya ma sai da taimakon sanda yake takawa sosai,yayin da suka yi mishi sallama da dalolin Africa inda ya tattparo ya dawo gida gaba d'aya,ganin tarin dukiyar da yake da ita kuma babu wani amfani da za tayi masa yasa ya fara aikin Allah da ita, ya fara rayuwa irin wacce mahaifinsa ya tafi ya bari,don tun yana yaro yakan ce masa.
"Turaki,rayuwa don al'umma itace rayuwa,ba rayuwa a cikinsu ba,duk irin mutanen da suke d'aukar matsalarsu ita kad'aice matsala,to tabbas tunaninsu tsukakke ne,wa'yanda kwa ke d'aukar matsalar al'umma itace tafi shafarsu to shakka sune masu k'aunar al'umma,kada ka damu da buk'atarka kai kad'ai ka damu da buk'atar ko da mutum d'aya ne."

Ya manta da kansa ya mayar da rayuwarsa ba komai ba,ya mayar da rayuwar alumma itace rayuwa,ba iya kad'ai garin zariya ba,har k'auyuka yake sakawa a binciko masa,duk k'auyan da ke buk'atar tallafi yakan bayar aje a tallafa musu,ya bada jininsa a bawa mabuk'ata,ziyartar gidan marayu kuwa ya mayar da ita al adarsa,ba kuma iya gidan marayun da mahaifinsa ya gina ba,dukkanin yaransa da ke tare da shi,rayuwarsu ya tallafa ya janyo su jikinsa, daga masu shaye shaye sai almajirai da marayu.
Chapter 57 · 0% Book details