Sashe 54
Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read
A yanzu Aashiq ko kwalbar giya ya tsani gani bare kuma cocaine, da na sani yake a baya ma da ya shata, yana tunanin inda k'arfin imaninsa ya tafi a lokacin da k'addara ta bud'o masa shafin jarabawar da ya kasa karb'arta.
Ba zaice yanzu ba ya jin dad'in rayuwar ba, don k'unci da damuwar nan duk yanzu ba ya jinsu, yana baccinsa a ko da yaushe idan ya so ba tare da yasha abin gusar da hankali ba, lallai Asghar da Nusrat haske ne cikin rayuwarsa don har yanzu ba su barshi haka ba sun mayar da rubutu ruwan shansa kuma yana jin dad'i sosai k'wak'walwarsa da zuciyarsa fresh yake jinsu.
Damuwarsa d'aya ce yanzu idan ciwon mararsa ya motsa yakan ji kamar zai mutu sai ya raba dare kafin bacci ya d'aukesa, maganin yanzu ya daina d'aukarsa sai allura ita kuma likita ya sanar da shi za ta bashi matsala, yana d'aya daga dalilin da ya k'ara k'arfin shan giyarsa yana sha in ya make shikenan yanzu kuwa da ya daina shan giyar sosai ciwon ya matsa masa, bai san ya zaiyi ba abu d'aya ne idan ya jewa likitan kayi AURE, kalmar da ya tsani ji a duk fad'in duniyar nan idan har a kansa ne, domin alk'alamin k'addara ya dad'e da musu zanen Katanga tsakaninsa da AURE.
Ba kuma zai iya zina ba, yafi kowa k'yank'yaminta don tun a tashan k'uruciyarsa Aasad yake ta jan ra'ayinsa amman yak'i duk kuwa da kasancewarsa mabuk'aci sai ya gwammace gara yayi aure ko da babu soyayya amman ina auran sai ya gagara domin k'addara ta riga ta gifta a tsakaninsu, amman duk da haka ya kau da idonsa daga mata ya toshs kunnansa da duk abinda Aasad zaice masa.
Hankalin Aasad idan yayi dubu ya tashi, musamman yanzu da yaga Aashiq da Asghar sun had'e sun kuma k'ullewa, amman shi ko wayar Aashiq in ya kira ba ya d'agawa, bai tab'a tunanin a ranar da suka samu sab 'ani zai iya bacci ba tare da ya neme shi ba sai gashi har aka shafe way'annan kwanaki ba tare da ya neme shi ba, idan yaje gidan haka zai tayi knocking ba za'a bud'e ba, Baffa K'arami ya had'asu yayi musu fad'a kan bai dace suna fad'a a tsakaninsu ba, amman duk da hakan bai sakar masa ba, ko da sun had'u duk zancen da zai masa daga um ne ko a'a, idan yayi mishi zancen giya ko cocaine kuwa yakan nuna mishi ba ya buk'atarsu yanzu, hatta su Baffa sun shiga d'imuwa da jin Aashiq ba ya shan komai a yanzu sun fara tunanin waye suke sara yake musu sassak'ainda kai tsaye Aasad yace Asghar ne, yayin da Baffan Asghar in yace zaiyi maganinsa kuwa, shine ya turashi Abuja yace ya koma can da zama ya dinga kula da harkokinsu na can gaba d'aya yafi sintirin da ake ana dawowa,baiyi musu ba ya d'auki matarsa da 'ya'yansa suka koma can da zama bayan ya kawo malamin da yakewa Aashiq rubutu gurin Aashiq in, aka bashi masauki a can bayan gidan, yacewa Nusrat a gurinsa za ta dinga karb'o rubutun Aashiq d'in in ya k'are.
Tun da yayi sallar isha ya samu ya hau gado a daddafe don mararsa ciwo take masa dalilin da yasa bai samu yaje masallaci ba kenan, juyi uake akan gadon cikin matuk'ar azaba, shi kad'ai yasan azabar da yake sha, sai kuma Allahn da ya d'ora masa, tasbihi kawai yake yana kiran sunan Allah.
Bayan sun kammala dinner Hajjaju ta kalli Nusrat tace "Ki kaiwa Turaki nasa, sai kizo kema ki kwanta, ni na shiga daga ciki."
"Toh" Tace mata, bayan barin Hajjaju gurin, na Mallam ta fara had'awa ta tafi kai masa,duk da akwai masu yiwa ma'aikatan gidan abinci suna kaiwa ko ina amman malam ita take kai pmasa safe rana dare,kumama dai ba kowa ne yasan da zaman Mallam in a cikin gidan ba,ta k'ofar kicin da zata sadaka da bayan gidan take bi ta kai masa,banda ba'a mutuwa a dawo da babu abinda zai hana tace Mallam d'innan Babanta ne, suna kama sosai da Baba sai dai shi Mallam ya tara k'asimba da gashi sab'anin Baba da bai barin suma yakance ciwon kai take saka shi, tana jin kusanci sosai da shi, tana jin kamar ta sanshi kamar sunyi rayuwa tare,musamman yadda yake mata in taje gurinsa ya d'auketa tamkar 'yarsa ta cikinsa, itama kuma yana bata nata rubutun tana sha, yace rayuwa cikin mutane da ba ganin zuciyoyinsu kake a kanka ba sai da neman tsari.
Bayan ta kaiwa Baba nasa tazo ta d'auki na Aashiq ta haura samansa, akan dining ta ajiye har za ta juyo taji kawai tana buk'atar sanin lafiyarsa, knocking tayi har kusan sau uku taji shiru, don haka ta murd'a k'ofar a hankula tana zira kanta ciki.
"Zo ki bani ruwa" Yace haka don ya san ita kad'aice za ta shigo masa,kuma tunda suka ga bai sauka dinner ba yasan za'ta kawo masa.
"Hajjaju ce tace na kawo maka dinner."
"Ke dama ai komai Hajjaju ce tace,kizo ki bani ruwa nace." Yap fad'a har lokacin bai d'ago daga kwancen da yake ba,d'an k'aramin pridge in dake bedroom in ta k'arasa ta d'auko ruwan ta tsiyayo a cup ta kawo masa, a lokacin ya tashi ya jingina da fuskar gadon don haka ta zaga ta gefen da yake, mik'a masa tayi ya had'a da hannunta gaba d'aya ya rik'e yana sauke mata idanuwansa da suka k'ara girma suka lumshe saboda ciwon da yake cinsa,wani electrification suka ji a jikinsu, kafin su lumshe idanuwansu a tare su kuma bud'esu a kusan tare, cikin muryarsa da tayi wani irin k'asa yace.
"Da tace ki kawon dinner tace kizo ki duba lafiyata?"
Wata mitsiyaciyar kunya ce ta kama ta gashi dama a takure take da hannunta da ya rik'e, ga sanyin ruwan yana ratsa tafinta yana kuma saukar mata da wani irin yanayi, k'asa tayi da kanta ta fara k'ok'arin k'wace hannunta ganin hakan da yayi yasa ya rik'e cup in da d'aya hannunsa kana ya fisgota gaba d'aya ta fad'o jikinsa tana zazzare idanu cike da tsoro...
Ciwon nono
1-Na'a na'a a dafata ta dinga gasa nonon sau uku a rana
2-Hulba a kwabata da ruwan zafi a shafa a nonon tun yamma har zuwa wayewar gari
3-Bak'in hims a dafa a ruwa a gasa nonon da shi, insha Allah zai sauk'i
[6/9, 8:50 PM] Rabi: 42
K'ok'arin tashi take daga jikin nasa amman bai bata damar hakan ko kad'an ba, sabili kuwa da ba rik'o yayi mata na wasa ba, sai da ya shanye ruwan da ke d'aya hannunsa ya ajiye cup in akan bedside drower kana ya birkita da ita ta haye kan gadon sosai kafin ya rank'wafa kanta yana sauke idanuwansa akan fuskarta, sosai tsoro ya bayyana akan fuskarta,idan ta d'ago za ta mik'e sai ya mayar da ita nan da nan idonta ya kawo ruwa, me ke shirin faruwa da ita,wani shafin kuma k'addara take shirin bud'e mata, ba za ta so k'addara ta bud'e mata wannan shafin ba,shafin da ta san zai risketa da ta rok'i Allah ya d'au ranta tun kan ya nuna mata zuwan wannan rana.
Rawa jikinta ya fara yi sosai yayin da Aashiq ya girgizata kafin ya rungumeta tsam a jikinsa, hawayen takaici da bak'in ciki ne suka zirarowa fuskarta kafin taji muryarsa yace.
"Babu abinda zan miki, na kasa bacci ne so nake ki taimaka mini na samu bacci."
"Amman kasan hakan babu kyau, tunda ni ba matarka ba ce?"
"Na sani."
"To don Allah ka cikani na tafi."
"Bazan iya ba" Ya fad'a da wata irin murya yana k'ara rungumeta sosai, wani irin rauni yake jin zuciyarsa tayi, yana jin kamar ya fashe da kuka.
"Don Allah ki taimakeni Nusss, idan kika tafi mutuwa zanyi, babu abinda zan miki wallahi asali ma ba halina bane, only sleep pls"
Yakai k'arshen maganar yana kuma shigar da ita cikin jikinsa sosai, donma hijabin jikinta duk ya takura masa, sai dai bazai iya cire mata shi ba domin zai k'ara haifar da rashin yadda tsakaninsu.
"Amman kasan da cewa ba zina bace kawai laifi, kusantarta ma babban laifi ne?"
Shiru taji yayi bai bata amsa ba, don haka ta yunk'ura za ta tashi, taji babu hanyar da za ta iya mik'ewa ya riga ya sakar mata nauyi kuma duk yabi ya cukuikuyeta, da alamu bacci ya samu, baccin ma kuwa me k'arfi ne ya fugeshi da alamu ya tara shi da yawa, ita kuwa sam kasa baccin tayi don tsoro bazai barta tayi ba, Astagfirillah take ta ambata a ranta tana ganin duk laifinta ne, da ba ta shigo ba da hakan ba ta faru ba, amman an gama ta rufe shigowa sashensa idan har yana ciki, don ba ta san gaba me za ta haifar ba tunda aka fara da haka, baza ta ce ga lokacin da sarkin iya sata ya saceta ba, sai k'arar kiran sallar Asuba ne ya farkar da su a tare, fitilar gefen gadon ya zira hannu ya kunna kafin ya tashi a hankula ya nufi toilet yana furta kalmar "Thanks" Wanka ya soma yi, don wankan janaba ya hau kansa, ya riga yayi mafarki da Nusrat, abinda bai tab'a yi ba tun tashinsa sai yau d'in, jinsa yayi sakayau duk da a mafarki ne amman yana jin abinda ke mararsa ya ragu, don sharkaf ya jik'e wandonsa na ciki.
Yana shiga toilet in ta yunk'ura da sauri ta fice daga d'akin, kanta tsaye ta bud'e d'akin nasu ta shiga don ta yanke ko da Hajjajun ta farka ba ta ganta ba za tace ruwa taje sha, sai kuma ta samu ma Hajjajun bacci take, don haka kawai ta nufi toilet, don wanka take buk'ata don gaba d'ayanta k'anshin Aashiq take ba iya kayan jikinta ba.
Sai da ta fito daga wankan ta d'auro alwala kana ta tashi Hajjajun,lokacin har an kusa idar da sallah ma.