Sashe 26
Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai meyasa kika cewa Mama ba ki da saurayi? Bayan ga Malam Tajo nan kamar zaiyi hauka a kanki kin kuma k'i ki bashi damar da zaizo ya fallasa asirin zuciyarsa. “
"Bazan tab'a bashi damar hakan ba Shukhura. “
"Saboda me? “
"Saboda girman alk'awari. “
"Hmmm Yayarmu kenan, na tambayeki.“
"Tom Allah yasa na sani.“
"Wai Yaya Rj yace yana sonki ne? “
"A'a baice ba, amman na san ya na dawowa zai gaya mini.“
"Baice ya na sonki ba, amman kike wahalar da kanki gurin zaman jiranshi, baki da tabbas d'in soyayyarki a zuciyarsa, bacin haka Aunty Maryam ba za ta tab'a bari ki auresa ba, domin Hidaya take da burin ya aura.
Dan Allah Yayarmu kiyi watsi da lamarin Yaa RJ, ki tsayar da zuciyarki guri guda, kina da samarin nan ki basu dama har ki samu gwani a cikinsu, don ni a ganina Yaa RJ b'ata miki lokaci kawai yake yana kuma wasa da hankalinki, tun da shekara uku yace miki zaiyi ya dawo, yanzu a k'aida saura shekara d'aya kenan amman me Hidaya tace, cewa tai saura shekaru biyu ya dawo, ke a tunaninki Baba zai barki har nan da shekaru biyu a cikin gidan nan, ko kuma za ki cigaba da nuna babu wanda ke zuwa yace ya na sonki?
Ta yaya kike tunanin zan karb'i lamarin aurena da muhimmanci bayan ke ba kiyi aure ba, har ga Allah ba na son na yi aure na tafi na barki.“
Hannuwan Shukhura Nusrat ta kama ta rik'e da hannu biyu kana tace.
"Ni yanzu ba lamarin Yaa RJ ne ke damuna ba, akwai abinda ke damuna, kuma shi yake hanani karb'ar soyayyar kowa.
Kada ki damu da lamarin aurena Shukhura, shi aure lokaci ne, kowa da akwai lokacin da Allah ya rubuta mata, babu ruwansa da wannan yaa ce ko k'anwa duk wacce lokacinta ya yi shikenan, haihuwa, aure da mutuwa duk tafiyarsu d'aya ne suna zuwar maka ne a sanda ba kai zato ba ba kai tsammani ba, don haka kada ma ki sake ki saka a ranki don banyi aure ba kema ba za ki ba, kin san Baba ba zai d'auki hakan ba, kar kuma ki amfani da hakan kice Mustapha bai miki ba, za ki cuci kanki ne don ni ba na hango aurena a nan kusa, ina ji a jikina akwai wasu abubuwa da zasu faru, amman bansan meye su ba.“
"Wani lamari ne ya hana ki karb'ar soyayyar kowa a zuciyarki. “
Wayar Mama ce tai k'ara alamun an kira Nusrat tace.
"Kinga har ya k'araso ba ki gama shiryawa ba, maza kiyi² ki k'arasa shirin in kin dawo ma k'arasa maganar, kuma ina fatan k'anin nan nawa ya dagargazo miki zuciyarki kafin ki dawo, kizo kiy tai mini hirarsa ina saurare don naga alamun hakan ma tun a waya. “
Murmushi kawai Shukhura ta yi, don har ga Allah muryar Mustapha ta tafi da ita, sakamakon wayar da suka dunga yi, Maryam k'anwarsa ya turo ta anshi number Mama shine yake kiranta suna gaisawa, burinta kawai ta ganshi a fili don ta na fatan ganinsa ya fi jinsa shikwa ya dinga ja mata aji har sai yau da aka kusa cin sati suna wayar sannan yace mata zai zo.
Shi d'inne kuwa yazo, don haka a gaggauce ta k'arasa shiryawa ta fita, Nusrat na ta zolayarta, don sun zamo tamkar wasu k'awaye aminai, don dukansu babu wacce za ta daki k'irji tace ta na da k'awa aminiya sai dai k'awar da za'a gaisa a wuce, sune k'awayen kansu, kuma hakan baisa Shukhura ta raina Nusrat d'in ba........
300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.
Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.
Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.
#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*
Wattpad@Rashuna
https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_
*KATANGA*
____________
*NINE*
Shukhura ta rasa yadda za ta yi da Iya, don abin nata kullum k'ara gaba yake, don idan taje su gaisa bai bata ko ficika ba samun guri take ta zauna, ranar da tai mata haka kuwa mantawa ya yi ya fito babu kud'i a jikinsa, ba ta tashi ba har sai da yace.
"Iya a mini afuwa ban fito da kud'i ba yau, amma gobe insha Allah za kiga sak'o. “
Takaicin duniya ya ishi Shukhura ji tayi kamar ta nitse a gurin da take a zaune don tsabar kunya yayin da Iya kuwa ta wangale baki tace.
"Tom shi kenan jikana babu komi, da yau da gobe duk d'ayane.“
Kunji sai kace ajiya ta bashi, wani d'an iskan kallo Shukhura ta bita da shi a ranta kuwa tace.
'Zanyi maganinki wallahi, yadda ko shi kansa Fandan aka ce gashi a soro ba za ki fito ba, ke ko govnor garinnan El Rufa'i akace gashi yazo zance gurina ba za kiyi gigin fitowa ba.'
Fuska taje ta siyo me mugun abun tsoro, sai dagurintaa ruwa bayan an idar da sallar asham, dama lokacin ne dai² zuwansa, tun yamma da tai wanka ta saka riga da wando dama, don haka sai ta d'auko hijabinta har k'asa ta sanya, Mama dama ta na d'akin Baba don haka sai ta cewa Nusrat.
"Yayarmu bari na fita soro.“
Tace mata.
"Tom. “
Iya na ganin giftawar Shukhura ta fasa tayar da sallar da za tai, don yau ta makara ba ta samu bin jam'in asham ba wani bacci ne ya kwasheta ta na zaune.
Murmushi ta yi ta ziro silifas d'inta ta biyo bayan Shukhura ta na k'iyasta yau sallamar da za'ai mata me matuk'ar nauyi ce, don ta na bin bashin wancen zuwan.
Shukhura na fita soro ta cire hijabinta ta sak'ala shi jikin k'ofa sannan tai saurin d'aura fuskar ta juya baya.
Bakin Iya ya k'asa rufuwa har ta doso soron, dama soron gidan gashi da mugun duhun tsiya, ko hucewa za kai sai ka haska saboda gudun masu lab'ewa, zance ma in zasui sai sun kunna fitila.
"A'a yau kuma ba ku kunna fitilar ba ne? “
Cewar Iya ta na tsayawa a dai-dai tsakiyar soron gidan don ba ta hangar komai kar taje ta taka wani daga cikinsu shiyasa tai maganar don su kunna fitila, wani irin dank'a Shukhura taiwa kanta ta had'a fuskokinsu guri d'aya ta sauya magana zuwa me abun tsoro.
"Ke wata iriyar nanatacciyar tshowa ce, mu ba ma son mutum me son abun Duniya, daga yau idan Mustapha ya k'ara zuwa kika fito sai mun karya tsila tsilan k'afafuwan nan naki masu kama da Babyn roba, kuma mu shanyar miki da b'arin jikinki gaba d'aya. “
Kar kar kar kawai jikin Iya ke yi uwa mazari ihun da taso ta yi ma ta k'asa wani mugun tsoro ne ya shigeta wanda ba ta tab'a jin irinsa ba.
Allahumma inni auzu bika minal kubsi wal kaba isi, kawai take karantawa a ranta kafin Shukhura ta buga mata razananniyar tsawa had'e da fad'in.
"B'ace mana da gani tun kafin mu mayar miki da k'afafuwanki a sama kanki a k'asa.“
Fitsari ne zirrrr ya fara bin k'afafuwan Iya kafin ta juya a guje sai ji kake k'um ta bugu da bango ta dawo baya, wata wahalalliyar k'ara ta saki, ta na so ta rarrafa ta bar soron ma ta k'asa anan ta zube a sume tsabar tsoro da rikirkicewa.
Umma ce ta jiyo k'arar, don haka ta nufo soro da 'yar fitilarta, ta na haskawa taga Iya a sheme cikin fitsari.
"Subhanallahi.“
Shine abinda tace kafin ta juya taje ta kirawo su Baba, ruwa aka watsa mata ta farka a mugun tsorace ganin su Baba kawai ta fashe da mugun kuka, Baba na tambayarta abinda ya faru, kawai cewa take su kamata su kai ta gurinta.
Babu yadda Baba baiyi da Iya ba akan ta fad'i abinda ya faru da ita tak'i, k'arshe tace ina ruwansa ya rabu da ita don dole ya k'yaleta
Mama ta dubi Nusrat tace.
"Kika ce Shukhura na soro, ya kuma ban ganta ba?“
"To nidai Mama haka na ji tace mini, to ina kyauta zaton ban jita dai² ba tun da banga ta d'auki tabarma ba ma.“
Ta na rufe bakinta Shukhura na sallama Nusrat tace.
"Yauwa ga ma ta nan.“
Kafin su amsa mata sallamar.
"Ina kika je? “
Shine tambayar da Mama ta jefeta da ita, sosa kai tai kafin tace.
"Mustapha ne ya kirani gashi a k'ofar gidanmu na fito na anshi sak'o, kuma da na fito ban ganshi ba ina jin zolayata yake, shine muka had'u da 'yar ajinmu muka tsaya muna d'an tattaunawa. “
"Ya yi miki kyau."
Mama tace mata, Nusrat kuwa ta kafe ta da idanuwa, ita ta san dalilin kallon da take mata akan abinda ya samu Iya ne ta na zargin Shukhuran ce tai mata wani abu, murmushi kawai Shukhura ta yi, don ta san in ta ritsa ta dole ta gaya mata gaskiya.
Tun daga wannan ranar Iya ba ta k'ara gigin fita in Mustapha yazo ba, saboda ita kad'ai ta san azabar da ta sha na jinyar goshinta, shi kuwa da yaga kwana biyu ba ta fitowa shine ya cewa Shukhura zai shiga su gaisa da Iya taje ta gayo mata, ko da Shukhura taje kuwa, iya tace ba ta san zance ba, ta yiwa Allah ta yiwa Annabinsa tace masa yasha zamansa ta yafe duniya da lahira, Shukhura kuwa tace ai kuwa sai ya zo ta fita ta na dariya Iya ta banko k'ofarta ta saka sakata tace sai dai yazo ya gaisar da k'ofa alk'ur'an.