← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 69

Sashe 51

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bazan iya ba Hajjaju bazan iya ba wallahi, zuciyata da k'wak'walwata ba zasu iya d'auka ba, bazan iya ba bazan iya ba nace."
Ya fad'a jikinsa yana wani irin karkarwa yana kallon hannunsa yana ganin kamar yanzun ne yake d'auke da gawar Faleesha, ganin yadda ya birkice yasa Hajjaju jan bakinta tayi shiru, ta dawo tattofa mishi adda'a kafin tayi mishi cikin ruwa ta bashi yashi, had'e da rarrashin shi da gaya mishi kalamai masu dad'i.

"Kici gaba da mini addu'a pls."
Yakai k'arshen maganar yana jin kamar ya cire abinda ke k'irjinsa don yayi mishi nauyi, nauyi yadda baza ku fahimta ba.

"Ban jin zan gaza da yi maka addu'a har zuwa ranar da numfashina zai tsaya, tashi muje muci abinci."

Bai yi musu ba ya mik'e, don tabbas yana jin yunwar, bai sani ba ko rashin lafiyar da yayi ne yasa ya daina jin dad'in d'and'anon girkin Baba Azumi, kamar yadda a kwanaki yaji ya canja masa yana mishi matuk'ar dad'i, sai da ya fara sabawa da shi kuma ya canja masa zuwa d'and'anon da bai jin dad'insa a harshe ya fi sonsa gaskiya, amman haka yake daurewa yana turawa saboda yunwa gashi ba ma'abocin cin abincin waje ba.

"A'a Asgharu tare kuke ashe."
Cewar Hajjaju tana kallon Asghar cike da fara'a, murmushi shima yayi had'e da amsa mata da.

"Wallahi kuwa Hajjaju tare muke, ya jikiin naki?"

"Jiki Alhamdlill Asgharu gashi yauma zan hau dining abinda na kwana biyu ban yishi ba, ai zuwan wannan yarinya alkhairine cikin rayuwata, ya ka baro mini kishiyoyina?"

Sai da ya fara sauke idonsa kan Nusrat in yana jin zuciyarsa na kuma nutsuwa da ita kafin ya bawa Hajjaju amsa daa.

"Kai amman naji dad'i Allah ya k'ara lafiya, wallahi suna lafiya suna gaida ki."

"Amin, ina amsawa, taso muyi dinner tare."
Ta fad'a tana daidaita zamanta akan kujerar dining in, shikwa Aashiq tuni dama ya zauna yana amfani da wayar da ke hannunsa.

A hankula ta taso ta fara serving in Hajjaju, kafin ta matsa gefen da yake tana serving insa shima tana amsar yadda zuciyarta ke wani irin dokawa, har ta gama serving insa ta yiwa Asghar ma kana ta yiwa kanta ta ja kujera ta zauna itama duk da tana jin kamar ba ta can canci hakan ba, kamar matsayinta bai kai nan ba,amman ba ta da k'arfin barin gurin saboda Hajjaju.

Duk da k'amshin abincin da ke sirarowa yana shiga k'ofofin hancinsa, yana jin kamar irin k'amshin abincin da yake muradi amman bai ajiye wayar ba ya fara cin abincin sai da Hajjaju ta d'ago ta kalleshi had'e da fad'in.

"Turaki ba za ka ja abincinnan kaci ba sai ya huce, kai da ba ka son hutaccen abinci."

Gabanta ne yayi wani irin fad'uwa jin sunan da Hajjaju ta ambata,don wannan ne karonta na farko da taji sunan a bakin Hajjaju don tun zuwanta gidan bai zo ba sai yau d'in da ya d'ebi kusan sati biyu a kwance bashi da lafiya, ji tayi kamar yanzu ne mutumin nan na mafarkinta yake furta TURAKI, ga wani turakin gabanta sai dai ba ta da tabbacin shi d'inne ko ba shi ba ne.

A hankula ya ja farantin ya fara ci, yana jin yadda d'and'anon ya zauna a harshensa kafin ya d'au cup in black tea yakai bakinsa, shima jinsa yayi yadda yake so yadda kuma yake muradi, ba mamaki wannan yarinyar zuwanta ita ta kamawa Baba Azumi girki shiyasa d'and'anonta ya zauna masa a harshe bayan barinta gidan kuma ya kasa dawo da d'and'anon Baba Azumi na daa da ke bakinsa, duk da itama Baba Azumin ba baya bace gurin iya girki sai dai wannan yafi zamar masa sosai.

"Ka dawo kusa da ni da zama."
Cewar Hajjaju tana kallonsa don jiran me zaice.
"Dama ai kece kika koremu."
"Na koresu dai, kai kuma ka bisu, ka janye mini Aleesha ma, ni kuma naji bazan iya hanaka ba, amman yanzu ina buk'atar ka dawo nan gaba d'aya."

Gyad'a mata kai kawai yayi yana cigaba da cin abincinsa itama kuma ba ta k'ara komai akan hakan ba sai Nusrat ta kalla da ke ta jujjuya cokali cikin plate in."

"Idan zaman anan yana takuraki, ki d'auka kije can d'aki kici."
Kamar jiran umarnin hakan take tayi hanzarin mik'ewa tana barin gurin.
"Tana da hankali, ga nutsuwa ga tsafta,uwa uba ga iya girki,a sashin nan bani da wasu masu girki tace a sallamesu komai ita take mini ba ta gajiya."

"Na fuskanci hakan nima Hajjaju, don na matuk'ar jin dad'in girkin nan sosai."

Cewar Asghar, shi kwa Aashiq bai ce ba kuma sun san bazai ce d'in ba.

。。。

"Zaki iya taimakona gurin ganin rayuwarsa ta dai daita?"
Asghar yace da ita, bayan d'an sabon da ya shiga tsakaninsu na kwanaki, musamman da Aashiq ya dawo gidan da zama sai ya zamana kusan kullum da daddare zaizo suyi dinner tare kuma yakan jaa Nusrat in da 'yar hira haka har ta saki jiki da shi, ko babu komai yafi wancan da ko gaisuwarta ba ya amsawa ba ma ya nuna yasan da tsaiwarta a gurin da yake.

Tasan akan wa Asghar in yake magana,sai dai ba tasan ta ina za ta iya taimakawar ba, bayan ba ta san matsalarshi ba, sai dai wanda ya zauna da shi ne kawai zai gane babu nishad'i a cikin rayuwarsa, ko murmushi zai yiwa Hajjaju idan ta kama, to yakan zo ne babu nishad'i ko kad'an a cikinsa a hak'ik'anin gaskiya yadda ta fahimta rayuwarsa a mugun k'untace take, za ta so itama ta taimaka d'in musamman da taji yanzun Asghar ya gaya mata sai da taimakon wine ko cocaine yake iya bacci, amman ba ta san ta yaya za ta iya taimakawar ba .

"Ina so na taimaka d'in, amman kuma bansan ta ya ya ba."

"A hankula nake so ki shiga cikin rayuwarsa ki zauna."
"Idan na shiga cikin rayuwarsa na zauna, ni kuma tawa rayuwar fa?"
"Ina ji a jikina rayuwarku za ta cure ta zama abu guda d'aya ne insha Allah."
"Ta ya kake zaton hakan zai kasance, bayan ko kallo ban isa a gurinsa ba?"
"Ke kike ganin hakan Nusrat, amman kin dad'e da zama cikin idanuwan Aashiq wannan dalilin ne yasa ba ya son kallonki saboda ba ya k'aunar alak'arki da su, saboda ya riga ya,haramtawa zuciyarsa motsi akan kowa, ina so ki k'aryata hakan,ki nuna masa bashi da ikon yin yadda yaso da rayuwarsa wannan ikon yana hannun mai duka ne, ina so ki kasance a duk inda zai kasance, kuma kiyi abinda zaki janyo don dole ya kalleki, ta silarki muke saka ran dawowar nishad'i cikin rayuwarsa , kada ki ruguza mana haka pls ina rok'anki"

"Zan gwada"
"Ni kuma zan taimaka, Allah ya bamu nasara amin"

Turare ya bata wanda za ta dinga yi ta tabbatar Aashiq in ya shak'a, sai tofi da rubutu wanda yace ta dinga mishi amfani da su gurin black tea in da yake so, ta fara mishi amfani da rubutun da tofin amman turaran ne har yau ba ta samu damar hakan ba, kuma ba ta gano ta inda za ta shiga cikin rayuwarsa ba don yanzu sai taga kamar ma yafi d'aure mata fuska akan daa....

Game da masu bukatar haihuwa.

1-Hurmul,ki dafasa ki zauna a ciki, kiyi kamar sau uku a sati, zaa dace indai mijinki ya sadu dake, idan Allah ya kawo rabon.

2-D'anyar gyad'a,ki dakata sai kina sha da ruwan d'umi.

3-Man rid'i, kina shafashi a mararki.

4-Yayin da kuna saduwa kina karanta Astagfirillahil azim wa atubu ilaihi.

5- ki soya k'wan agwagwa da man tafarnuwa ki ci.

Allah Ubangiji kasa mu dace.
[6/8, 6:01 PM] Rabi: 39

~BAYAN WATANNI UKU~

Har zuwa wannan lokacin Asghar bai daina kawo mata tofi da rubutu ba ita kuma sai ta dafa mishi shayi da shi saboda mayan black tea ne safe rana yamma dare sam ba ya gajiya, turaran kuma ta samu damar yi masa amfani ne ta hanyar gyara masa d'aki da take yi, kasancewar babu wasu masu aiki da suka rage a sashan kuma bazai yuhu kartin namiji ya dinga shigo musu ba don shine yake yi mishi a can gidan Baba Azumi kasancewar yana da k'ofarsa ta shi kad'ai nan kuwa dole sai ka ratso ta falon kana za ka hau matattakalar da za ta kaika zuwa sashensa.

Yawanci duk sanda za ta yi gyaran yana nan bai fita ba,kasancewar ba office yake zuwa ba, sai dai in zashi ziyartar gidan marayu ko asibiti don ba da jini ko kuma gurin su Baba Azumi ko gun Baffanninsa kuma yawancin fitar tasa da yamma yake yi, in ta gyara falo ta kan k'wank'wasa mishi domin ya dawo falon ta gyara ciki, to sai ta tsaya rik'e da garwashin da ta wura ta kuma zuba turaran a ciki idan ya fito ta tabbata zai shak'a a haka ta dinga masa amfani har ya k'are.

Ba za'ace ba'a ganin ci gaba ba,don sosai ya rage shaye shayen nasa ba kamar daa ba, tsakaninshi da Nusrat kuwa gaisuwa ce in yaga damar amsawa, duk wani kakkauce matan da yake bai hana ta k'ara yin kusancin da idanuwansa ba, tana motsa dukkan wani gurbi da yayi tunanin ya dad'e da daina aiki cikin zuciyarsa ba kuma zai kuma tashi ba, amman Nusrat tana k'ok'arin k'aryata tunaninsa don sosai yanzu zuciyarsa take doka mata,hakan yasa shi kuma d'aure mata fuska fiye da daa, don sam ba ya k'aunar kusancin da zuciya da idaniyanshi suke nema daga gareta, banda bakinsa da yasaba da d'and'anon abincinta da tsaf zai iya komawa can gurin su Baba Azumi to ya tabbata cin abinci zai kawoshi gidan, anyi ba'ayi ba kenan.
Chapter 51 · 0% Book details