← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 69

Sashe 37

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan gama cin abincinsu duk a falo suka yada zango kowa yana ta zuba santin dadin abincin, kasancewar basu taba cin jalof in taliya da taji kayan had'i irin haka ba, hasali ma basu taba cinta da hadin coleslow ba sai yau, Daddy me k'orafin baison jalof in taliya in ba a lokacin zaici ba sai gashi yace gobe ma da ita zasui dinner.
Sun gaisa da Nusrat ya k'ara mata ta'aziya, ya kuma ce yaji dad'in tahowa da akayi da ita, zai rik'eta tamkar su Hidaya, shima yana so ta rik'eshi tamkar mahaifinta duk abinda take bukata kar taji nauyin sanar da shi, yayin da ita kuma ta dunga zuba mishi godiya, yana shirin barin falon yace.
"Nusrat da fatan kin taho da takaddun makarantarki, da zaman da zaki kawai kema zan nema miki Buk sai ku dinga tafiya da Hidaya?"
Wani mugun sanyi ne ya ratsa zuciyar Nusrat, tana da burin yin karatu,kuma bata taba tunanin zata samu cikar wannan burin nata ba cikin sauk'i, sai gashi babu zato babu tsammani burinta na gab da cika, yayin da Aunty Maryam kuma taji k'irjinta yayi mugun bugawa, ita mahaukaciyar ina ce da zata bari ya saka Nusrat in a makaranta, to kenan meye amfanin tajowa da ita, saboda girki ta daukota idan kwa tayi saken da ya sanyata a makaranta to tabbas girki kanta zai dawo babu batun hutun da take hangowa kanta, kuna ita a rayuwarta ba ta k'aunar mijinta ya kashewa wani kud'i idan ba ita da 'yayanta ba, inda Allah ya taimakeshi don a tsaye yake shiyasa yake samu yana hidimtawa yan uwansa, kuma Aunty Maryam ba ta iya bin malamai ba batta da bak'in halinta dai, Nusrat in na k'ok'arin yin magana yayin da Aunty Maryam tayi saurin rigata da cewa.
"Ai Dadynsu Nusrat bata da sha'awar yin karatu kwata kwata, tun sanda akayi bikin su Shukhura na samu na lallaba Yaya Audu akan ya bar Nusrat d'in ta fara zuwa ko ABU ce kafin itama Allah ya kawo mata nata mijin,ni zan dauki nauyin karatun nata amman yarinyar nan ta bulan k'asa a ido, ta tirje ita akan baza taci gaba da makaranta ba."
Takai k'arshen maganar tana jifan Nusrat in da kallon gargad'i.
"Kekuwa Nusrat me yasa ba kya son karatu, karatu da kike gani yana da mugun muhimmanci cikin rayuwar dan adam,kuma shine hasken rayuwarsa, yanzu ma mazan sunfi son mace me ilimi, nidai inai miki sha'awar cigaba da makaranta, idan kin shirya hakan kozo ki sameni."
K'asa tayi da kanta don jin yadda k'walla ta ciko mata idanu cikin sanyin murya tace.
"Ni da saboda yadda nake jin ana fadin tarbiyar yara na lalacewa shiyasa nak'i yadda, amman insha Allah zanyi tunani na gode."
"Hidaya ki wayar mata da kai, duk abinda kuka yanke kuzo ku sameni."
Hidaya da bakin cikin Momyn tasu duk yabi ya isheta, don ita a sanin da tayiwa Nusrat tana da mugun son cigaba da karatu don kawai bata samu damar hakan bane, yana daya daga cikin abinda yasa taso Nusrat in ta biyosu bayan mutuwar Mama don ta samu damar cigaba da karatun amma Nusrat in tak'i, wannan labarin k'anzon k'uregen da Momy tayi kuwa ba ta san lokacin da akayi ba, kuma ba ta jin ma anyi hakan, kawai Nusrat in ta karbi hakanne don babu yadda za tayi kuma ta lura da irin kallon da Momyn ta jefeta da shi.
"Zan wayar mata da kai kuma zata aminta insha Allah."
Tacewa Dadyn nasu da ya fara hayewa samansa

Wani shegen kallo Aunty Maryam ta watsawa Hidaya kafin tayi hanyar kitchen hade da cewa Nusrat ta biyota.
"Nusrat kar kiga laifina ko d 'aya, na d'aukoki ne dama saboda girki Daddynsu ba ya cin abincin 'yan aiki kuma bai yadda 'yayansa ma suci ba, wannan dalilinne yasa bani da me girki, to shiyasa na d'aukoki, yanzu idan na bari kika fara zuwa makaranta ai banga amfanin tahowa dake na ko kad'an don haka ina umartarki ki cire rai da karatu don bashi na d'aukoki yi ba, ki kuma sanar mishi ke sam ba kya sha'awar cigaba da karatu, kika sake kika bada k'ofar da zaisan ni na hanaki wallahi sai nayi mugun sab'a miki ko da kuma kin koma can zariyan da zama baza ki taba jin dadin zaman can ba don sai na kuma lalata tsakaninku.

"Bama zan bada k'ofar hakan ba, zan sanar masa kamar yadda kika ce."

"Hakan shine zaman lafiyarki kuwa."
Daga haka ta shiga nunnuna mata duk wani abin amfani a kitchen d'in, ta kuma sanar mata daga yanzi ita zata dingai musu Break fast,launchin nd dinner.

Hidaya kamar za tayi kuka ta samu Aunty Maryam akan ra bar Nusrat in ta soma makaranta, amman ta rufe ido taiwa Hidayan tatas kuma tace ta sake ta sanarwa Daddynsu ita ta hana sai tai mugun sab'ar mata.

Hidaya da Nusrat babu wata hira da suka yi suka kwanta kasancewar zuciyoyinsu babu dad'i kowa da tunanin da yake sak'awa, ita Hidayan kunyar Nusrat inma take ji saboda abinda Mommyn tasu tayi mata, ai ko babu komai Nusrat d'inma d'iyarta ce kamar yadda suke 'ya'yanta, amman son kan Momyn tasu yasa taki fahimtar hakan duk ko k'ok'arin da tayi na fahimtar da ita sai ma rabuwar ba dadi da sukai tsakaninsu.

Washe gari tun asuba da ta tashi ba ta koma ba ta sakko k'asa ta had'a break fast ta jeresu akan dining, kana ta koma sama ta kwanta a lokacin Hidaya har ta gama shiryawa, Hibba da Abbas ma haka, Abdul shi ya gama secondary nan da sati aya ma zai tafi chennai acan zaici gaba da karatunsa, Abbas ma saura shekara daya ya gama yana gamawa zai bi bayansa, Hibba kuma wannan shekar zata tafi SSS one tare suke tafiya da Yusra saanni ne ma....

200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.

#NWA
#KTG
[4/26, 8:43 PM] Rabi: BEBE'ARTH

Wattpad@Rashuna

®️NAGARTA WRI.ASOCIATION

KATANGA...

In baki siya ba ya kamata ki mallaki naki a hannu kar garab'asar ta wuce ki, in na gama free page zaki siyeshi akan 300 ne,kuma in kin siya yanzu zaki samu damar karanta CIN AMANA kyauta, kada ku bari wannan garabasar ta wuceku, kada ku manta akwai abin amfani a ciki.

Masu tambayata document in na gama, shi kuma zaku sameshi akan 500kacal.

...............22

A cikin 'yan kwanakin da Nusrat tayi kowa yana mugun jin dad'in zama da ita, ga kuma girkunan da take musu kala kala wanda da basa samun kamarsa saboda k'iwar Aunty Maryam, shi kanshi Daddynsu yana mugun jin dadin girkin Nusrat in kullum cikin zuba santi yake yana shi mata albarka.

Ko a fuska ba ta taba nunawa Aunty Maryam taji zafin hanata makaranta da tayi ba, ta saki hakan a ranta idan Allah ya rubuta za tayi to tabbas ta tabbata hakan zaizo cikin sauk'i, abinda tayi amanna da shi kenan ta saki ranta tana mugun ji da Hibba tana jinta tamkar Yusranta don tana mugun d'ebe mata kewarta, yanzu haka ma tare suke a kitchen za ta d'ora dinner sai Hibba cewa tayi.
"Dan Allah Yayarmu kiyi mana macaroni yau duk gidannan."
Bata damu da macaroni ba, sam ba ta birgeta a cikin nauikan abinci, kuma a dan zamanta a gidan ta fuskanci suma basu wani damu da ita ba shiyasa ba ta tab'a gigin dafata ba, amman yau da Hibba ta buk'aci hakan sai taji kawai tana sha'awar dafa tan."

"Ai ba ma sai kin hadani da Allah ba, yau kowa da macaroni zaiyi dinner."

Tsalle Hibba tayi had'e da fad'in.
"Yeee Yayarmu shiyasa nake mugun sonki, da me zan kama miki?"

Murmushi Nusrat tayi had'e da fad'in.
"Nima ina sonki Hibbata."

Kafin ta bata abinda zata rage mata da shi.

Hidaya ce ta shigo kichen in ta tarar da su suna yanka salak,cabeji da su cocumber suna hira, kasancewar yau da wuri ta dawo daga scl takadda daya suka zana, da dukkan alamu Hidaya Aunty Maryam ta biyo don itama mugun k'uiyya ce da ita ba kamar Hibba ba da bata da son jiki ko kad'an, don ba ta yadda masu aiki su gyara mata dakinta da kanta take gyare abinta sakamakon Hidaya da komai ma 'yan aiki ne suke mata zuwan Nusrat ne itama ta daina bari 'yan aiki suna gyara musu take yi da kanta.

"A'a yau wani delecious in ake had'a mana kuma?"

Takai k'arshen maganar tana bud'e tukunyar da Nusrat in ta zuba macaroni tana ta tafasowa, yatsina fuska tayi tana kallonsu gaba aya, yayin da Hibba ta k'yalk'yale da dariya.

"Haba Yayarmu me yasa zaki biyewa Hibba ki dafa wannan abar, wallahi kaf gidanna babu me sonta hatta Daddy ma, Hibba ce kad'ai don kuma ita kad'ai Daddy yake bari ana had'owa da ita cikin kayan abinci, in tana shaawa sai ta saka a dafa mata."

" Yo ni da nake bak'uwa ai ban san da haka ba, yanzu tun da na riga na dafa haka kowa zai hak'ura yaci, nima ba sonta nake ba, amman tunda Hibba na so babu case ko Hibba?"

"Haka zancenki yake Yayarmu babu d'igon gyara ko aya."

Wata muguwar harara Hidaya ta zabga mata had'e da fad'in.

"Ku da Daddy don nikam babu ruwana."

Daga haka ta juya ta bar kichen in cike da takaici, don tayi mugun tsanar macaroni gashi wata muguwar yunwa take ji, ulcer inta ce ta motsa da taci abinci za taji tamkar ba ta ci ba.

"Ai kar ki damu, idan Daddy yaci wannan girkin na tabbatar miki sai yayi mana babbar kyauta."

Cewar Nusrat wanda ba ta tabbatar taji ta ko ba ta ji ta ba.
Chapter 37 · 0% Book details