← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 69

Sashe 67

Katanga Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kuka Umma take sosai na azaba,tana jin gara kawai ta gaya musu abinda tayi ko ta samu damar neman yafiyarsu ko ta samu sauk'in azabar ciwon da k'afarta take mata,tana jin kamar alhakinsu ne,tana kuka ta shiga gayawa Baba sihirin da tayiwa Mama yayi sanadiyar mutuwarta da farrak'un da tayi tsakanin Shukhura,don kawai ta mori dukiyar mijin Shukhuran,to ga dukiyar nan ta mora shin me ta tsinana mata?a yawon bin boka duka suka tafi gashinan tana karb'ar hukuncinta tun a duniya kafin taje can,a sanda take fad'ar Nimha ta shigo,kud'i ne ya narkewa Saminu a kaa,komai da ya mallaka an siyar hatta gidan da suke ciki amman bai kai kud'in da ake binsa ba shine jiya police suka zo suka tafi da shi,duk abinda mahaifiyarta ta fad'a a kunnanta suka sauka,ta fashe da wani irin kuka zuciyarta tayi nauyi da me zata ji ina kuma zata saka ranta,hannun Shukhura Baba yaja suka fita don bai san me zai cewa Umman ba, kawai dai yasan k'arshen zamansu ne yazo don ya gama auranta har abadan abadina....
[7/1, 7:37 PM] Rabi: 53
Suna kicin suna had'a dinner ita da Yusra,a gaggauce suke yin komai kasancewar yamma ta kawo kai,kuma tasan Aashiq yana hanya,tun safe suka fice da Asghar,kuma ba ta samu wayarsa ba har yanzun,tana aikin tana tunanin ko lafiya ta jishi shiru haka,wayarta ce tayi k'ara,agaggauce ta k'arasa gurin da wayar ke ajiye don duk a tunaninta Aashiq ne sai taga number in da ba ta sani ba,a sanyaye tayi peaking in wayar,ba zato ba tsammani taji muryar Shukhura tace."Yayarmu." "Shukhura"Nusrat ta fad'a cike da shakkun ko ba dai dai kunnuwanta suka jiyo mata ba. "Na'am Yayarmu ina bakin estate d'inku." Lumshe idanuwanta tayi ta bud'e tana furta Alhmdlillahi cikin zuciyarta,kafin tace. "Ki jira yanzu za'a zo a taho da ke." Tana kawowa nan ta kashe ta fara lalubar number Khalili da yake ba tare suka fita da Aashiq ba,yana d'aga wayar ta sanar mishi tana da bak'uwa a babban gate,Allah Allah take taga Shukhuran tazo kar taje kafin zuwan Khalil ta bar gurin,don gani take kamar ba gaske ba,wai Shukhuranta ce ta kirata a waya,ta kuma tako inda take.Ita kanta Shukhura a gaggauce take taga anzo tafiya da ita, babu yadda Baba baiyi akan ta bari da safe tazo don ganin magariba ta kawo kai,amman ba ta jin za ta samu nutsuwar zuciya idan ba ta saka Yayarsu da Yusra a idonta ba, ganin ta kafe kawai yasa ya rabu da ita,don bai manta kafiyar Shukhura ba,in tace sai tayin nan sai tayi,duk abinda zaa mata sai dai a mata,daga k'arshe ma fitowa tayi daga cikin motarta ta tsaya tana baza idanuwa,da yake Najib bar mata motar yayi yabi ta haya ya koma,babu inda ba ta zuwa da mota kawai dai Mustaphan ba ya so tayi dogon tuk'iy.Ganin itama a mota take sai Khalil d'in yayi gaba yace ta biyoshi a baya,cikin Yusra da Nusrat ban san wa yafi matsuwa yaga Shukhura ba,Hajjaju sai kallonsu take yadda duk suka je bakin k'ofa suka tsaya suna jiran a danna bell,dukkaninsu sun mata uzuri,sun san ba laifinta ba ne,a kullum zaman jiran dawowarta garesu suke,tunda kwa ta dawo ba za suyi sakaci ba,zasu karb'eta su manta da baya su fuskanci gaba,a kusan tare hannunsu ya sauka gurin bud'e k'ofar bayan da aka danna bell d'in,sai dai suna bud'ewa fuskar Aashiq ta bayyana da ta nuna gajiyar da yake tattare da ita,hannun Nusrat kawai ya kama ya jata zuwa matattakalar bene,sai dai suna tafiya tana waigowa tana kallon k'ofa,murmushi Hajjaju tayi kafin tace. "Turaki" Waigowa yayi don sam bai lura da Hajjajun ba tsabar gajiyar dake jikinsa,so kawai yake ya jishi cikin ruwan d'umi ko gajiyar za ta saki. "Jiran zuwan Shukhura take,kada ka b'ata mata wannan damar." Cewar Hajjaju tana kallonsa, gajiyayyun idanuwansa ya sauke akan Nusrat d'in kafin ya juya ya tafi ba tare da yace komai ba, yana buk'atarta kusa da shi sosai,amman bai jin zai b'ata mata wannan damar kamar yadda Hajjaju tace,banda a gajiye yake zai tsaya yaga farin cikinta,domin dariyar Nuss dariyarsa ce farin cikinta farin cikinsa haka ma kukanta kukansa ne,shiyasa kullum yake da burin ganin farin ciki ya wanzu cikin rayuwarta.
Bakin k'ofar ta koma suka dasa sabon zaman jira,k'ofar ma a bud'e take bayan shigowar Aashiq Yusra ba ta rufe ba,da ita da Amnan gaba d'aya suka bi suka cukuikuye suna ihun murna,sun rasa ina zasu tsoma ransu don dad'i,kafin su dawo kan Amna wannan ta d'auka wannan ta ajiye suna jin wani iri sai yanzu ta sansu,kamata yayi tun zuwanta duniya ta dinga ganin gilmawarsu har ta fahimci su d'in iyayanta ne,amman haka Allah ya tsara ba su isa su kaucewa hakan ba,Kallonsu Hajjaju take cike da sha'awa,soyayyarsu da k'aunarsu ta burgeta ainun,wacce ta raba soyayya da shak'uwar nan ta d'au alhakinsu,alhaki kuwa ba kad'an ba,tana jin da ace Allah ya bata zuri'a da yawa tabbas da irin wannan KATANGAR za ta gina a tsakaninsu.

Sai da suka gama murnar ganin juna suka nutsu,kafin Nusrat ta raka Shukhura d'aki,Yusra kuma ta tafi da Amna,bayan ta raka Shukhuran d'aki tace ta kimtsa kafin itama ta haye sama,sanda ta shiga d'akin sai a sannan ya fito daga wankan,ta baya ta rungumeshi,daga yadda yaji rungumar yasan yau Nunus d'insa farin ciki ya cika zuciyarta,zago da ita yayi gabansa yana ganin yadda murmushi ke kwance saman fuskarta,lumshe idanuwansa yayi yana kuma warasu akan fuskarta da tayi mishi kyau,har zuciyarsa ta fara wani irin yamutsawa,rungumeta yayi tsam yana shin shinar wuyanta,yadda take cikin farin ciki ya tabbata zai samu kanta fiye da yadda yake zato,yadda taji yana kuma matseta cikin jikinsa yana shin shinar wuyanta da k'irjinta yana wani lumshe ido tasan akwai bayani,sai ta fara d'an jan jikinta tana fad'in.
"K'auri fa nake." Bakinsa kawai ya saka cikin nata ba tare da ya bata amsa ba,kafin ya d'auketa ya nufi gado da ita,d'an dukansa ta fara yi tana."Sallah fa za'a kira." Inaa ai sam ba ya sauraranta bare yasan me take fad'a.
Chapter 67 · 0% Book details