Sashe 61
Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read
Suna d'aki da ita da Yusra sai su Rabeeah,su Baba Azumi suna tare da Hajjaju,da Hajja,sai Mami mahaifiyar Aasad,sai kuma mutanen cikin estate in, ba wani taro akayi ba,don ko su Baffa Ibrahim Hajjaju cewa tayi a rabu da su tukunna a gani,a d'aura aure in komai ya dai daita sai ai shagalin bikin daga baya.
Ta sha kwalliyarta cikin shiga ta alfarmaFareeda tana ta zolayarta tayi shiru gabanta sai fad'uwa yake,Ji sukayi ana salati da sallallami a falon ai ta rigasu mik'ewa ta fito karaf a kunnanta maganar ta sauka.
"Allah ya amshi ran Aashiq."
Maganarsa ce ta jiya da daddare ta fad'o mata a rai.
"Nuss,ina jin a jikina na kusa baki fili,filin da zai baki damar auran wani ba tare da tunanin komai ba,in na mutu kiyi murmushi a duk sanda kika tuna ni,idan tunanina yana sakaki kuka to sam kada ki tunanina."
Wani irin gunjin kuka ta saki ta zube a gurin.
[6/23, 10:50 AM] Rabi: 48
Kai Hajjaju ta rik'e tana jujjuyawa,da na sani yana mugun lullub'eta,daa tasan mutuwa zaiyi da babu abinda zaisa ta matsa sai anyi aurannan,shi kenan yanzu shi da take gani taji sanyi a ranta shima yabi bayansu,dama shi kad'ai ne irinta ya rage mata wanda take gani yake rage nauyin zuciyarta,gashi ya tafi ba tare da ya bar mata wani irin ba,yanzu kam ita babu mutuwar da ba ta ga
ni ba,taga ta mahaifanta,mijinta,'ya'yanta,jikokinta,yanzu kawai tata take zaman jiran zuwanta kawai.
Nusrat kuwa a gurin da ta zube numfashinta ya dinga sama yana k'asa,rik'eta Yusra tayi tana jijjigata tace.
"Yayarmu ki ja numfashin,kada ki sake shi don Allah."
Jan numfashin take amman ta kasa jansa daga k'arshe ya tsaya cak,jikinta ya saki gaba d'aya.
"Yayarmu"
Yusra ta k'walla kiran sunanta cikin fitar hayyaci tana jijjigata,Ramla ce tace. "Ki nutsu Yusra, ba mutuwa tayi ba suma tayi,bari a yayyafa mata ruwa."
Farida ce ta mik'o ruwan aka yayyafa mata amman shiru ba ta motsa ba,ganin hakan yasa Baba Hadiza fita harabar gidan ta cewa Kalil ya tayar da mota,kafin ta koma ciki tace su kamota a nufi asibiti da ita,daga Baba Hadizasai Farida,sai Yusra da ta shige gaban motar suka tafi asibitin,suna zuwa aka karb'eta don bata taimakon gaggawa,musamman ma da aka ga daga gidan da suke.
"Dogon suma tayi,zata farka insha Allah."
"Ai ba son farkawar tata nake ba,saboda itama tsafi ya nuna bazaiyi aiki a jikinta ba,kamar yadda baiyi a jikin Falisha ba,shiyasa na saka aka fasa cewar Aashiq ya mutu,don estate in ta hargitse mu samu damar kashe Nusrat in, amman maganar gaskiya ban sani ba yana raye ko ya mutu,sai dai na san suna tare da Asghar ban kuma san a ina ba,na kira shi shima tsinanne yak'i d'agawa,in bai wasa ba zai riga Aashiq in yin gaba wallahi,to kuma sai gashi tazo hannu cikin sauki don haka so nake ka k'arasata da wannan allurar."
"In dai aikinka ne ban jin yinsa saboda na san zaka min biya da me kauri,bara na d'auko sirinji."
"Ok" Yace da shi yana peaking in wayar da ta shigo masa,had'e da nufar k'ofa zai fita,sauke nunfashin da ta rik'e tun d'azu tayi,saboda kada su san ta farka,kafin tayi saurin sakkowa daga gadon ta nufi k'ofar za ta fita,gabanta na dukan tara tara,sai dai tana kai hannu za ta tab'a handle in k'ofar taga alamun ana murd'asa ta waje,sai tayi saurin b'uya a bayan k'ofar,Aasad yana shigowa da yake kansa yana kan waya bai lura da babu kowa akan gadon ba,sai da ta bud'e k'ofar ta fice da gudu,kana ya d'ago ya kalli gadon yaga wayam,bai san sanda yayi wani irin zagi ba ya biyo bayanta,da gudu ta iske Baba Hadiza da Farida. "Ku tashi mu gudu mu bar asibitin nan,ku tashi." Shine abinda tace da su,ba ta saurari me zasu ce ba tayi hanyar da za ta sadata da waje da gudun gaske,su Baba Hadiza suka bi bayanta a tsorace,suna tunanin ko ta haukace ne,Fareeda tana yi tana waigawa ko za ta hango Yusra,kada ta dawo ta tarar ba sa nan.
"Ba wata matsala ba ce insha Allah,ya shiga rud'u ne,amman zai farka insha Allah ba da jimawa ba" Cewar Dr Sa'ad yana kallon Asghar,jinjina masa kai kawai Asghar yayi,kafin Dr Sa'ad in yayi mishi sallama ya tafi,bai jima da tafiya ba Aashiq in ya farka,idonsa akan Asghar ya fara sauka,a hankali ya mik'e zaune yana jin yadda kansa yayi masa matuk'ar nauyi. "Rayuwar wa kuka saka cikin had'ari?" Ya jefowa Asghar tambaya."Ba mu saka rayuwar kowa a had'ari ba,ka kwantar da hankalinka insha Allahu wannan karan babu abinda zai samu auranka." "Ba zaka gane yanayin da nake ciki ba Asghar" Yace haka,muryarsa na bayyanar da yadda zuciyarsa tayi rauni,Nusrat kawai yake son gani ya shiga jikinta ko zai samu nutsuwa. "Kira mini Nuss" "Ita da take amarya ai ba zaka samu damar ganinta ba,ka bari zuwa dare tukunna." Wani irin bugawa zuciyarsa tayi har sai da ya danneta da hannunsa kafin yace. "Idan Nunus ta bar rayuwata bazan tab'a yafewa kaina ba,nima kuma na tabbata bazan k'ara ko minti aya a duniya ba zanbi bayanta."
"Ba za ta mutu ba,ka daina kawo hakan a ranka." "Ta ya kake son na yadda da kai,Falisha sai da na saki jiki sannan ta barni,Nunus kuwa zuciyata ce ita da rayuwata gaba d'aya,rashinta yana nufin rasani nima."
"Tabbas za ta mutu,amman ba yanzu ba insha Allah,za kuyi rayuwa mai tsayi da izinin Allah,za kuma kace na gaya maka."
"Ka kira mini ita don Allah"
Baice komai ba ya d'auki wayar Aashiq in da ke gefensa ya lalubo number in Nusrat in ya danna mata kira,sai dai har yayi 4miss call ba tare da an d'aga ba. "Kira Yusra" Aashiq yace da shi don yasan duk inda take to tabbas suna tare,bugu d'aya yayiwa number in Yusran ta shiga,a lokacin suna tsaye suna jiran tsammani daga likitan da ya shiga gurin Nusrat in wayar ta shigo mata,hannunta na rawa ta d'aga saboda ganin me kiran,Yayanmu,kamar yadda tayi saving in numbersa,da ta d'aga kwata kwata ba ta jin me ake cewa, hakan yasa tayi d'an gaba da gurin da suke,tana tunanin ko gurinne babu network, wata kujera ta samu ta zauna akai,tana shirin bin bayan kiran sai gashi wani ya kuma shigowa da hanzari tayi peaking. "An tayar mana da hankalin cewa ka mutu,gashinan Yayarmu ta suma,har yau an kasa gano kanta." Ta kai k'arshen maganar hawaye masu zafi na biyo kuncinta." "Subhanallahi yanzu tana ina Nusrat d'in?" Jin muryar Asghar ba ta Aashiq ba ta sa ta cewar. "Yaa Asghar ina Yayan namu,ko ya mutun da gaske ne?muna nan asibitin gogel."
"Go me?" Ya tamvayeta a gigice."Gogel" Ta bashi amsa,d'if ya kashe wayar,bai tsaya ya saurari Aashiq ba ya zari key in mota ya fice a gagauce,yana zuwa bakin gate in Nusrat na fitowa da gudun gaske,Allah yasa idonsa ya sauka a kanta,"Nusrat" Ya k'wala mata kira yana zaune a cikin motar,tana waigowa kwa idonta ya sauka a kansa ta nufi motar,su Farida ma da suka fito suka maro mata baya,gaban motar ta bud'e ta shiga ta zauna,sai a sannan wani azababban kuka ya kubfce mata,baice da ita komai ba ya barta ta samu nutsuwa tukunna,ko su Baba Hadizan bai tambaya ba da suka bud'e gidan baya suka shiga,yana k'ok'arin tayar da motar Farida tace."Yusra kar tazo tana nemanmu ban san inda tayi ba."
A firgice Nusrat ta d'ago jajayen idanuwanta. "Bari na kirata a waya tazo ta samemu mu tafi." Cewar Asghar yana nemo numberta ya danna mata kira.
Gaba d'ayansa ya shiga tashin hankali mara misaltuwa,ya rasa wani irin tunani zaiyi,shikenan asirinsu ya gama tonuwa, bashi da wani abu da zai kare kansa dole sai an tuhumesa,tuhumar da za ta tono abubuwa da dama,kawai ganin Yusra yayi a gabansa tana tambayarsa.
"Banga su Aunty Frida ba,ko Yayar tamun ta farfad'o ne?" Hannunta ya ja zuwa d'akin ba tare da yace mata komai ba.
"Idan kina son rayuwarki da ta Yayarki ta tsira,to ki kira wayar da za ta had'ani da ita yanzun nan."
Zaro idanuwanta tayi don ba ta gama fuskantar inda maganarsa ta dosa ba,sai kuma ga kira ya shigo wayarta,fusge wayar yayi yana k'arewa number kallo,tun a kallo d'aya da yayi mata yasan number Aashiq ce. " Yaa Asghar ne." Baice da ita komai ba yayi peaking wayar yana sakata a speaker kafin ya d'ora mata wuk'a a mak'oshinta.
"Yusra kina ina ne?Ki fito muna bakin gate muna jiranki."
Muryar Asghar ta bayyana a cikin wayar. "Ina Yayarmun?"
"Ga ta nan muna tare." "Bata wayar" "Ok tom" Yace yana bawa Nusrat wayar, ba ta kai ga magana ba taji muryar Aasad. "Idan kina son rayuwar k'anwarki zaki iya jan bakinki kiyi shiru da abinda kika ji,muddun kwa kika gayawa ko mutum d'aya ne,to da ke da shi da k'anwarki zaku bak'unci lahira a yau yau d'in nan." Rintse idanuwanta tayi hawayen tashin hankali na kuma zirarowa ta kuncinta.
"Me tace?" "Tace tayi nisa za ta biyo keke nape ya ajiyeta." "OK" Yace had'e da tayar da motar suka nufi gida."