← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 69

Sashe 34

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana nan tsaye suka fito shi da likitan, ta cikin nik'af inta take k'are masa kallo, saurayine kyakkyawa da shi amman yake wannan d'anyen aikin shikwa me yasa, ba dai zai wuce kud'i ba wanda tasan sune zasu saka likitanma ya amshi buk'atarsa, a ranta kawai taji tana adduar Allah yasa kar dai likititan ya amshi buk'atarsa, kai da ma wuya kam don irinsu in baa amshi buk'atarsu ba kashe mutum suke.
Yusra ce itama ta taho bayan ta fito daga d'akin da Baba yake, sakin baki tayi tana kallonta yayin da likitan ya nufota yana kiranta "Murja" Da alama sunan wacce ta bata kayan kenan, yayin da k'irjin Yusra ya fara wani irin bugu ta daskare a gurin a tsaye...

Nayi k'okari ai, dogon typing yana bani wuya, amman zanyi kokari kullum ina post in banyi ba to kumin uzuri ban samu lokaci bane na gode.

200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.

#NWA
#KTG
[4/26, 8:42 PM] Rabi: BEBE'ARTH

Wattpad@Rashuna

®️NAGARTA WRI.ASOCIATION

KATANGA...

In baki siya ba ya kamata ki mallaki naki a hannu kar garab'asar ta wuce ki, in na gama free page zaki siyeshi akan 300 ne,kuma in kin siya yanzu zaki samu damar karanta CIN AMANA kyauta, kada ku bari wannan garabasar ta wuceku, kada ku manta akwai abin amfani a ciki.

Masu tambayata document in na gama, shi kuma zaku sameshi akan 500kacal.

...............18’
"Likita"
Nusrat ta fad'i haka tana shan gabansa wanda hakan ya bawa Yusra damar bacewa daga gurin kamar walk'iya.
"So muke a sallamemu."
Ta fad'i hakan tana d'age nik'af in fuskarta domin ya shaidata.
"In lokacin sallamar yayi ai zan sallameku ba sai kun bukaci hakan ba."
"To ai asibitin naku ne yayi tsauri da yawa ance babu masu jinya sannan kuma yanzu an hanamu shiga muga mahaifinmu, ai abin baiyi tsari ba sam wallahi."
"Ke yarinya ce baza ki gane abinda muke nufi ba, amman zamuyi magana da d'aya namijin."
Ya fad'i haka yana neman barin gurin yayin da Nusrat tayi saurin shan gabansa.
"Nifa bazan bar asibitin nan ba sai naga mahaifina wallahi."
"K'warai kuwa Yayarmu, mu da mahaifinmu ai mana k'arfa k'arfan hanamu ganinsa, bayan duk ga sauran d'akunan marasa lafiyan ana ta shige da fice sai mu za'a hana shiga."
Cewar Yusra da ta nufo gurin da suke a tsaye.
"Mahaifinku yana buk'atar hutawa sosai, wannan dalilinne yasa muka hana kowa ganinshi, da wani yare kuke so nai muku ku fahimta ne?"
"Toh munji, amman yanzu muje tare muganshi sannan sai mu tafi." Suka fad'i hakan a kusan tare, ganin dai babu yadda zaiyi da su don Yusra har gefen rigarsa ta rik'e yace.
"To sakeni ku muje d'akin"
A ransa yana addu'ar Allah yasa Aasad yayi abinda zaiyi ya fita to sai kuma suna karya kwana suka ci karo da shi, don haka likitan yace su jirashi anan bara yaje ya daho, bai jira me zasu ce ba yabi bayan Aasad in.
Cikin muryar tashin hankali Aasad in yace.
"Likita akwai matsala"
"Bai mutu bane ko wanine ya ganka?"
"To ai in wani ne ma ya ganni da sauki don akwai hanyar da zan bi na aikashi lahira shima, ya gudu, baya cikin d'akin na duba ko ina da ina kaga takardar da ya bari akan gado"
INA NAN DAWOWA
Innalillahi likitan ya hau ambata bayan ya gama karanta takardar.
"Yanzu meye mafita, me zan cewa wa'yannan yaran su fahimta"
Ya zauna dab'as akan kujera yana jujjuya kansa ya rasa mafita guda d'aya gareshi.
"Kai ta abinda zaka cewa iyalinsa kake, ni kuma ta abinda zaije ya daho nake, don haka nayi alkawarin sai na binciko inda ya shiga a duk fad'in garin nan in kwa bai wasa ba sai na kashe dukkanin ahalinsa."
Yana kawowa nan ya fice daga ofis in yana banko k'ofar da k'arfi ta bada k'ara mai sauti, likita dai kulle kansa yayi a ciki don in ya fita baisan me zai gayawa wayancen yaran ba don ya tabbata sai sun tara masa mutane, musamman wacce ta rik'e gefen rigarsa don yaga alamun rigimammiya ce, su kuwa da suka gaji da tsaiwa sai Yusra cewa tayi.
"Yayarmu zo mu tafi ina jin dai likitannan wayo yayi mana ya gudu, tunda dai na samu na shiga na ganshi ai shikenan."
"Wai kayan wa kika saka ne?"
"Wallahi wata nurs ce ta bani, ina zuwa kuwa ba tambayar wani d'aki zan shiga tun da sun ganni da uniform, amman dai har yanzu ba ya magana yasa na mik'o masa biro da takarda da aka ajiye kan drowa yayi rubutu a jiki ya bani na baki."
Takai k'arshen maganar tana mik'o mata takaddar, karb'a tayi tana fad'ii.
"Mu tafi gidan, amman wallahi gobe duk bura'ubar da za'ayi sai dai ayi sai naga Babana."
Jinjina kai Yusra tayi, tunda suke bata tab'a jin Yayarsu tayi zagi ba sai yau, soyayyar Baba da Yayarsu daga Allah ne, sun kwana da sanin yafi k'aunarta a cikinsu kamar yadda Mama tafi k'aunar Shukhura sai dai b'oyewa da suke k'ok'arin yi.

Likita ya shiga mugun cakwakiya ya rasa yadda zaiyi, taya zaai ace paitent a cikin asibitin nan ya gudu?Dole sai 'yan uwansa sun tuhumesu kuma hakan zai tab'a kimar asibitin wanda ya tabbata Aashiq yaji bazai tab'a k'alewa ba kuma tabbas hakan zai iya sawa ya binciko abubuwa masu yawa da suka bunnesu, don haka kawai ya yanke shawarar zuwa mutuware, ya samo gawar da ba'a gane fuskarta kana yaje yayi report wa 'yan sanda bayan suma ya basu cin hanci me tsoka kana washe gari ya kirawo Baffa Shamsu akan yazo asibiti akwai matsala.

Tunda Amima ta shigo ta gaya musu cewar Baffa Shamsu ya tafi asibiti an kitashi akan akwai matsala Nusrat take zabga uwar gudawa mai azaba ta tashin hankali, gaba d'aya gidan kowa ba ya cikin nutsuwarsa,can bayan jimawa da tafiyarsa suka ji hayaniya ar mutane a waje, Nusrat ce ta zabura ta mik'e had'e da fad'in.
"Shi kenan sun kashe shi wallahi."
Dai dai nan Baffa Shamsu ya shigo, fuskarsa kawai ta kalla ta saki murmushin rashin mafita had'e da fad'in.
"Kun gani dama na fad'a wallahi sun kashe mini Babana."
Iya da Umma Baffa Shamsu yaja gefe yana gaya musu abinda ya faru k'asa k'asa.
"A yadda likitan da police sukamin bayani wai fitowa yayi da niyar guduwa daga asibitin shine su kuma suka bi bayansa a k'ok'arinsa na tsallaka titi mota tabi ta kansa,kuma sunce har yau basu gano dalilinsa na yunkurin guduwa ba, ga gawarsa can na shiga da ita can gida zan had'ata."
A tare Iya da Umma suka saki salati da gunjin kuka, hakan yasa Nusrat da ke ta k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da Mman Amima tayi mata na sai taje gurin da su Iya suke magana, fasuwar kukansu yasa ta samu amsar da take son zuwa juyowa, a hankali idanuwanta suka k'afe k'af numfashinta ya d'auke gaba d'aya."

A hankali idanuwanta suke washewa yana dad'e tariyo abinda ya sameta, cak idonta ya sauka jikin drowar dake gefen gadon da take a kwance, GOGEL HOSPITAL shine abinda ta gani a rubuce, firgicewa tayi hade da zabura ta mik'e tsaye tana me saukowa daga kan gado ta nufi hanyar waje, Sai a lokacin Mamn Amima da Yusra dake tare da ita suka lura suka biyo bayanta a hanzarce.
Sauri kawai take zubawa burinta ta fice daga cikin asibitin ba tare da wani ya dakatar da ita ba, karo kawai taji tayi da mutum, wanda shi kuma hakan yasa sandan dake rik'e a hannunsa fad'uwa sukayi baya kamar zasu kifa yaransa dake bayansa suka yo kansa yayi saurin dakatar da su da hannunsa ya rik'eta sosai yana me daidaita tsayuwarsa, ruk'unk'umeshi tayi tana sakin kukan dake cinta had'e da fad'in.
"Dan Allah na rok'eka ka fitar da ni daga cikin asibitinnan kashe mutane suke yi sun kashe mahaifina shine nima aka kawo ni su kashe ni "

Dago da kanta yayi yana me sauke lumsassun idanuwansa a kan fuskarta, kallon yadda hawayen ke sauka akan fuskarta suna zirarewa yake don ko d'igon hawaye baya tsayawa saboda santsin fatar da Allah ya huwace mata....

200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.

#NWA
#KTG
[4/26, 8:43 PM] Rabi: BEBE'ARTH

Wattpad@Rashuna

®️NAGARTA WRI.ASOCIATION

KATANGA...

In baki siya ba ya kamata ki mallaki naki a hannu kar garab'asar ta wuce ki, in na gama free page zaki siyeshi akan 300 ne,kuma in kin siya yanzu zaki samu damar karanta CIN AMANA kyauta, kada ku bari wannan garabasar ta wuceku, kada ku manta akwai abin amfani a ciki.

Masu tambayata document in na gama, shi kuma zaku sameshi akan 500kacal.

...............19
Chapter 34 · 0% Book details