← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 69

Sashe 65

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba sam bai ji dad'in abinda mahaifiyarsa da 'yan uwansa suka yiwa Nusrat ba,da ba don Allah ya jefota hannu na gari ba da shikenan sunyi silar gurb'acewar rayuwarta ko kuma ma a rasa wacce duniyar ta shiga,sun mata abinda shi bazai tab'a yiwa jininsu ba ko da kwa a yanzun ne,ko da kuma cikin shegen tayi da gaske. Khalil ne ya d'aukko su,bayan Nusrar ta sanarwa da Hajjaju zasu je can gidansu da Baba,shine Hajjajun tace tayi zamanta acan bayan lafawar komai za'ayi shagalin biki,sai azo a d'auketa,Aashiq kuwa tex ta tura masa ta waya,don rabon da ta ganshi tun a gurin taron,kuma tana jin nauyin zuwa inda yake tunda ba kaita a kayi ba,don haka ta share duk da so da k'aunar da zuciyarta take taga a wani hali yake,don d'azun taga yadda idanuwansa gaba d'aya suka jirkice,Suna shiga da Aunty Maryam suka ci karo a babban tsakar gida,ta d'an fito shan iska,fad'a sukayi da Daddy akan zai k'ara aure inda tayi tsallan bad'ake ta nuna bai isa ba,shikwa yace tayi kad'an ta hanasa aure,shine tayi zuciya ta had'o kayanta ta taho ita da Hidaya,Hibba kwa tace babu inda za taje tana tare da Daddynta Abbas kwa dama yabi bayan Abdul channai,dama haushinta Daddy yake ji don tun barin Nusrat gidan har yau ba su dawo dai dai ba,kawai yana danne zuciyarsa ne,RJ yasha matuk'ar wuya kafin ya samu ya saba da rashin Nusrat,Hajiyan Rj d'in kuwa babu lallamin da ba tayiwa Daddy ba akan ya hak'ura ayi bikin Rj d'in da Hidaya amman sam ya k'i yace a barta ta d'an d'ana yadda ta sanya zuk'atansu suma,a can gurin aikinsu Zulaihat ta mak'ale masa,nacin yau da ban na gobe da ban,kuma ya riga ya fito fili ya gaya mata gaskiyar bai jin zuciyarsa za ta numfasawa wata mace bayan Nusrat,amman tak'i rabuwa da shi ta bi ta kafe shi take so take auna,da matsawar Hajiya tayi masa yawa akan aure kawai sai ya hak'ura ya sallamawa Zulaiha,amman da sharad'in duk ranar da Nusrat ta bayyana zai aureta domin itace Muradin ransa,tace taji ta yadda ta kuma aminta inda aka sha bikinsu,Hidaya ta kuma saddak'arwar ta rasa RJ har abada kamar yadda tayi sanadiyar rasa junansu da sukayi,sai dai tasan cewa da sonshi da k'aunarsa za ta mutu,tunda gashi ta kasa saurarar kowa,kuma an koreta daga makaranta sakamakon sharrin satar amsa da aka yi mata,anan nadama ta kuma shigarta sosai,yadda taji ciwon sharrin satar da aka yi mata ina ga Nusrat da suka yiwa sharrin zubar da ciki,ta tabbata alhakin tane yake yawo da rayuwarta,don gashi kamar k'ara mata son Rj ake ta kasa bawa kowa dama,har Daddy ya ibar mata kwanakin da in ba ta tsayar da miji ba zai bayar da ita sadaka,wannqn dalilin ne ma yasa da Mommy tace taxo su tafi zariya ta biyota,inda Daddy yayi hanza da su yaci gaba da shagalin auransa.

Wata iriyar zabura Aunty Maryam tayi da taga Baba,juyin da za tayi ta arci na kare tayi tun tub'e ta kifa akan hannunta aikwa ta saki k'arar tsurewa da ta azaba,Baba ya nufi gurinta yana. "Subhanallah,Maryam yi a hankula,nine dai ba wani kike gani ba." Girgiza mishi kai take tana jaa da baya,ta kasa magana ta kuma kasa tashi,Hidaya da taji k'arar Momyn tasu ta fito daga gurin Iya itama tayi tozali da Baba don ko da su Nusrat ba ta lura bata juya da gudu tana.
"Iya Baban su Yayarmu,Baban su Yayarmu ne a tsakar gida." "Ke ba na son rashin hankali,wanda ya mutu yana dawowa ne banda sokarci irin naki,sai dai in gizo yayi miki ko alj.." Maganar tata ka karewa tayi,yayin da tayi tozali da idon Baba ya shigo gurin da sallama, wani irin juyi tayi za ta koma d'aki sai ji kike k'umm ta k'ume da bango.
"Yi a hankali Iya nine ba gamo kikayi ba." Cewar Baba yana nufar gurin da take ai sai ta k'ara gigicewa ta nufi d'aki,sai dai ina,ai Hidaya ta rufe ta saka sakata,girgiza k'ofar Iya ta shiga yi tana. "Dan Allah kuyu hak'uri,tsautsayi da k'addara ne yasa na kori Nusrat daga gidan nan,wallahi yanzu na canja halina,na daina kwad'ayi da son abin duniya." kafin ta fara karanto duk addu'ar da tazo bakinta,tana sakin fitsari da gudawa a lokaci d'aya,jin ihun Iya yasa Umma fitowa da sauri don ganin abinda yake faruwa garin sauri ba ta kula da b'awon ayabar da taci ta hullar ba ai kwa tayi sufa k'afarta ta tale sai ji kika b'as aikwa ta saki K'arar azaba.

Aunty Maryam gocewar k'ashi tayi a hannunta,Umma kuwa karyewa tayi a cinyarta,Iya kuwa goshi yayi suntum abin tausai,har suma tayi kafin kuma su fahimci cewar Baban ne da gaske ba gamo sukayi ba,Yusra kuwa tasha dariya son ranta don babu wanda ya bata tausayi cikinsu,gaba d'ayansu babu wanda ya iya had'a ido da Baba,har Baffa Shamsu da ya shigo,matuk'ar kunya da nadamar da ba ta da amfani suke yi,kafin su shiga neman yafiya da duk abinda suka aikata,sun karb'i kuskuransu kuma suna fatan su gyara shi a nan gaba,ko bai gyaru gaba d'aya ba,yayin da Baba ya nuna musu babu komai,komai muk'addari ne daga Ubangiji,mutum bai isa ya sauya k'addarar da ke rubuce cikin littafin kowa ba face sai abin nan dai da alk'alami ya rubuta,suka nemi yafiyar Nusrat ma ta nuna babu wanda ta rik'e a ranta Hidaya kuwa kasa had'a ido tayi da Nusrat a hakan ta nemi yafiyarta,ta nuna mata babu komai ba ta rik'i kowa ba amman ba za ta manta da darasin da suka koya mata ba. Baba fad'a ya yiwa Aunty Maryam sosai da yaji dalilin zuwanta, inda yace a washe gari ta had'a kayanta ta bar gidan,to kuma sai ga Rj da Hibba sunzo washe garin, inda suka rankaya suka juya gaba d'aya,ta hak'ura ta saduda za taje ta rungumi k'addarar kishiyar da ta shigo rayuwarsu, Nusrat sun gaisa da Rj sun kuma tattauna bayan saduwa,kowa yaji abinda ya kasance da d'an uwansa bayan rabuwa,na jajantawa suka jajanta na murna suka taya juna murna,sai dai bai ji dad'in rasa Nusrat da yayi har abada ba,amman hakan bai hana yayi mata murnar auran da tayi ba,musamman da yasan wanda ta aura mutumin kirki ne na bugawa a jarida,ta riga kam ta gama dacewa,kamar yadda yake da yak'inin samun Nusrat d'in da Aashiq ya dace cikin masu dacewa. Hibba tayi murna sosai da ganin Nusrat da Yusra,don ta so ta zauna amman saboda makaranta babu yadda za tayi...
[6/29, 7:42 PM] Rabi: 52
Kasancewar ba wani bincike za'ayi ba dukkan wasu shaidu da hujja suna hannu kuma dukkaninsu sun amsa laifinsu ba wata doguwar shari'a akayi ba aka yankewa kowa hukunci dai dai da abinda ya aikata,an kamo wa'yanda suka kashe Baffan Aashiq da wa'yanda suka kashe Falisha an yanke musu hukunci kisa ta hanyar rataya,Baffa da Baffa k'arami da Aasad d'aurin rai da rai,Mami ma kisa ta hanyar rataya,likita kuwa shekara goma gidan kaso,bayan an koreshi daga aiki,yadda ko nan gaba ba za'a kuma d'aukarsa a wani guri ba.
Rayuka gaba d'aya babu dad'i,don kuka sosai sukeyi yayin da 'yan sanda suka kad'a kawunansu za'a fita da su,kuka sykeyi na tarin nadama,nadamar da ta riga tazo musu ak'urarran lokaci,musamman Mami ita da ratayeta za'ayi haka 'ya'yanta da 'yan uwanta suka rungumeta suna kuka itama tana yi tana kaico da zuciyar da ta bata shawarar da ta aikata hakan,tana jin inama baya za ta dawo ta samu damar gyara kuskuranta sai dai ba za ta tab'a dawowa ba idan ta wuce ta riga da ta wuce har abada,babu wanda ya isa ya juyo da ita. Aashiq bai so 'yan sanda suka shigo cikin lamarin ba,da yasan haka abin zai kwab'e tabbas da bai bari an kama Aasad ba,don silar kama shine hakan ta faru,ya riga ya yafe musu gaba d'aya babu wanda ya rik'e a ransa, da saka hannunsu ko babu idan Allah ya tsaro rayuwarsa haka za ta kasance bai isa ya sauya hakan ba, iya abinda yake rubuce cikin k'addarar rayuwarsa iya abinda zai samesa,masoyi ko mak'iyi babu wanda zai sauya masa komai sai abinda Allah ya zartar a kansa,dama can haka Allah ya tsaro rayuwarsa zata kasance tun fil azal,shiyasa yake ta tausar Asghar da yabi ya sanyawa ransa damuwa,shi da Hajja,ba zab'insu bane Baffan ya kasance haka ba,su godewa Ubangiji ma da suna da damar ziyartarsa a duk sanda suka so,ba kisan gilla za'a masa kamar Mami ba,kuma yana da damar da zai gyara tsakaninsa da Ubangijinsa,da kuma yafiyar wa'yanda duk ya b'atawa ma. Hajjaju ganin rayuka duk babu dad'i kowa yana jimamin abinda ya faru,kawai sai ta fasa shagalin bikin da tace daa za'ayi ta tura gidan su Nusrat,suyi walimarsu washe gari za'a zo d'aukar amarya,don taga alamun Aashiq d'in shi kansa yana buk'atar matarsa,duk da ba zuwa yayi ya gaya mata ba amman ta tabbata yana son kasancewar wani kusa da shi a halin da yake jin zuciyarsa kawai yana sharewa ne da mazewa,kamar yadda kwa tace d'in anyi walima a gidan su Nusrat,an d'an tara mutane ba laifi,don kowa ya san da auran nata,Hidaya da Hibba sunzo,har da matar RJ,Aunty Maryam babu dama ana can da hannu ya kuma suntumewa,gashi washe gari tarewar kishiyarta,walima ta k'ayatar,da daddare kuma aka zo d'aukar amarya,bayan tasha nasihu nasu ratsa jiki a a gurin Baba kana aka wuce da ita.
Chapter 65 · 0% Book details