← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 69

Sashe 63

Katanga Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sai dai Asghar yana zuwa ya tarar da Nusrat d'in babu lafiya,don haka ya koma ya gayawa Malam d'in yace su barwa gobe idan Allah ya bata lafiya...
[6/26, 12:11 AM] Rabi: 50
Aashiq gadin Nusrat ya zauna yi,mintina kad'an ya lek'a k'irjinta ya tabbatar da tana numfashi,sallah ce kawai ke tashinsa,yana idarwa zai dawo gefenta ya zauna,sai da akayi sallar isha kana ya tashi zuwa kicin ya dafo black tea insa na k'aida ya dawo d'akin ya zauna yana sha, mutsu mutsu yaga Nusrat tana yi sai ya ajiye tea in akan drowar gado ya haura kan gadon yana janye bargon dake jikinta,gumi yaga tana had'awa sosai alamun zazzab'in ya sauka,remort d'in Ac ya d'auka ya k'ure k'arfinta,a firgice ta farka tana wani irin kuka tana kiran sunan Yusra,jijjigata yayi yana kiran sunanta,amman tak'i sauraransa idonta a rintse yake tana kiran sunan Yusra,ganin yayi yayi ta saurareshi tak'i yasa ya d'auki wayarsa ya kira wayar Yusran kusan sau hud'u tak'i shiga, sai ya kira Khalil yace yaje can gidan Hajjaju ya taho masa da Yusra,kafin yaci gaba da rarrashinta,ya samu tayi shiru cikin jikinsa tana ta sauke ajiyar zuciya.
Khalil da yaje neman Yusra aka sanar masa ba ta nan,har Farida na cewa tayi tunanin ma Yusran ta dawo suna tare da Nusrat d'in,jin hakan da Khalil yayi sai ya kira wayar Aashiq ya gaya masa,shi kuma sai yace yaje can gidan Kawu Iliya ya dubo,can ma dai da yaje Aunty Hafsa ta sanar masa Yusran tana nan estate d'in,da ya kira Aashiq ya gaya masa sai lamarin ya d'aure masa kai ainun,to ko dai wani abu ne ya samu Yusran shi yasa Nisrat d'in take irin wannan kukan?Gashi bacci ya kuma d'aukar Nusrat d'in bare ya tambayeta,sai ya kira wayar Asghar yake tambayarsa abinda ya faru,sai Asghar yace ya fito falo suyi maganar da yake shigowarsu cikin gidan kenan shi da Ramla,sai Ramlan ta shige bedroom inta d'auke da 'yan biyu ta bar Asghar d'in yana jiran fitowar Aashiq.
"Nayi tunanin ko ta gaya maka abinda ya faru,don a gigice naga ta fito daga asibitin,wanda nima tunanina wani abin zai iya samunta a asibitin,shiyasa Yusra tana gayan suna can na tafi d'aukosu."
"Ba ta gaya mini komai ba,banda sunan Yusra babu abinda take fad'i,kuma na kira wayar Yusran ba ta shiga,na saka aje a taho da ita,duk inda ake tunanin samunta ba ta nan,dama ba tare kuka dawo ba?" "Babu ita suka fito daga asibitin,da na kira wayarta kuma sai tace na bawa Nusrat,to bansan me ta cewa Nusrat d'in ba,amman naga takuma firgicewa,da na tambayeta sai cewa tayi,Yusran tace muje ta taho."
"Mtssss,Asghar jikina yana bani akwai matsala."
"Ni kaina ina jin hakan,hankalina bai kwanta da wayar da sukayi da Yusra ba,amman kamar wayarka tana nad'ar sautin magana ko?" "Anyi haka,bara na d'auko a duba." Ya nufi bedroom in ya d'auko ya kawo masa shi kuma ya shiga bin binkitawa,ya shiga wannan yaji ba maganar bace ya shiga wannan a haka har suka samu abinda suke so, muryar Aasad rangad'a d'au ta fito da abinda yacewa Nusrat. "Biri yayi kama da mutum,ina zarginsa sosai a kanka,tunda na tab'a jinsa yana waya akan a kashe Malam,nasan akwai wata munak'isa da yake shirya maka,abinda ya dakatar da ni a kansa,saboda Malam bai gaya mini dalilin da yasa suke neman kasheshi ba,kai kuma ban san ta ina zan fuskantar dakai ka fuskanta ba,abin tashin hankalin kuma ba mu san me Nusrat d'in taji ba,ga kuma Yusra da rayuwarta ke cikin had'ari."
Dukkaninsu shiru sukayi ko wanne da tunanin da yake sak'awa a ransa,kafin Asghar ya tashi ya fita daga cikin gidan,bai jin ko ya bud'e bakinsa zai iya yin magana a halin da yake jin zuciyarsa,yana kallo Asghar d'in ya fice ba tare da ko tambayarsa inda zashi yayi ba.

Ya kwana da sanin tun bayan mutuwar Alisha Aasad baya kwana cikin estate d'in nan,bai damu da sanin inda yake kwana ba saboda yasan yana sharholiyarsa da 'yan mata,kuma ba wani shiri suka cika yi ba yawancin had'uwarsu da fad'a suke rabuwa,saboda kowa ya gano inda yasa gaba akan Aashiq, ya tabbata duk inda Aasad yake a yanzu can yakai Yusra,don haka ya saka akayi tracking numbersa,ya d'ebi 'yan sanda suka nufi can,me gadin gidan nasa suka saka yayi nocking,da yaji muryar me gadin bayan ya tambayi waye sai ya bud'e kai tsaye don a tunaninsa ko wani abu ne ya faru me gadin yazo sanar masa,daga shi sai gajeran wando ya fito,ganin 'yan sanda suna nuna shi da bindiga sai yasha jinin jikinsa amman ya maze yace."Lafiya?" "Lafiyarce ta kawomu." Cewar Asghar yana fitowa daga bayan 'yan sandan da ya tsaya,kafin ya basu umarnin su kama shi."Me nayi?" Ya fara fad'e yana fus fusgewa,Asghar da wani d'an sandan suka sa kansu cikin gidan,dai dai fitowar Baby daga ita sai tawul,taji Asghar d'in shiru shine ta biyo bayansa,tana ganin d'an sanda ta arci na kare ta koma had'e da datso k'ofa,d'aki d'aki suka duba a d'akin k'arshe suka sameta,marabarta da gawa numfashinta da ke kai kawo a k'irjinta,don har lokacin abinda ya shak'a mata bai saketa ba,Asghar ne ya d'aukota yana k'arewa innocent face inta kallo,jallabiya d'an sandan ya gani kan kujera ya d'aukowa Aasad suka fito,aka bashi ya saka rigar,yana sakawa yana kallon Asghar yana k'wafa. "Wallahi sai kayi da na sani,domin kama ni yana nufin tono abubuwa da dama tonowar da baza tayi maka dad'i ba,zaka ga abinda zatonka bai tab'a baka ba,kuma na tabbata hakan sai yafi tab'aka sama da kowa." Asghar bai kulashi ba,don ya d'au maganarsa a zafin tonuwar asirinsa da bai tab'a zata ba.

Dr Sa'ad ya kira ya duba Yusra ya tabbatar da lafiyarta k'alau,abinda ya shek'a mata ne yafi k'arfin jininta zai saketa insha Allah nan da safiya,Nusrat ta farka a lokacin sai taji ta samu nutsuwar zuciya,tasan ba kowa ne da wannan aikin ba sai Asghar,yayin da ta shiga yi masa godiya domin rayuwarta ya ceta ba ta Yusra ba,daga Asghar har Aashiq d'in babu wanda ya mata tambayar abinda taji,shi Aashiq bai shiryawa ji ba yayin da Asghar ya barwa zuwa safiya.
Wanka tayi ta gyara jikinta,sai a lokacin taji wata mitsiyaciyar yunwa,Aashiq ba ya d'akin yana can falo tare da Asghar da ya saka Ramla sama musu sassauk'an abinci don daga shi har Aashiq d'in baijin akwai wanda ya d'orawa harshensa wani abu a wunin yau,wanda ya tabbata kwana a hakan zai basu matsala,shirya kanta tayi cikin doguwar rigar baccin da iya kacinta guiwarta,sai dai ba me nuna tsiraici bace shiyasa ta daure ta sakata saboda rashin abinda za ta saka d'in,bud'e k'ofar tayi ta lek'o sai ta hango su tare da Asghar sai ta koma,don baza ta iya fita a haka ba,ko shi kad'ai d'in za taji nauyin ya ganta a haka,sai dai kawai don ba yadda za tayi,d'an buga k'ofar tayi,yana jin haka ya taso ya nufo bedroom d'in.
"Yunwa" Ta fad'a tana dak'una fuska idonta cikin nasa,lumshe idanuwansa yayi ya kuma bud'esu a kanta,kafin ya juya ya fita,hijabi ya anso mata gun Ramla har k'asa,ta saka ta fito,yace taje kicin ta taya Ramlan,don zai so cin wani abu da ya fito daga hannunta.
Ta murzu sosai a gurinsa don ya kasa hak'uri sai da ya rage zafi da ita,a tunaninsa idan ya jita cikin jikinsa zai iya samun bacci amman ina,yadda take manna k'irjinta a nasa tana mimmik'ewa duk a cikin bacci yafi komai kunnashi,kunnawar da babu abin kashewa,don haka ya hanata baccin sai da ya rage zafi tukunna suka samu sukai bacci, ko ina na jikinta yana rad'ad'i musamman lab'b'anta da k'irjinta,don baiyi musu rik'o na wasa ba,sun murzu iya murzuwa,musamman yadda dama tsakaninsa da su kallo ne ya dad'e yana kwatanta yadda laushi da santsinsu zai kasance a hannusa,bai tab'a tunanin hannunsa zai sauka a kai ba don bai gano yuyuwar aure tsakaninsu ba.
Chapter 63 · 0% Book details