← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 69

Sashe 43

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata sanyayyar soyayya ce ta fara gudana tsakanin Nusrat da Rj wacce sam Mommy ba ta ankara da ita ba saboda ba kasafai take sakkowa k'asa ba, tana da komai na buk'ata a cikin d'akinta, abinci kuwa Nusrat ce ke kai mata ta kuma sakko da kwanukan, sai yamma take sakkowa ta koma sashen daddy saboda tararsa shine sai a had'u ayi dinner tare, yanzu kuwa da Daddy ba ya nan dinner ma ba ta sakkowa a d'akinta take wuni sir abinta tana karatun novel idan 'yayan suna bukatarta sai suje gareta, duk da babu wata shak'uwa tsakaninsu saboda ba ta ginosu akan haka ba.

Tafiya ce ta kama Daddy dalilin da yasa kenan Rj bai tare shi da maganar soyayyarsa da Nusrat ba ya bari ya dawo tukunna in yaso sai ya sameshi da maganar don ba ya fatan shi ya rigashi yi masa maganar Hidaya don bazai iya kaucewa hakan ba, sannan kuma a yadda yake jin soyayyar Nusrat bazai tab'a iya kwatanta rayuwa babu ita ba yana jin kawai sai dai ya had'asu su biyun ya aura idan hakan ta faru.

Ko da wasa bai tab'a bari Nusrat in tasan da maganar aure tsakaninsa da Hidaya ba don yasan muddun ta san hakan tabbas za ta ja jiki da shi, haka ma Hidayan sam bai nuna mata yasan abinda take nufi da shi ba duk kwa na k'okarinta gurin nuna mishi irin tarin soyayyar da take masa sai ya dinga kakkauce mata yana nuna mata shi sam bai gane me take nufi ba Nusrat itace zab'in zuciyarsa.

Tsakanin Hidaya da Nusrat kuwa babu abinda ya canja, don Hidaya tana k'okari gurin danne zafin Nusrat in da take ji saboda zumunci, amman dai ba ta fasa cusa Ishaq cikin rayuwar Nusrat in ba saboda ta bar mata Rj dinta don a yanzu tayi amannar muddun Nusrat na nan ba ta ishi Rj kallo ba indai a barin soyayya ne, don haka ta d'au alkawarin sai tayi silar da Nusrat za ta auri Ishaq ko da ba ta so ta hakanne itama za ta samu muradinta, shiyasa ta k'agu Daddy ya dawo domin ta fara shirinta.

Nusrat kuwa gaba d'aya ta gama karantar Hidayan tsaf son Rj take, wanda shima Rj in ta lura yasan da hakan kawai yana kakkauce mata ne, Allah ya gani tana son Rj so ba na wasa ba shima kuma yana sonta wannan dalilin ne yasa ta biye mishi suke soyayyarsu amman fa can k'asan ranta tsoro ne fal cikinsa musamman sanda Rj in ya rarraba musu tsaraba ita har da tanfatsetsiyar waya ya bata wacce ya siyo mata ita ta musamman to da taje nunawa Momy sai ce mata tayi.

‘’ Ki dai tsaya matsayinki banda shishshigin shiga hurumin da ba naki ba domin ba dake ya kamata ba, idan kuma kinki ji duk abinda ya biyo baya babu ruwana."

To wannan ne yake sawa wani zubin duk sai ta sare tana hango tafiyarsu da Rj in babu inda zata je wanda hakan itakam bazai shafa mata lafiya ba, duk da Rj in yakan kwantar mata da hankalin Daddy yana dawowa zai sameshi da maganar auransu don ba lokaci yake so a jaa, to idan tayi laakari da sauk'in kan Daddyn wanda tayi amannar bazai hanashi auranta ba sai taji hankalinta yana d'an kwanciya.

Wata d'aya Daddy yayi ya dawo wanda yazo ya tadda familyn nasa cikin murna da d'aukin dawowarsa sai ya alakanta hakan akan bai tab'a yin kwanaki irin haka ba idan tafiya ta sameshi.
A daren da Daddy ya dawo Hidaya ta d'au wayar Nusrat tayiwa Ishaq tex akan ta amince da shi gobe ya turo magabatansa gidansu sak'o inji Daddy, sai da ta tabbatar ya shiga kana ta goge ta saka number tasa a black list kana ta ajiye mata wayar cike da zallar farin ciki tana ganin tarkonta kamar ya gama danuwa.

Ishaq da yaga message in Nusrat ya shiga matuk'ar farin ciki duk da kasan ransa yana mamakin anya kwa Nusrat ce tayi mishi wannan tex in don sun riga sunyi sallama ya daina kiranta ma don ta sanar mishi wanda za ta aura ya dawo kuma ba ya son muamalarsu don haka sai yayi mata fatan alkhairi yazo ya fara jinyar cire soyayyarta a ransa don yanzu yayi amannar ya rasata kenan har abada sai kuma gashi tex inta ya riskeshi a yau don gaka baiyi k'asa a guiwar danna mata kira ba amman sam tak'i shiga don haka sai ya juya akalar kirannasa ga number Hidaya.

Gaisawa sukayi bayan nan ya buk'aci ta had'ashi da Nusrat tace masa tayi bacci da yake kanta na mata ciwo, nuna rashin jin dadin ciwon kan nata yayi kafin ya tambayeta game da tex in da Nusrat in ta turo masa, nan ta k'ara masa k'arfin guiwa had'e da tabbatar masa gaskiya Nusrat in ta fad'a don gobe ma an shirya tarb'arsu.
Cikin zallar farin ciki Ishaq yajishi yana yawo don haka a wannan dare yaje ya samu mahaifinshi ya gaya mishi, sai dai mahaifin nashi yace zasuje amman tambaya kawai zasu yi sai anyi bincike kafin su kai kud'i.

Hidaya suna gama waya da Ishaq tayi tsalle ta dire don ita kad'aice a dakin Nusrat ba ta shigo ba suna can tare da Rj, Hijabi ta saka ta nufi sashen Daddy, shi kadai ta tarar a kishingide yana cin tufa yana kallon tsofaffin fina finan indiya a cumpuiter insa.

"Daddy Nusrat ce ta aiko ni."

"To ina jinki."
Yace mata yana gutsirar tufarsa.

"Dama manema auranta ne suka ce zasu zo gobe, shine tace kunyarka take ji ni nazo na gaya maka."
"Wannan yaron da yake zuwa gurinta?"
"Eh shine Daddy"

"To masha Allah, Allah ya nuna mana goben ya kawosu lafiya, amman me yasa momynku ba ta sameni da maganar ba?

"Amin Daddy, ai itama ba ta sani ba yanzu in na fita daga nan zanje na shaida mata, kunyar Nusrat ce tayi yawa.
"Ni na shaida hakan, Allah yayi muku albarka gaba d'aya, in kinje ki turon Momyn taku da alama yau ta manta da ni."

" Amin, tom zan turota."
Daga haka ta fice daga sashen cike da zallar farin ciki, a kwance ta tarar da Mommyn tasu tana karatun novel, wani littafi take karantawa K'addar rayuwarmu, ya d'auki hankalinta sosai ko d'auke idonta daga kan wayar ba ta son yi shiyasa ba tajewa Daddy ba don ta san bazai barta tab'a wayar ba musamman da yau ya dawo daga tafiya kuma tana son jin k'arshen littafin shiyasa ta bari in ta gama sai ta tafi gaba d'aya.

Idonta akan wayar ta amsa sallamar Hidayan, gefen gadon ta samu ta zauna tana sauke idonta kan mahaifiyar tasu da babu ruwanta da lura da damuwoyinsu myddun in ba sune suka zo suka gaya mata ba.
"Mommy magana nake so muyi."
Ta fad'i hakan da sanyi a muryarta, haka kawai sai taji tana son bawa 'yar tata hankalinta don haka sai ta ajiye wayar tamik'e zaune tana sauke idonta akan Hidayan kafin Hidayan tace.

"Momy kince akwai maganar aure tsakanina da Yaa Rj amman shi Nusrat yake so, yanzu haka ma soyayyarsu suke sha abunsu, ni kuma Mommy ina mugun sonshi soyayyar da tayi mini muguwar illar da ban jin zan iya warkewa don haka naji bazan iya barwa Nusrat Yaa Rj ba don na fita buk'atarshi shiyasa nayi amfani da Ishaq saurayinta don ya aureta na samu ta bar mini muradina don idan soyayyarsu taje kunnen Daddy zai aura mata shine ni kuma sai dai sonshi yayi ajalina."
[4/26, 8:46 PM] Rabi: BEBE'ARTH

KTG30

Shiru Mommy tayi zuciyarta na wani irin tafarfasa, tun da tazo ta nuna mata irin kayan da ya bata ta fara zargin wani abu tsakaninsu duba da shakuwarsu tun kafin tafiyarsa makaranta dalilin da yasa kenan tayi mata gargad'i gargad'in da ba taji ba kenan.

"Me yasa tunda kika fahimci suna soyayyar ba kizo kin gaya mini ba?"

Ta fad'i hakan tana sauke idonta akan Hidayan wacce gaba d'aya ta zama wata iri saboda rashin nutsuwa amman ta kasa ganin hakan wani irin b'acin rai taji yana taso mata zuciyarta tana zafi.

"Ay nayi tunanin kin sani, sai daga baya na lura,ba ma kisan abinda ke faruwa ba ."
Hidaya tace da ita haka.

"Jeki ki kira mini ita."
Ta fad'i hakan had'e da had'iye wani abu me d'aci a zuciyarta.

Kaya take sauyawa zuwa na bacci, tana yi tana sakin murmushin samun kwanciyar hankali, saboda rabuwarsu da Rj kenan yace mata gurin Daddy zaije ya sameshi da maganar auransu.

Murd'a kofar da Hidaya tayi ne yasata juyawa har lokacin da murmushi akan fuskarta.
"Kizo inji Mommy"
Hidaya tace da ita had'e da juyawa ta bar dakin.
Saukar maganar Hidayan tare suka zo mata da fad'uwar gaba, jiki a sanyaye ta d'auki hijabinta har k'asa ta sanya ta fice.

Tun da ta d'ora idonta akan fuskar Momyn taji gabanta ya fara dukan tara tara bama uku ba.
Guri ta samu a kasa ta zauna hade da fadin. "Gani Momy"
"Nusrat"
"Na'am" Ta fada da rawar murya.

"Watakan gargadin da nayi miki bai shiga jikinki ya zauna ba har sai da kika aikata abinda zuciya da ruhinki yake so ko, ban isa nayi miki katanga da shi ba saboda kin rainani kika tsallake kika janyo ra'ayinsa ke ga mara mutummci me kike tak'ama da shi ne?‘’

"Ba ke kika haifeshi ba."
Hidaya ta fad'a tana turo baki gaba, Nusrat kuwa k'asa tayi da kanta ba tare da tace komai ba tana saurarar yadda kirjinta yake bugu har ma da zuciyarta a yanzun.

"D'ago ki kalleni"
Momy tace da ita, a hankali ta cire kanta ta sauke idanuwanta kan Mommy wanda suka d'an sauya kala hade da girkicewa.
"Kina tak'ama don bani na haifi Rj ba shiyasa kika tsallake maganata?"

girgiza kai tayi hade da fadin "Kiyi hakuri."
"Hmmm babu wani hak'uri da zanyi sai dai ki karb'i hukuncinki a yanzu, duk da bani na haifi Rj ba amman na haramta aure tsakaninku, kinga matarshi nan wacce akayi mishi tanadinta jira ake kawai ta gama karatunta amman kikazo kina cusa kanki gareshi har sai da kika sauya mishi tunani gaba daya saboda na dauko rayuwarki daga talauci na tsundumoki cikin daula."
Chapter 43 · 0% Book details