← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 69

Sashe 30

Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iya, Umma, Mmn Amima (Matar Baffa Shamsu)suka zo duba Mama a motar Baffa Shamsu, shi ya kawo su ma, sam basui tsamnanin zuwansu ba tun da har yau kwanansu biyu da zuwa, su na shirin tafiya sai ga su Shukhura nan suka koma suka zauna ana ta gaishe gaishe, Iya sai shishshigewa H Inna take, Shukhura kuwa gefen Mama taje ta zauna suna dad'a gaisawa, daga d'aya gefen Maman Nusrat ce ta sunkui da kanta k'asa tana wasa da gefen hijabin Yusra da tayi matashi da cinyarta tana bacci cikin sanyin murya ta ambaci sunanta.
‘’Yayarmu‘’
'Dago kanta tayi wanda suka cika da ruwan hawaye tana kallon Shukhuran, to itama Shukhuran nan da nan nata idon ya kaho ruwa, Baffa Shamsu ne ya lek'o yayiwa su Umma magana akan su yake jira don haka sukayi musu sallama suka fita, Hajiya Suwaiba ma sallamar sukai musu ta ajiyewa Mama dubu ashirin a sayi magani da ita, Mama ta dinga godiya to Mustapha ma dubu hamsin ya bawa Nusrat a hannunta ta rik'e ko wani abu zai taso suka tafi suka bar Shukhuran sai dare zaizo ya d'auketa.

Hira sosai aka sha tsakanin Mama da tagwayen yaran nata wanda yawanci kalaman Maman kamar nasiha take musu akan su rik'i junansu suci gaba da gina katangar da ta gino musu tun a yarinta, ta had'e hannuwansu duka su ukun ta kalli Nusrat tace.
‘’ Yayarsu kece babba kimin alk'awarin kula da rayuwar k'annenki baza ki bari sui kuka ba, zaki zame musu katangar da zasu jingina da ita.‘’
‘’Na miki alkawari Mama, amman me yasa kike irin wa'yannan maganganun?‘’
Me makon ta bata amsa kawai sai tayi murmushi ta kalli su Shukhura.
‘’Ku mini alk'awarin mayar da yayarku tamkar mahaifiyarku, ku gaya mata damuwarku ni na tabbata za ta share muku hawaye don baku da tamkarta.‘’
‘’Mun miki Mama‘’
Suka had'a baki ita da Yusra gurin fad'a
‘’Masha Allah, ku rik'e zumunci, ku rik'e mahaifinku, da 'yar uwarku Nimha, Yayarsu ki had'a kawunanku kuyi zumunci sosai, kar ku rik'e abinda wani yayi muku kuk'i zumunci da shi, kuyi zumunci da shi domin Allah ba don halinshi ba.
‘’Mama kina tayar mana da hankali, kalamanki kamar wasiyya kike yi mana.‘’
‘’In wasiyar ce ma na gode Allah Shukhura da ya bani damar yi muku,ita mutuwa rigace a jikin kowa,dama haka yake ko na rigaku tafiya ko ku rigani, fatana idan ta Allah ta kasance gareni ku rik'e junanku ku kuma rik'e zumunci ku d'auki jimirin yi mini addua to zan kwanta a kabarina cikin salama.‘’

Dukkaninsu shiru sukai ko wanne da abinda yake sak'awa a ransa, amman har lokacin hannunsu a dunk'ule yake har na Maman tana binsu d'aya bayan d'aya da kallo.

Hankalin Umma in yayi dubu ya tashi, ita da boka yace muddun Shukhura ta kwana a gadon nan ta musu Katanga da 'yan uwanta to ya hakan bai faru ba, dole ta koma gurin bokan nan, kuma tana son ma dangin mijin nata ta mallakesu suma su dingai mata kallon babar Shukhuran, yanzu tana ji tana gani ji kud'in da sirikar Shukhuran ta ajiyewa Mama, shima Mustaphan wa yasan adadin nawa ya bawa Nusrat in,don haka ta yanke gobe da sassafe can gurin bokan nata za tayiwa tsinkayi.

~WASHE GARI~
Ta gurfana gaban boka kamar wacce ke shirin yi masa sujjada, bayan ta gama zayyana masa abinda ke tafe da ita.
‘’ Kin fiya gaggawa in baki wasa ba aljani bela zai fatattaki aikinki gaba d'aya daga nan gurin.‘’
Cikin rawar murya Umma tace.
‘’ Allah ya huci zuciyar aljani bela, na tuba kaina bisa wuya, idan aiki ya kammala na maka alk'awarin dubu d'ari biyar.‘’
‘’Aljani Bela yaji dad'in kyautar da kikai masa don haka yace ki koma gida ki kwantar da hankalinki, kina zaune zakiga al'amura suna canzuwa hatta sirikan nata sai sun dawo gurfana miki.‘’
‘’Godiya nake, godiya nake aljani Bela.‘’
Ta fad'i hakan tana barin gurin da baya da baya.....

200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.

#NWA
#KTG
[4/26, 8:42 PM] Rabi: BEBE'ARTH

Wattpad@Rashuna

KATANGA...

...............14

Rashin zuwan Baba sosai yake damun Mama amman ba ta fito ta gaya musu ba, amman abin yana mugun bata mamaki ainun,amman duk da hakan ta nayi mishi uzuri may be wani abu ne ya hana shi zuwa, amman yau tabbas za ta saka Nusrat ta kira mata shi, don tana son su gana kafin ta Allah ta kasance a kanta, don wannan ciwon nata ba ta jin na tashi ne, da mugun zazzab'i ta kwana, sai da gari ya d'an sha sannan ya sauka gashi yanzu ma tana jin alamun dawowarsa, kallon Nusrat tayi tace.
‘’ Yayarsu yau in kinje gida kicewa Babanku yazo ina son ganinsa .‘’
‘’Tom insha Allah zan gaya masa, jikinne naji muryarki wani iri?‘’
‘'Zazzab'in ne yake son dawo mini kin sanshi da naci'’
'‘Sannu, insha Allah ma bazai dawo ba, ni wallahi har ina saka ran sallama ma da naga jiya jikin naki yayi kyau'’
‘’Wallahi nima haka Yayarmu, har na fara murna zaman asibitin nan sam ba dad'i‘’Cewar Yusra.
‘’Zaman asibiti ina yaga dad'i ai sai dole sai kuma ta kama ka, bari naje gida yanzu don na dawo da wuri, ki kula da Maman.‘’
‘’Tom shikenan sai kin dawo, ki tahon da wani kayan na sauya wannan.‘’ ‘’Tom‘’
Kafin ta matsa jikin gadon tace.
‘’Mama na tafi‘’
‘’Tohm sai kin dawo, kar ki manta ki kirawo mini Baban naku.‘’
‘’Insha Allah, na san bai fita ba ma tun da yanzu goma tayi.‘’ Tana kawowa nan ta saka kai ta fice.

Ta kwa samu Baban a gida, d'akinsa ta fara shiga suka gaisa kana ya tambayeta jikin Maman tace ‘’Da sauk'i, tace ma in ka samu dama kaje tana son magana da kai.‘’
Shiru yayi kamar bazai ce komai ba daga bisani ta numfasa yace.
‘’Na rasa me yake damuna ne wallahi, sam bana jin dad'in jikina in zauna inyi rubutu ma in sha abin ya gagara amman bara ki gani‘’
daga haka ya nufi ma'ajiyarsa ya lalibo wata takadda, ya d'auko alk'alami da tawada da allo ya mik'o mata.
‘’Ungo maza rubuta mini ita yanzun nan na sha. ‘’
Karb'a tayi had'e da amsa mishi da ‘’To‘’Kafin ta gyara ta fara rubutun, to da yake tana da saurin rubutun sai nan da nan ta gama ta wanke masa, ya karb'a yayi bismilllah ya shanye tas yayi hamdala.
‘’Ki tafi da takaddar ki ajiye a gurinki, in kin samu lokaci ki dinga rubutawa insha Allahu ba dai mutum yayi tasiri a kanki ba.‘’
‘'Tohm na gode '’
Cikin hanzari tayi duk abinda za tayi ta koma asibitin tana zuwa ta tarar da jikin Maman sosai ya rincab'e likitoci ne ma a kanta, Yusra na gefe tana kuka.

Likitan ne ya juyo ya kalli Yusra yace.
‘'Ina me jinyar nata?‘’
Kafin Yusran tace wani abu Nusrat tayi saurin cewa. ‘’Gani nan‘’ had’e da shigowa ciki.
‘’Ana buk'atar jini da hanzari, don zazzab'in ya k'one mata jini.‘’ Cikin tashin hankali Nusrat tace da shi.
‘’To a ina zan samo jinin?‘’

‘’Baza kije ki tambaya ba ko ni kike so na rakaki?‘’
Yace mata a kausashe, girgiza masa kai tayi had'e da ficewa da hanzari k'walla na taruwa a idanuntaa, da tambaya ta samu ta isa d'akin da ake sayar da jinin, tana zuwa suka tambayeta wani gruop za'a bata, sai a sannan ta tuna shaf ta manta jininma kala kala ne baki na rawa tace musu bara ta koma ta tambayo, har da gudu gudu ta had'a tana haki tana tambayar likitan kafin ya gaya mata sai da ya balbaleta da masifa.
‘’Ke wata irin dak'ik'iya ce tun kan ki tafi ya kamata ki tambaya, idan kika jaho ta rasu ai bani nayi asara ba , kice 'O' zasu baki.‘’
‘Ai ba ta bari ya rufe bakinsa ba ta kwasa da gudu ta na ayyanawa a ranta da Shukhura ce sai dai su d'ebi 'yan kallo da likitan nan, don taga alamun tijararre ne tun zuwansu ake fad'arsa har ba'a so dutynsa ya kama itama taso kafin zuwansa an sallamesu don ba ta son hayaniya.

Sai da ta koma ta kuma tuna ba ta tambayeshi guda nawa ba, kawai ta amso leda biyu ta juyo, tana zuwa ya ansa yana b'alla mata harara yaje ya sakawa Maman inda Allah ya taimaketa dama biyun ake buk'ata, guri ta samu tana mayar da numfashi 'yan gefen gurinsu sai sannu suke mata Yusra kuma ta d'auko ruwa ta bata.
‘’Na gode.‘’
Tace da ita tana cisge bakin ledar ta hau sha.
Ana fara sakawa Mama jinin ta samu bacci, sai kuma ga Baba yazo, baiji dad'i ba da ya tarar tana bacci amman sai ya kasa tafiya yaja kujera ya zauna daga gefenta yana jiran ko za ta farka, ganin Baban ya zauna yasa Nusrat da Yusra suka fita harabar asibitin sai gashi sun ci karo da Nimha da mijinta suna ta zagayen neman inda suke, gaisawa sukayi suna tambayarsu me jiki su kuma suna basu amsa kafin suce suzo su shiga ciki su ganta duk da bacci take, suna shiga kuma sai suka tarar ta farka suna magana da Baba, wanda yafiyarsa take nema, tana bashi amanar yaranta, shi kuma sai kwantar mata da hankali yake yana alak'antamagan ganun nata da zafin ciwo ne.
Cike da tausayawa Nimha ta k'arasa gaban gadon tanaiwa Mama sannu, Saminu kuma ya durk'usa gaban Baba suna gaisawa kafin itama ta tsuguna ta gaisheshi, basu wani jima ba sukai musu sallama suka tafi, bayan sun ajiye lemon zak'in da suka kawo ana ta musu godiya, Baba kuwa ranar har dare yakai a asibitin da ya motsa za ta rik'e shi, sai da dabara yake zuwa yayi sallah ya dawo.
Chapter 30 · 0% Book details