Sashe 60
Katanga Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba ta k'arasa ba ya d'auketa da mari.
"Ko ubanki yayi kad'an ya karb'i kud'in nan a hannuna,fitsararriyar banza da ta hofi,ki b'ace mini da gani ko na karyaki a cikin gidannan na karya banza."
Dafe da inda ya mareta tace.
"Ni kuma zan nuna maka na isa na karb'arwa Yayarmu hak'k'inta,za ka iya cin nawa kaci bulis,amman banda nata."
Tana kawowa nan ta busa masa kararan da ta kwance a leda,da yayo kanta zai daketa,ba shiri ya saki ledar da kud'in ke ciki ya hau susa,yayin da Yusra ta d'auke ledar tana dariya.
"Yauwwa Yisra,bani su nan,kinji shale lan jikata"
Wani kallo Yusra ta jefeta da shi kafin tace.
"Ban tab'a ganin zilamammiyar tsohuwa irinki ba,sai mutum yana da abin duniya yake mutum a gurin ki,ba ga iya jikokinki kad'ai ba,hatta ga 'ya'yanki,kina tunanin da mahaifinmu zai daho yaga irin rik'on da kikayi mana bayan mutuwarsa zai yafe miki?ture wanda kikayi mana da ransa,don sai yafi jin zafin wanda kikayi mana bayan babu ransa,don zaiyi tunanin bayan babu ransa zaki dubemu,sai yaga sab'anin hakan,zan iya rantsuwa duk cikin 'ya'yanki Baba yafi sonki da yi miki biyayya da kuma son faranta miki,amman da Allah ya jarabceshi da babu kika bi kika d'ora masa karan tsana,tunda kika yiwa d'an cikinki su waye mu don kin mana,amman ki tina fa,akwai hisabi tsakanin d'a da mahaifa,domin kiwo ne ya baku,kuma sai ya tambayeku yadda kuka rik'e amanar da ya baku, idan ba ki guji duniya a yanzu da kike neman gangarawa ba sai yaushe,ko mak'iyina ba zan so zuciyarsa ta kasance irin taki ba Iya,wannan kud'in kuwa kinyi kad'an ki ci ko da ficika a ciki,darajar tsufanki ce kawai za ta saka na k'yaleki ban watsa miki kararan nan ba wallahi." Kafin ta juya ta kalli Baffa Shamsu da ke ta faman susa,duk yayi wurgi da kayan jikinsa saura gajeran wando da singileti tace.
"Rigima idan ta shafeni mazewa nake,idan aka tab'a Yayarmu kuwa illatarwa nake,zan iya sauka akan ko wani bugire indai akan Yayarmu ne,idan kuma kana ganin k'arya nake ka biyo ni da sunan kazo karb'ar kud'in nan,ko kuma in an kawo lefe wani ya tab'a tsinke a ciki."
Tana kawowa nan ta juya ta fita daga d'akin,suka had'a ido da Umma da ke rarraba idanu,ta watsa mata ragowar kararan hannunta,yayin da ta saki ihu ta nufi d'akinta da gudu tana susa don gudun kada tayi tsirara a waje,Baffa Shamsu ma da yaga abin ba na k'are ba ne da gudu ya fice ya nufi gida.
"Kawu kayi hak'urin b'oye makan da nayi"
Yusra ce ke gayawa Kawu Iliya haka.
"Me kika b'oye mun?" Ya tambayeta,yayin da ta kwashe duk abinda ya faru da Nusrat daga barinta gidan Aunty Maryam ta gaya masa inda ta d'ora da. "Yayarmu ce tace kar na gaya maka shiyasa nayi shiru da maganar,gidan k'awata ma da nake ce muku na tafi, gurin Yayarmun nake zuwa,to shine yanzu wanda ya taimaketa zai aureta shine aka kai mata kud'in aure,to sun ce basa buk'atar ko tsinke da za'a kaita da shi,shine Baffa Shamsu ya bata kud'in auran a hannunta,ita kuma tace in kawo maka ka ajiye mata." Idan ta gaya masa yadda akayi ta anso kud'in,zaice ta mayar masa ne don shine k'anin mahaifinsu shi yafi can canta da ya rik'e kud'in a hannunsa,kawai ta yanke gobe insha Allah za taje hisba takai k'arar Baffa Shamsun don a ja masa kunne,ba irin k'anin mahaifin da ake sakarwa komai ba ne,ko Nusrat yanzu ba za ta gaya mata ta anso kud'in ba sai nan gaba,don ta san halinta itama za ta iya cewa a mayar masa ko ya cinye babu komai,itakwa tana jin zuciyarta bugawa ce kawai baza tayi ba idan yaci kud'in nan.
Kawu Iliya da Aunty Hafsa sunyi matuk'ar farin ciki da auran Nusrat in,musamman da Kawu Iliya yace ya san Aashiq in da za ta aura mutumin kirki ne,akwai taimakon alumma.
。。。。
A hankali yake sakkowa daga benensa,duk yayi wani iri da shi,yau kusan kwana biyar rabon da ya sanyata cikin idonsa,ya matse kansa sosai,abinci ma in zai sakko yaci sai ya tabbatar sun bar falon,shima kuma yayyagula zaiyi ba kamar daa da yake sakin jiki yaci sosai ba,bai san da kai kud'insa da akayi ba,Hajjaju ce tace kar a gaya masa,har sai an d'aura auran don zai iya basu ciwon kai.
Motsi ya juyo a kicin kai tsaye ya nufi can,ya tsaya daga bakin k'ofar yana k'are mata kallo,,tana tsaye tana wanke kwanukan da ta b'ata,tun dosowarsa kicin in taji a jikinta,ga mayen turaransa da ya cika mata hanci,tunda ya tsaya ta daina fahimtar komai,zuciyarta ta tafi garesa gaba d'aya,sai ta koma yin wanke wanken a sanyaye sakamakon da da take yi da kuzarinta,sai da ya gama morewa kallonta kafin ya taka ya shiga cikin kicin in,duk wani taku da zaiyi da bugun zuciyarta yake tafiya,rungumota yayi ta baya yana sauke bakinsa kan kunnanta,a tare suka sauke ajiyar zuciya,wacce ta futo da iska mai d'umi ta sauka cikin kunnanta,rintse idanuwanta tayi tana jin wani abu na tsirgawa ta mararta,a duk sanda sukayi kusanci da Aashiq sai taji irin wannan yanayin,wani zubin ma ko kallonta yayi haka take ji,kuma akansa kawai take karb'ar yanayin.
"Duk yadda zan takura zuciyata nayi,amman ta kasa hak'ura da ke,ina so nayi miki adalci cikin rayuwarki,amman sai dai adalcin kokawa yake da numfashina."
Yana ajiye maganar yana kuma matseta cikin jikinsa,had'e da sauke mata kiss me matuk'ar d'umi a dokin wuyanta,ji tayi duk gab'ob'in jikinta suna sassarewa,abinda ke tsirgawa ta mararta tana jin fitarsa da d'umi a jikinta,k'afafuwanta sunyi sanyi kamar ba zasu iya d'aukarta ba,tana son magana amman ta kasa saboda yanayin da ke sauka a jikinta,juyo da ita yayi yana k'arewa fuskarta kallo yana shirin sauke bakinsa kan nata ta kautar da fuskarta had'e da dak'unata kafin tace.
"Muje na baka abinci tukunna."
"Ina jin yunwar,amman nafi buk'atarki akan abincin,domin rashinki ne ya hanani ci,kwatanta rayuwa babu ke Nuss yana sakani ciwon kan da sai na kwana biyu kan ya sakeni,ki daina cewa zaki barni don Allah."
Murmushi ta sakar masa wanda ya k'ara jinsa matatce akan k'aunarta.
"Aash da Nuss,rayuwar da basa tare ba sunanta rayuwa ba,zan kasance tare da kai a ko da yaushe,har zuwa ranar da numfashina zai tsaya."
Tana kawowa nan ta ja hannunsa ta zaunar da shi akan kujerar teburin cin abincin da ke kicin in,kana ta zuba abincin a plate ta soma bashi yana binta da kallo cikin so da k'auna,yana gama ci ta d'auko rubutunsa da ta karb'o gurin Malam ta bashi,itama yanzu kullum sai Malam ya bata rubutu,da hayak'i tana yi,saboda sunyi waya da Asghar ya gaya mishi auran Nusrat in za'ai da Aashiq kuma dama Malam in ya san matsalar Aashiq d'in.
。。。
Saura sati d'aya biki aka kai lefan Nusrat,saitin akwatina shida,Hajja mahaifiyar Asghar Hajjaju ta saka ta had'o lefan,Yusra tana can aka kai lefan ta kafa ta tsare,mutane sai cin cirindon zuwa ganin lefan ake, wasu cewa suke anya kwa ba siyar da ita za'ayi ba,wasu suce ai sunji dama ance wanda zai auretan sau hud'u yana aure matansa na mutuwa a ranar da aka kaisu,k'ila jininsu yake shanyewa yake tsafi da shi,magana dai iri iri babu wacce mutane basa fad'e,inda Umma ta sanu bakin magana tana ta yadawa Yusra magana. "Ki daina dai kirinki tsafi za'ayi da Yayar takun da ki
ke girin gid'ishshille a kanta.‘’
"Bak'in ciki ne dai yayiwa mutum yawa,bayan gorin aure da aka gama yi mata,gashinan Allah ya bata miji na kere sa'a,sai dai mutum ya mutu don haushi."
Ana gaggama ganin lefan su Khalil suka zo da motocinsu suka kwashesu aka kaisu can gidan Kawu Iliya,yayin da Umma ta dinga fad'in dama dai opay ne mu za'a rainawa hankali, Iya kuwa ina jin dai an saukar mata da,manzon shiriya,tun ranar da Yisra ta gaggaya mata magan ganun nan suke mata ciwo,gami da suya a ranta,ba ta tab'a sanin kuskure take aikatawa ba sai a ranar,ba ta tab'a jin kunyar halinta ba sai a ranar,halintane k'aramar jikarta take fad'in ko mak'iyinta ba za ta so yayi hali irin nata ba,tabbas ta aikata kuskure,kuskuren da babu damar gyara na baya sai dai na gaba,gaban kuwa ta tabbata ba za ta k'ara ko da kwatan shekarun da tayi a baya ba,kuma babu ran Maimuna da Audu bare ta nemi yafiyarsu,uwa uba mijinta Malam,me sonta da k'aunarta,me hak'uri da halayenta,tayi kuka kamar ba gobe,tana neman yafiyar Ubangiji ko za ta samun sauk'in wani abun, gaba d'aya tayi sanyi duniyar ta fita a ranta.
"Yisra,don Allah ku yafe mini,kicewa 'Yar baiwa itama ta yafe mini."
"Nidai na yafe miki,amman Yayarmu bazan nema miki yafiya gurinta ba har sai na tabbatar da ingancin nadamarki, ba kwad'ayin daular da za ta shiga kike yi ba."
Binta kawai tayi da kallo cikin k'unar zuciya,yanzu me son duniya ya haifar mata?
。。。。
"Dan Allah kayi sauri ka fito daga wankan nan,lokaci yana k'urewa fa."
"Kaga ni malam kada ka takura mini,kak'i gayan d'aurin auran wa zamuje kuma kazo kana azal zalata."
Yakai k'arshen maganar yana fitowa daga toilet in,murmushi Asghar yayi yace.
"Kada ka damu,idan munje zaka ji ko na wane,abinda a cikin masallacin estate innan za'a d'aura."
Tab'e baki Aashiq yayi yana zama kan stool in mudubi,kyakkyawar fuskarsa ta bayyana a ciki,kafin yasa towel in hannunsa yana tsane ruwan da ke sumarsa.
"Dan Allah kayi da jiki,yanzu sai ka tsaya shafe shafe kamar wani mace."
Cewar Asghar yana fito masa da shaddar da zai saka daga leda,iri d'aya ce sak da ta jikinsa har d'inkin,shine ya d'inka musu har Aasad,amman da ya karb'a Aasad in dariyar mugunta ya bisu da ita,don yaga Asghar in sai wani zumud'in auran yake,bayan kamar wa'yan can shima haka wannan d'in zai kasance.
An d'aura auran,Aashiq Aliyu Gogel,da na amaryarsa Aysha Abdullahi Ahmad (Nusrat)kunnuwansa ba su gama jiyo masa da wacce aka d'aura masa aure ba numfashinsa ya tsaya cak ya zube a gurin, yayin da Aasad yake adduar Allah yasa ya k'arasa can gaba d'aya.