← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 69

Sashe 56

Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lalacewar ciki
Garin zogale,rai d'ore garin habbatus sauda, sai a had'asu guri d'aya a cakudasu ana shan cokali daya, safe,rana,dare,a kunu ko koko.
[6/11, 11:27 PM] Rabi: 43
Aliyu gogel,haifaffan garin gogel ne,mahaifinsa ya rasu tun mahaifiyarsa Hajjaju na d'auke da cikinsa,shine d'ansu na biyu,amman na farkon ba rayayye ba ne ya rasu tun yana da shekaru biyu a duniya sakamakon k'yanda da yayi fama da ita,Hajjaju ta tsaya tsayin daka gurin tarbiyar tilon d'anta,duk wani tashi fad'i tana yi akan rayuwar d'anta ta inganta, abokansa tun na k'uruciya biyune daga Ibrahim (Baffa Ibrahim) sai Hamza (Baffa k'arami)Abokansa ne k'ush da k'ush,gidajansu yana manne da na juna shiyasa a ko da yaushe zaka samesu a tare sai dai idan Aliyu ya tafi makarantar boko,kasancewar yawancin duk samarin da suka taso d'ai d'aiku ne masu zuwa makarantar boko Aliyu yana d'aya daga cikinsu,kasancewar shima Hajjaju ta tsaya a kansa,to idan ya dawo daga boko makarantar allo da ta dare duk tare suke zuwa,suna matuk'ar k'aunar juna,Aliyu yaso suma a sanyasu a makarantar boko amman mahaifansu sunk'i,saboda hali na rayuwa kuma ba su kad'ai ne a gabansu ba kamar yadda ya kasance shi kad'ai gurin Hajjaju.
Hamza yana matuk'ar bak'in cikin yadda rayuwa take garawa Aliyu,babu abinda ya nema ya rasa cikin rayuwarsa,yakan ji dama shine,dama shine hakan ta kasance a gareshi,yana k'ulafucin son yin karatun boko sai gashi bai samu damar hakan ba,duk Aliyu ya tattare damar,amman ya iya b'oye abinda ke ransa ko kad'an bai tab'a nunawa Aliyu ba sai dai ya nuna yafi Ibrahimma k'aunarsa, sai dai kuma soyayya da k'aunar da Aliyu yakewa Ibrahim ta dabance dan ta huce ta aboki da amini dai d'an uwa.

Bayan ya kammala secondary school insa sai ya koma zariya da zama hannun yayan mahaifiyarsa, inda aka nema mishi gurbin karatu a jami'a ya fara zuwa cikin sa'a, da yake shi 'ya'yansa duk matane sai namiji d'aya sa'an Aliyun,Bashir (Baffa)da k'yar aka samya gama secondary,irin yaran nanne da basa k'aunar makaranta ko kad'an, gashi mahaifin nasa yana son yayi karatu duk wani burinsa akansa ya d'orasa amman yana kauce masa to zuwan Aliyu sai yayi watsi da shi ya mayar da burinsa kacakom kan Aliyun,musamman da yaga yadda yake da jajircewa akan karatu,sai ya hak'ura da Bashir d'in tunda in ya takura masa ma to bazaiyi abin kirki ba tunda ransa ba ya so,sai suke tafiya kasuwa tare.

Duk wani hutu idan ya samu gogel yake tafiyarsa gurin abokanansa, don shak'uwarsu har yau ba ta ragu ba k'aruwa take k'arayi, yanzuma bikin Ibrahim yaje, shine ma yayi masa babban aboki,Hamza ba ya nan ya tafi neman kud'i yadda yaji a bakin Ibrahim d'in.
Abinda yasa Hamza tafiya neman kud'i,saboda yarinyar da yake matuk'ar k'auna Zuriyya mahaifiyar Aliyu ta nema mishi auranta,kuma sunyi magana da iyayanta ta fahimta,inda tace ba za'ai bikin ba sai Aliyu ya gama karatunsa kuma suka amince don haka sai ta sanyata a makarantar boko,wannan bak'in cikinne yasa Hamza barin garin,ya tafi neman kud'i don ya nunawa Aliyu ilimi babu tarin dukiya aikin banza ne don haka zaije neman kud'i,kuma zaiyi kud'i don ya nunawa duniya ko babu ilimi ana yin arzik'i.

Zuriyya k'anwar Ibrahim ce, kyakkyawa ce ta ajin k'arshe don duk a 'yan matan da suka isa aure a k'auyan babu me kyahunta da kalar birninta, ga ladabi da biyayya wannan dalilin ne yasa Hajjaju ta nemawa tilon d'anta auranta don tana tsoron 'yan matan jami'a, ba tayi nauyin baki ba kuwa da yazo bikin Ibrahim ta zayyana mishi tayi masa natar aure,inda babu musu yayi na'am da wacce ta zab'a masa.

Bayan kammala digirinsa na d'aya aka sha bikinsu da Zuriya a lokacin haihuwar matar Ibrahim biyu mace da namiji,Hamza kuwa ko labarinsa ba'a ji, anan k'auyan yabar Zuriya ya koma kano don had'o digirinsa na biyu, da yake a cikin gidansu ya zauna gata ga Hajjaju ba ta da wata matsala sai dai in ya samu lokaci ya dinga zuwar musu.
Sai da ya had'a digirinsa na biyu yayi masters kafin ya soma aiki cikin nasara da albashi me matuk'ar tsoka,nan da nan komai ya fara sauya musu kud'i ya zauna masa, da yake mutum ne me alkhairi hatta 'yan k'auyan cin gajiyarsa suke,sai dai har lokacin Allah bai kawo musu haihuwa ba amman suna zaune k'alau abunsu, a lokacinne Hamza ya dawo, babu laifi ya nemi kud'i ya kuma yi d'an karatunsa,sai dai ko kad'an bai kama k'afar Aliyu a gayu da gogewa ba uwa uba dukiyar da ya tafi nemowa don ya fisa, me makon ya saduda amman ina sai ya kuma jin haushi har da tsanar Aliyun ma,duk da yazo ya tarar da yana kula da iyayansa,don har ginin gidansu ya sauya musu, da ya tashi gyaran nasu ne ya had'e har na su Ibrahim aka gyarasa gaba d'aya.

A kusan lokaci d'aya Zuriya da matar Hamza Nuriya,da ya aura bayan dawowarsa,suka haihu suka haifi 'ya'yansu duk maza,inda Aliyu yasawa nasa d'an Aliyu,sunan mahaifinsa kenan,shima sunansa yaci zasu dinga kiransa da Aashiq, shi kuma Hamza yasawa nasa d'an Aasad.Haihuwar Aashiq tazo mishi da alkhairai da dama don a yanzu har company yake da shi me zaman kansa, bayan asibitin da ya gina da masallatai duk a garin Zariya don tun fara aikinsa ya d'auko Zuriya suka dawo zariyan,sai dai duk weak end a gogel suke yi, saboda Hajjaju tak'i yadda ta biyosu, acan ma ya gina masallatai,duk wani abu da babu a k'auyan ya kai musu,don haka suke matuk'ar alfahari da shi.

Ya gina k'atuwar estate duk da danginsa ba su kasance masu yawa ba yayi ne don Al'ummar annabi,da duk wani d'an gogel da zaizo neman kud'i,kansa tsaye yazo ya samu gida a ciki ya zauna. ya gina gidaje hud'u tanfatsa tanfatsa iri d'aya sak, nasa da na Ibrahim,Hamza,Bashir, haihuwar matarsa uku biyu mata sai namijin sa'an Aashiq me suna Asghar, dukkanin su ukun ya basu aikin da ya dace da iliminsu cikin companynsa, Ibrahim kuwa ya kaishi kasuwa donshi baiyi wani ilimi ba.
Bayan ya gina estate sai ya gina gidan marayu, kafin ya kuma yin wani companyn nasa a Abuja,a lokacin Shekarar Aashiq biyar a duniya an haifo masa k'anwarsa mace wacce taci sunan Hajjaju suna kiranta Aaleesha,a haihuwarta ne Hajjaju ta dawo gidan da zama da k'yar,ita tafi son zaman gogel,kamar yadda mahaifan su Ibrahim da Hamza suka k'i dawowa.

Hamza da Bashir sun k'ulla ne yayin da suka gano burinsu d'aya ne na son ganin bayan Aliyu,da dukiyar da yake tutiya da ita ta dawo hannunsu, don haka kullum cikin kitsa yadda zasu ga bayansa suke, musamman yadda ya cika zuciyoyin mutane da k'aunarsa ba iya cikin garin zariya ba har gogel gaba d'aya,yana rayuwane domin al'umma ba a cikinsu kad'ai,kullum cikin taimako da cika musu burinsu yake.

Al'amarin ya faru ne Aashiq yana da shekaru goma a duniya..

Tsarin haihuwa

1-Idan aka jik'a gishiri da mad'aci aka sha kad'an a watan ba zaa samu ciki ba in Allah ya so hakan.

2-'Ya'yan garafuni,idan aka sha guda uku to a wannan shekarar ba za'a samu ciki ba, ko kuma a daka ayi insertin da shi za'a dace in Allah yaso hakan.

3- A miki laya da ganyan na'a na'a, idan kina tare da ita ba za ki d'au ciki ba, sai dai in rabo ya tsago.

4- Kuna gama saduwa ki mik'e tsaye ki lashi gishiri ki tsalle.

Ki saka a ranki komai nufi ne na Ubangiji.
[6/13, 9:01 PM] Rabi: 44
Abuja suka tafi da shi da Bashir da Hamza,kafin tafiyarsa da k'yar suka rabu da Aashiq,mak'ale masa yayi sai ya bisa don yafi k'ulafucinsa akan mahaifiyarsa ita kuma Aleesha tafi k'ulafucinta.
A ranar sukayi abinda zasuyi suka juyo saboda fitar wuri sukayi don su daho akan kari,sun kusa shiga zariya al'amarin ya faru, akuya kawai ya gani a gabansa bai san daga ina ta fito ba,saura kad'an yabi ta kanta yaja wani irin birki wanda har yayi tunanin tayarsa ta samu matsala ya fito don ya duba ya gani,wasu mutane ya hango sun taho da makamai a hannunsu, cikinsa ne yayi wani irin k'ugi ya nufi motar a gigice yana jan murfin sai ya jita a kulle,a rikice ya kalli su Hamza da ke cikin motar yace.
"Ku bud'e mini,mu gudu wasu mutane ne suka taho."
Yana maganar yana waigawa yana kallon mutanen sun kusa zuwa dab da inda yake,tuni tsoro ya gama mamaye zuciyarsa.
"Ku bud'e mini don Allah, sun kusa taddani."
Babu wanda yace d a shi k'ala kamar gumaka haka suka zama,cikin raunin murya da sarewa yake cewa.
"Bashir,Hamza abinda zakumun kenan,me nayi muku da zaku aikata mun hakan?"
Sai a lokacin dabarar guduwa tazo masa amman ina sun riga da sun cimmashi,wani k'aton k'arfe suka d'aga suka k'wala masa a kansa.
"Iyalina,ku kulamun da Aashiq."
Itace kalmarshi ta k'arshe kafin ya fara kalmar shahada,jina jina sukayi masa,kafin Hamza da Bashir su fito daga motar suna jinjina musu,kana suka yiwa motar kwatsa kwatsa yadda zai nuna hatsari yayi, kafin su d'au wayarsa da itama suka yi mata kwatsa kwatsa,suka kira Ibrahim suka sanar masa yayi hatsari bayan sun kira police sun kwatanta musu gurin,kana suka bar gurin bayan sun tabbatar ba su bar shaidar komai da zai tona asirinsu ba.
Chapter 56 · 0% Book details