← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 69

Sashe 68

Katanga Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da sukayi sallar isha'i kafin su had'u dukkaninsu akan dining,d'aukar Amna Aashiq yayi yana jin son ganin jininsa shima,aikwa ta shiga zaro masa zance,shi kuma yana biye mata,sun gaisa da Shukhura sosai a ranta tana yaba kyau da tsarin mijin Yayartasun don tayi kyahun dace kamar yadda shima ya dace,bayan gama cin abincin nasu kafin ya tashi Shukhura ta rok'eshi akan ya bata aron Yayarsu su kwana iya yau kawai,bazai iya hanata ba don ya tabbata itama Nusrat d'in za ta so hakan,amman ya tabbata zai mugun azabtuwa kafin gari ya waye,ya riga ya saba bacci a jikinta yana jinsa jikinta ba ya sanin sanda bacci yake saceshi,amman idan ba ta kusa da shi ba ya wani samun isasshen bacci,d'aga mata kai yayi kafin ya kalli gurin da Nusrat d'in ke zaune yayi mata kallon da ita kad'ai tasan ma'anarsa. Raba dare sukayi suna hira,kowa yaji abinda ya faru da d'an uwansa bayan rabuwa,akan filo d'aya suka kwanta duka su ukun,suka saka Nusrat a tsakiya kamar yadda suke a gida,suna jin inama baya ta dawo suga Mamansu tare da su.
Takaddun Yura sun fito,suka fara shirye shiryen tafiya,sunje gogel sun musu sallama,su Baffa Ibrahim da kakannin Aashiq kamar su lashe Nusrat don so da k'auna,haka ma mahaifan Baffa k'arami,da har yau suke jin ciwon abinda d'ansu ya aikata,ranar da sukaje gidansu sallama take jin Umma na asibiti k'ashin k'afarta ya rub'e za'a yanke mata k'afar kuma babu kud'in yi mata aikin,da ta koma gida sai ta bud'e gurin da take ajiyar kud'in da Aashiq ke yawan bata,kuma ita ba taga amfanin da za tayi da su ba komai na more rayuwa akwai shi tattare da su babu abinda ta nema ta rasa,idan ta nema d'inma zai siya,tambayarta yayi abinda za tayi da kud'in shine take gaya masa,yace ta ajiye kud'inta,a ranar suka je asibitin ya biya kud'in,kuka Nimha ta dinga yi tana yi musu godiya,Shukhura da taji labari ta dinga yiwa Nusrat banbamin me yasa ta biya,ai da ta bari duka k'afofin sun rub'e sai aga k'afar zuwa gurin boka,Nusrat tace."Ai yanzun ma idan tana da hankali,ya kamata ta hankaltu,kuma ni don Nimha nayi,ko yaya ne mahaifiyarta ce,kuma tana son kayarta domin ba zab'inta bane mahaifiyarta ta kasance a haka,don da zab'inta ne na tabbata baza ta tab'a d'aukar Umma a matsayin mahaifiya ba,Shukhura kowa da zab'i ake bar masa bazai tab'a d'aukar bara gurbi cikin zuri'arsa ba." "Hakane Yayarmu,nima naso yi don Nimha,amman idan na tuna abinda ta mana sai naji na kasa,amman na gayawa Mustapha yace zai biyawa Saminu bashin a sakesa"
Sai a lokacin Nusrat taji abinda ya faru da Saminun don daa ba ta sani ba,inda ta k'udirce a ranta bayan fitowarsa za tayiwa Asghar magana a bashi wani aikin a company,domin Nimha ba abin yarwa bace a gurinsu,'yar uwarsu ce jininsu ce basa bambamta ta,ko a daa ma mahaifiyarta ce ta janyo bam bamci da Nimha ta gane don kanta take neman kusanci da su. Ranar laraba jirginsu ya d'aga zuwa Lakshdweep,sati guda da zuwansu aka gama hada hadar komai abu na kud'i nan da nan suka soma karatunsu cikin kwanciyar hankali....
[7/1, 10:26 PM] Rabi: 54
Bayan shekaru biyar,sun kammala karatunsu cikin nasara,har lokacin haihuwa shiru babu labari,duk da so da k'aunar da suke na ganin jininsu basu sanyawa ransu damuwa ba,tunda duk sun tabbatar lafiyarsu k'alau,sun tabbata komai lokaci ne idan akwai a rubuce zasu haihu to zasu haihu d'in,idanma Allah bai basu ba zasu rungumi k'addara ba zasu butulce mishi ba,may be ba alkhairi ce garesu ba shiyasa bai basu ba,da Shukhura ta haifi cikin jikinta mace ta haifa me kama da Nusrat sak,wani ma zai iya rantsuwa Nusrat ce ta haifeta,kuma sai ta yiwa Nusrat d'in takwara,tana yin arbain suka taho lakshdweep ita da Mustapha suka kawo musu little Nusrat suka gani,da suka tashi tafiya anan suka baro musu Amna,sai ta k'ara raya musu gidan suka sanyata a makaranta,kafin su tashi dawowa taje primary 3 in yaso in suka dawo sai ta d'ora daga inda ta tsaya.
Sai da suka jira suka harhad'a takaddunsu,kafin su wuce yawon k'asashe kana suka yada zango a saudiya don sauke farali,a can suka had'u da Baba da 'yar matarsa Aunty Shafa, bazawara ce ya samu yayi wuff da ita,gata da kirki sosai da son jama'a,duk shekara sai sunzo aikin Hajji wanda Aashiq ne ya d'auki nauyin hakan,Iya ma tazo shekaru hud'u da suka wuce,yanzun ma don k'arfinta ya jaa ne,inda Shukhura ta dinga yi mata tsiyar cewar,gashinan dai su da ta tsana ta tsani mahaifiyarsu gajiyarsu take ci,wacce ko mahaifiyarsu ba ta samu damar ci ba,Nusrat d'in da take cewa 'yar aljanu gashinan tana cin arzik'inta bayan duk cin kadjin da ta mata ashe a sanadinta za taje ta sauke farali, iya sai dai tayi shiru tana jin kunyar abinda ta aikatawa jikokin nata da kulluum cikin rok'ar yafiyarsu take kafin ta gangara,harma da 'ya'yan nata,tana k'ok'arin gino musu KATANGAR da ba ta ginota ba tun suna yara.

Suna dawowa suka fara jan ragamar company d'in,nan da nan suka fara bunk'asa,rayuwa ta k'ara yi musu dad'i,ga Amna da ke hannunsu,da gaske dai Shukhura ta bar musu ita halak malak,inda suka sanyata taci gaba da zuwa makaranta anan,duk wani hutu da su Shukhura zasu samu gurin aiki,gidan Yayarsu take tarewa har Mustapha ya gaji yake biyota,da yake yana da hak'uri,kuma zuciyarsa ta riga ta raunata sosai duk wani abu da Shukhura take so shi yake so,ko baya so zai fara sonsa daga ranar da yasan tana so,muk'ullin kusa da nasu Aashiq ya basu suke sauka idan sun zo,da yake sun koma can kusa da gidan Asghar,dama gidan nasu a jere yake su uku,da nasa da na Asghar da Aasad,sai ya basu na Aasad d'in,da yake sun baro gidan Hajjaju,sai su Baba Azumi suka koma can,zaman Nusrat da ita,yasa ta jin baza ta iya zama ita kad'ai ba,Yusra a sha ruwan tsintsaye take mata,su Baba Azumi na dawowa ita da Baba Hadiza,ta sulale ta dawo gurin Yayarsu,da yake anyi bikin Faiza da Khalil shekaru biyu da suka huce, suma dai suna cikin estate d'in da zama. Shukhura ce ta matsawa Nusrat da cewar,tana yi mata alamu da masu ciki,anya kuwa ba ciki ne da ita ba?Nusrat tace ke ba likita ba bare nace kin gano kawai dai idonki ne ke nuna miki haka,Shukhura sam ba ta yadda ba sai da ta tilastata yin fitsari ta bata,ta siyo tsinke ta gwada,sai ga rad'a rad'an jan layi biyu,rawa sosai Shukhura ta hau tik'a,yayin da Nusrat sam tak'i yardar cewar ciki ne a jikinta,Aashiq Shukhura ta fara kira ta gayawa ma,da yake baya nan sunje Abuja shi da Asghar,suna shirin bud'e wani companys,d'inne,daga Aashiq sai ta kira Baba,sai Hajjaju na zaune,ba ta wani takwar kwashe ba har yanzu da d'an k'arfinta da yake an taso da farcen susa,su Baba Azumi kawai sai gani sukayi tana girgid'a kai suka tambayi ba'asi ta gaya musu,suma sai suka,hau murna da farin ciki,yayin da Hajjaju ta kira wayar Baffa Ibrahim ta gaya masa nan da nan suma suka hau murna suna masu mik'a godiyagurin Ubangiji da ya amsa musu addu'arsu, Aashiq kuwa yana gama waya da Shukhura ya kira Nusrat don yaji ta bakinsa don yasan halin Shukhura za ta iya d'ibarsa,duk rashin son maganarsa idan suka had'u da Shukhura sai ta sakashi,ga copynta nan kuma a gurinsu Amna,idan ya dawo bakinsa ba ya shiru har sai tayi bacci,ta sanar masa fitsarinta ta gwada ya nuna tana da cikin,amman ita ba ta wani yadda ba,yayin da Aashiq ya shiga nuna zallar farin cikinsa da kuma mik'a godiyarsa ga Ubangijinsa.

Kamar jira ake asan da zaman cikin nata ta fara laulaye laulaye,inda sukaje adibiti gwajin farko ya nuna tana da ciki har ba tsawon wata uku,farin ciki gurin Aashiq kamar a sannan yasan da zaman cikin,a ko da yaushe idan suna tare hannunsa yana k'asan cikinta yana jin d'umin gudan jininsa,ashe shima zai haihu,ashe zai zamo uba,ashe zai ga gudan jininsa,ashe shima Allah zai bashi farin cikin da ko wani bawa ke sani yayin da ya azurtashi da samun d'a. Ni ban san wa yafi bawa Nusrat kulawa ba tun daga samun cikinta har ya tsufa,Aashiq dai yace kowa sai dai ya biyo bayansa,tunda cikinta ya tsufa Baba kullum sai yazo ya kawo mata rubutu da kansa ya zauna ta shanye sannan zai tafi. Kowa idan yaji cewar Nusrat ta haifi 'yan biyu sai yayi mamaki,saboda cikinta baiyi girman da zakayi tsammanin biyu ne a ciki ba,farin cikin da ke zuk'atan bayin Allah nan bazan iya rubuta muku shi,anyi hidimar suna,anyi shagali babu kama hannun yaro a sunan twince,musamman dama da ba wani shagli akayi ba a bikin nasu,Hidaya da Hibba sunzo,saura wata biyu bikinsu,tare za'a had'a,Daddy ya gaji da ajiyarta ya bawa abokinsa ita, Nimha ma tazo tun ana ya jibi suna da 'ya'yanta uku biyu maza mace d'aya,Amima ma tunda akayi haihuwar tazo,da yake mutuniyar Yusra ce,sai dai har yau Amiman babu wani k'wak'k'waran saurayi da ke zuwa gurinta.
Chapter 68 · 0% Book details