← Book details Katanga Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 69

Sashe 23

Katanga Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan kammala saukar aka fara kiran d'aliban da sukai na d'aya zuwa na goma don a basu kyauta.
Aysha Abdullahi Ahmad aka fara kira wacce tai na d'aya sannan aka kira Safiyya Abdullahi Ahmad ita tai ta biyu sai Maryam Farouq Fanda da tai na uku daga haka har aka kai na goma duk aka basu Kyaututtukansu, anan Alhaji Faruoq Fanda ya karb'i speaker yai magana akan ya bawa makaranta kyautar million d'aya, sannan ya bawa Aysha Abdullahi Ahmad da Safiyya Abdullahi Ahmad kyautar million d'aya, saboda yaba k'wazonsu, cikin d'alibai kusan 100 su suka d'au matakin na d'aya da na biyu.
Nan gurin taro ya hautsine kowa na fad'in albarkacin bakinsa, yayin da wasu ke cewa ai kyautar million biyu gurin Alhaji Farouq Fanda ba komi bace kamar biyar haka yake jin ya cire daga aljihunsa.
Iya kuwa sai dashe baki take ta na kuma b'antarar goronta, ta kalli Umma da ranta yai bak'ik'k'irin saboda bak'in cikin Shukhura da Nusrat, harara Iya ta galla mata tace.
"An dai yi asarar haihuwa, ace duk kyaututtukan nan da ake rabawa babu sunan Nimha ko d'aya, saboda k'wak'walwarta irin ta jaki ce, amma kalli 'ya'yan albarka, gaskiya Maimuna ta iya haihuwa banda kyaututtukan da suka samo har kyautan million d'aya suka samo mana saboda 'yan arzik'i ne su irin albarka, don ni har ma na fara kasafta nawa kason da za'a bani, na san dai zan samu kamar dubu d'ari biyu, kinga dubu d'ari zan sayi kayan abinci har da su maltina da madara da su k'wai, da taliyar nan me kanannad'ewa ta gwamnati, d'aya dubu d'arin kuma na ajiye a hankula ina zara ina siyo gasashiyar kaza da youghot ina ci da daddare in tayar da kai, wayyo ai a cikin satin nan ma sai an k'asa gane ni zan canja kala saboda cin dad'i, fatar nan tawa da ta fara yamutsewa saboda wahala za ta gyaru, kai Allah dai ya shiwa Maimuna albarka da ta haifo wa'yannan 'yan albarkar, tun da nake ban tab'a rik'e dubu goma ta kaina ba, amman gashi dalilinsu zan rik'e,har dubu d'ari biyi, ni ban san ma tun tuni me ya hanani nuna musu k'auna ba wallahi, amman duk cikin jikokina Allah na gani na fi son su.“
Duk zubar nan da take ita kad'ai take yinta, don Umma ta bar gurin saukar tun sanda ta fara maganar, saboda ganin za ta d'ora mata wani bak'in cikin ne kawai, da ta jujjuya ba taga Umman ba itama sai ta nufo gida ta na tafe ta na kuma kasafta dubu d'ari biyun da za'a bata.

Sai kusan k'arfe uku suka baro gurin saukar, saboda an yiyyi hotuna acan, a matuk'ar gajiye dukkaninsu suke, don haka ko waccensu sai da tai wanka kafin su kwanta zuwan jiran yamma ta yi, duk da gidan nasu a cike yake da 'yan hidimar saukar.
Da yamma sukai walimarsu anan cikin gidan, kaya iri d'aya suka saka dukansu, Aunty Maryam ce ta d'inka musu, itace ma ta d'au nauyin kayan snacks d'in da suka raba a walimar.
Har kusan dare Iya na d'akin Mama tak'i tafiya sai jan Mama take da hira, Mama kwa sai dai tai ta binta da um da umum saboda rashin sabo.
"Aini fa ko, tun tuni dama ina sonki da 'ya'yanki dama duk makircin shegiyar matar can ne wallahi, kullum ita kenan kawo mini b'atanci akanku, ai gashinan ta haifi yarinya mai k'wak'walwa irin ta jaki, da k'afafuwanta kamar na babyn roba. “
"Uhm“
Mama tace kawai, ta na mik'ewa don jin ana kiran sallar isha, in ba sallar ta tayar ba Iya ba za ta k'yaleta da wa'yannan zantuttukan nata mara sa kan gado ba, ganin Maman ta tayar da sallah yasa Iya ta tashi ta fice ta na jifan d'akin Umma da banzan kallo, Umma ta na hangota ta labule a ranta tace.
'Makirar mata kawai, insha Allahu k'wandala ba za'a baki cikin kud'in ba inga ta tsiya, ina nan kuma za ki dawo jikina in miki rashin mutumcin da har ki koma ga mahaliccinki baza ki manta shi ba, tsohuwar banza kawai.'

Iya tun ta na jiran shigowar Baba yazo a kasafta kud'in, har bacci yai gaba da ita ba tare da ta sani ba, Baba kuwa sai gurin 11 na dare ya shigo, bayan ya rufe gurinsu ya kirawo Mama da su Shukhura anan ya ke gaya musu.
"Na kai Accaunt number d'ina makarantarku, Alhmdlillh d'azu na ji kud'inku sun shigo har million d'aya, yanzu me kuke gani za'ai da kud'in?“
Shiru dukkaninsu sukai su na kallon Mama, ganin Maman ba za tai magana ba yasa Nusrat tace.
"Nidai Baba a shawarata kawai ka bar kud'in a Accaunt d'inka, in yaso sai a 'yebi wasu daga ciki a siyo kayan abinci, duk wata lalaura da za ta taso sai a magance da kud'in ko kuwa? “
Ta fad'a ta na kallon Shukhura.
"Eh Yayarmu, nima hakan nake shirin fad'a kika riga ni. “
Murmushi Mama ta yi, ta na mai yabawa da hankalin yaran nata, kuma taji dad'in abinda suka ce da mahaifin nasu tace.
"Na ji dad'i matuk'a da abinda kuka yanke, dama nak'i maganane don na ji ta bakinku, ku tashi maza kuje d'aki, Allah ya yi muku albarka. “
"Amin.“Suka amsa a tare suka tashi suka fita, bayan fitar tasu Mama ta kalli Baba tace.
"Ta bakin nasu nima zanyi, ka d'ebi wasu kud'in ka siyo mana kayan abinci, kabar ragowar a asu sun naka, in yaso duk abinda aka d'an samu sai ka dinga ajiye su, saboda kwanan nan za ka ji auran yaran nan ya tashi, kuma duk su ukun nake magana, don Nimha da Shukhura sun fi Yayartasu gab'b'an girma, in suka jero sai ka rantse itace k'aramar su, shiyasa ma ita Yayartasu d'in ba saurayin da ke zuwa gurinta, sab'anin Nimha da Shukhura, bare ma Shukhura babu ranar banza da ba za'a zo ace ana sallama da ita ba, sai na tursasa ta take fita, sai tace ai wai ita Yayarsu ba ta zance. “
"Da gaskiyarki Maimuna, nima ina tunani idan akace mini auran yaran nan ya taso, duk dai da Allah na dogara shi na mik'awa lamurana, tabbas kuma da ace Nusrat na da tsayayye a yanzu zan aurar da ita, tunda ta yi candy tai sauka me kuma za'a jira, amnan tunda babu sai muyi rok'on Allah ya kawo mata na gari, su Shukhura kuwa babu zancen ai yayarsu ba ta zance, shi aure ai lokaci ne ba'a jiran sai yaya tayi sannan k'anwa za tayi, duk wacce ta samu miji zan aurar da ita, fatana dai Allah duk ya had'a su da mazaje na gari, kuma na ji dad'in shawararki hakan kuma za'ai Allah ya shiga lamarinmu ya kuma dafa mana. “
Mama ta amsa masa da.
"Amin. “

300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.

Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.

Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.

#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*

Wattpad@Rashuna
https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_

*KATANGA*

____________
*EIGHT*
Chapter 23 · 0% Book details