← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 58

Sashe 9

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Zaina don Allah ki bar ni na koyawa wannan kucakar yarinyar hankali. Na nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne".
Wacce ta ƙira da Zainan na bi da kallo da ta yi musu alama da hannu akan a kawo mata kujera cikin sauri aka kawo mata ta zauna tana fuakanta na sosai. Tsawon wasu daƙiƙu ba ta ce komai ba sai can ta soma magana a gadarance.

"Ni ce shugaban masu kawo talla a wannan wajen kuma duk wacce kika gani a nan tana ƙarƙashin iko da isata ne. Ko kara na ajiye babu wacce za ta tsallake shi sannan kafin ki kawo talla nan wajen sai kin zo wajena na yi miki regista sannan a kowacce rana dole ki biya haraji ko kuma ki fuskanci hukunci mai tsauri". Ta dakata kafin ta doka mini tsawa"me ye kike sayarwa?".

"Kamar yadda kike gani kunu nake sayarwa. Kuma duk waɗannan ƙa'idodin da kika gindaya ba za su aiki a kaina ba don daga yau ba za ki ƙara ganina a nan ba. An yi na farko kuma na ƙarshe".

"Kunu? Wannan ne kunun?".

Ta ƙarƙare zancen tana saka ƙafa ta yi kutubol da bokitin kununa. Sam na miƙe Zulfa'u ta doka mini wata tsawar, cikin ba da umarni ta ce"koma ki zauna ƙasƙantacciya, ke har kin isa Zaina tana zaune ki tashi tsaye ki tsaya mata akai". Na cire leɓena raina cike da takaici na bi su da kallon ɗaɗɗaya kafin na ce"ita ɗin wace ce da in zan tashi ko zan zauna sai na nema izninta, ko ba ki ga ɓarnar da ta yi mini ba ne? In ce dai talla ta zo kuma ni ma shi ya kawo ni don haka ba mu da wani bambanci. Kayana kuma sai an biya ni".
Suka tashi gabaÉ—aya suka yi kaina suka cakumo ni kokuwa ya kaure a tsakaninmu. Kafin wani mutum ya zo wajen ya shiga tsakaninmu. Ya janye Zaina gefe guda tana tambayata abin da ya faru.

"Allah ya ja zamaninka wannan yarinyar ce ta zo ta zauna ba tare da ta cike ƙa'idodi ba".
Ya juyo yana kallona sosai"ke me yasa kika zo ba tare da kin bi ƙa'ida ba?".

"Ni baƙuwa ce a nan wajen ban taɓa zuwa ba. Shi yasa ban da dokokin ba, maimaikon ta kawo hankali cikin fahimta sai ta sa ƙafa ta zubar mini da kununa". Na kai aya ina yi masa nuni da inda gabaɗaya kunun ya malale.
Ya jinjina kansa yana ƙara kusanto ni har yanzu idanunsa suna kaina ya furta"ba a kyauta miki ba kam, ke Zaina me yasa da ta zo ba ki kawo ta wajena ba?".

Sai da ta wurga masa harara kafin ta ce"na ga zan iya shawo kan matsalar da kaina ne, ba tare da mun je teburinka ba".
"To yanzun kin shawo kan matsalar ne na zo na tarar da ku haka?". Ta waro idanu waje"Mai aska ni nake maidawa magana haka a gaban kowa? Ko ka manta waye ce a gaban ka?. Zaina ce fa tauraruwarka".

"Zaina na gane ki mana akwai ina sanar da ke kuskuren da kika yi ne. Na sha gaya miki idan irin hakan ya faru ki dinga zuwa kina sanar da ni amma sam na fahimci ba kya jin abin da nake faÉ—a miki ba".
Ta zabura ta kurma wani uban ihu kamar wacce aka watsawa garwashi ta yi kukan kura za ta cakumo ni ya tare ta ya riƙe ta gam. Amma duk da haka ba ta fasa kai mini duka ba. Ganin ba za ta tsaya ba ya sanya
shi É—auke ta marin da ya sanya kowa shan jinin jikinsa duk suka yi tsam kamar ruwa ya cinye su.

"Ke Zaina ke wata iriyar mahaukaciya ce jaka kawai marar lissafi. Ana tare ki har kina wani ƙara dagewa sai kin yi, to ga ta ki duke ta na gani. Wallahi in har kika yi kuskuren ɗaura hannunki a jikinta sai na tabbatar da hakan ya zamo kuskure mafi girma da za ki yi a cikin rayuwarki".

"Wayyo jama'a ku taimake ni ga annoba ta zo. Mai aska yau ni kake gayawa haka?".

"Na gaya miki ɗin uwa ta ce ke? Na ce uwa ta ce ke da ba zan gaya miki magana ba?. Na baki mintuna goma ki tattara kayan tallanki ki bar nan wajen, kuma idan ba ki wasa ba har matsayin da na ba ki sai na ƙwace sa".

Za ta yi wani maganar Zulfa ta hana ta, sai da suka rirriƙe ta saboda yadda jikinta yake karma kafin suka bar wajen. Maganar da ya soma yi shi ya dawo da ni duniyar zahiri.

"Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke kyakykyawa da kyawun zubi gami da tsari. Mene ne sunanki?".

"Sunana Amatullah".

"Sunan ya dace da ke matuƙa. Shin ko zan iya sanin adadin kuɗin kunun da Zaina ta zubar miki, ina so na biya don na san hatta su kuɗaɗan za su yi farin ciki idan suka shiga hannun kyakykyawar mace kamar ki". Na ɗan yi jim don na fara tsorita da irin kallon da yake yi mini.

"Ina fatan ba za ki hana ni aikata wannan aikin alkhairin ba. Ya ke tauraruwa mai haske duniya".
Tuna jarfan da zan tarar da gidan idan na koma a haka babu kuɗin kunu babu kunu a wajen Ummata, ya tursasa mini jam dogon numfashi na fesar daga bakina kafin na sama sararin cewa"dukka dubu uku ne amma na yi dubu da ɗari biyu". Babu musu ya zaro kuɗin ya irga su ya miƙo mini yawansu ya tsorita ni don na tabbatar da sun zarce dubu ukun da na faɗa masa.

"Ka yi haƙuri ba na buƙatar kuɗinka, iya kuɗin ɓarnar da aka yi mini kawai nake buƙata".
Bai yi musu ba ya irga su ya ba ni na karɓa sai na miƙa masa dubu daya da ɗari biyun da na yi amma ya ƙi karɓa, na ajiye masa su a wajen na fara tattare kayan tallana. Na kimtsa komai na soma ƙoƙarin barin wajen ya dakatar da ni.
"Zan so ki ba ni damar ki yi miki rakiya har gida. Don na tabbatar da tsaronki saboda na san Zaina kamar yunwar cikina ba ta da daɗi ko na misƙalla zarratin za ta iya bin bayanki". Ambatan sunan Zaina da ya yi shi ya tursasa mini amince ya yi mini rakiya, sai dai ban yi zaton rakiyan zai yi tsayi ba. Har bakin layinmu ya yi mini rakiya kuma bakinsa bai fasa magana da yabon girin jikina ba duk da ba na tanka masa, shi yake kiɗansa yake rawarsa.
[7/13, 7:23 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

________________________________________

Page 0️⃣8️⃣

"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya tsara halittarki ya kuma busa miki numfashi. Bai bar ki haka ba ya kuma yi miki tagomashin iya magana da iya taku".
Cak na tsaya jin kalamanta da suka sauƙa a na'urar naɗar sautina, na juya ina kallonsa don tunin na yi gaba na bar sa sai dai ban yi tunanin tazarar ta kai haka ba. Hijabina da iska ya ɗaga mini shi ta baya na yi saurin gyarawa ina ɗauke kaina daga gare shi.
"Rakiyar ta isa haka na gode sosai Allah ya saka da alkhairi. Ya biya maka buƙatunka".

"Amin tauraruwa, amma zan so na kai ki har ƙofar gidanku don na sauƙe nauyin tsaronki da yake kaina".

Cikin ƙosawa da sauraronsa na ce"Malam na ce maka ya isa na gode, to kuma me ye kake so da ni? Don Allah ka bar ni ka koma wajen sana'arka". Ya yi wani irin shu'umin murmushi yana takuwa a hankali ya zo gabana.
"Ai tun da na yi tozali da ke zuciyata take wajabta min ya zama dole na ba ki kariya da kuma kulawa ta mussamman. Babu wani aikin da ya sha gaban hakan a yanzu". Taɓe baki na yi na ƙara yi masa godiya na ci gaba da tafiya ganin har yanzu yana bi na ya sani ɗaga ƙafa kamar wacce aka jefo haka na faɗa cikin gida ina waige-waige. Saura ƙiris na yi karo da Ummi da Auwal da suke zaune a zaure suna hira, cikinmu babu wanda ya ce da wani ko kanzil na yi wucewa ta cikin gidan.
Duk matan gidan suna waje yayin da Sahura mahaifiyar Amira take baza shewa ta baje a ƙofar ɗakinsu tana irga cinikin da Amira ta yi yau na waina fuskarta kamar gonar auguda.

Kamar wacce aka tsigarawa matsilli haka Umma ta yi wani wawan zabura ta miƙe sa'ilin da ta ganin. Ta iso wajena tana bi na da wani irin kallo kafin ta ce"Amatullah yaya haka nake ganin ƙasa a jikin bokitin?".

"Umma na sayar da shi gabaɗaya, a hanyar dawowa ne bokitin ya faɗa shi ne kika ga haka". Na ƙare zance ina miƙa mata kuɗin ta amsa tana lalle su ɗaya bayan ɗaya, tsakanin mamaki, al'ajabi da farin ciki na gaza bambance takamanmen wanda ya hana Umma yin magana a lokacin sai juya kuɗin take yi a hannunta kafin daga bisani ta ja ni zuwa ƙofar ɗakinmu muka zauna.
Tsakin da manaifiyar Amira ta buga shi ya hana ta maganar da ta yunƙuro za ta yi ta kallo ta.

"Ke kuma tsakin na me ye Sahura?".
Chapter 9 · 0% Book details