Sashe 19
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To ma ce miki aka yi su É—in soyayya muke yi ko me ye? Ko ke za ki ba da shaidar babu wanda nake so a cikin zuciyata sama da Mansur".
"Ko ba soyayya kuke yi ba amma ai abin da kuke yi bai dace ba. Me ye zai kai ki É—akin mutum ku kwashe tsawon mintuna kuna hira don kawai zai sayi abin da kike talle alhalin ku ba muharraman juna ba ne, me yasa ba zai zo ya saya ba kamar yadda kowa yake yi?".
"Lokacin da lamarin zai juyo kanki, na tabbatar miki a sa'ilin ko kalmomin kare kai ba za ki same su akan tsinin harshenki ba".
Rashin gane inda zancen natan ya dosa ya tursasa mini yin shuru ba don na rasa abin faÉ—a ba. Haka har muka isa gida cikinmu babu wanda ya kuma cewa uffan almajiran suka shigar mana da kayan har cikin zaure, ta ba su naira É—ari biyu bayan ta ce da su gobe da safe ma su zo su É—auka mana kayan.
Cike muka iske gidan kowa yana tsaye cirko-cirko kamar waɗanda suka haɗiye taɓarya sai da muka ƙarisa shigowa muka gane wa idanunmu abin dake faruwa.
Mahaifin Ummi ne a tuɓe a tsakar gidan daga shi sai singilet da gajeren wando tana ta ɓarin zancen da ikirarin sai ya ɗaukar wa ɗiyarsa fansan fitar mata da jini da Maman Adnan ta yi ba gaira ba dalili. Yayin da mahaifiyar Ummin take ƙara rura wutar rikicin. Can ka ce kwabo yaran unguwa da uwayensu sun cika ƙofar gidan har cikin zaure babu masaka tsinke.
Muka shige ɗakinmu tare da Amira muka tarar da Umma tana zaune a falo tamkar ba ta san wainar da ake toyawa a cikin gidan ba. Duk rusuna muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu yabo babu fallasa. Amira ta yi mata bayyanin mun sayar har mun dawo Umma ta cika da farin cikin mussamman lokacin da ta miƙa mata wannan dubu huɗu ta haɗa mata da bayanin inda muka same su. Lamarin da ya faranta ran Umma har ya kai ta ga rangaɗa guɗa.
"Aw ashe fa gidan ba lafiya? Amira ai irin ki ake so É—iyar azirki irin albarka. Ga Amatullah nan na bar ta a hannunki ki ci gaba da É—aura ta akan hanya".
"Ba ki da damuwa Umma. Yanzu dai bari na je na huta".
"To yarinyar kirki ɗiyar fita kunya, na gode sosai ko". Murmushi kawai Amira take ta baza wa ta tashi ta fita. Ta bar ni da ƙuncin rai don ban yi zaton za ta iya faɗawa Umma yadda aka sama kuɗin nan ba sai gashi ta shafe idonta ta aikata.
"Umma ga cinikin da aka yi, bari na yi salla na yi shirin islamiyya". Na furta yayin da nake miƙa mata kuɗin cinikin da yake wajena. Ta amsa tana washe baki har kunne, ganin ba ta da niyyar ce mini komai ya sani fallasa abin da yake raina.
"Umma ni ma ko sau É—aya ai sai ki sa mini albarka".
"To Allah ya yi albarka. In ce dai shikenan ko?". Babu shiri wani ƙayataccen murmushi ya suɓuce mini"na gode sosai".
Sallan na yi kana na yi wanka na ci abinci na yi shirin islamiyya na tafi. Bayan mun fito sallan Malam Suleiman ya aiko ƙura na na je na same shi a cikin staff room.
[7/22, 6:43 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
________________________________________
Page 1ï¸âƒ£5ï¸âƒ£
Shuru ya biyo bayan gaisuwar da na yi masa ya amsa. Sai da aka yi nisa kafin ya kawar da shurun ta hanyar soma faɗin"Amatullah na je na yi nazari akan maganganun da muka fara tattaunawa da ke jiya, mataki na farko da za ki ɗauka wanda babu nadama shi ne ki dage da addu'a, ki dinga tashi cikin dare yayin da kowa ya kwanta ki yi alwala ki yi salla ki yi kuka a Allah ki ƙasƙantar da kanki gare sa. Ki yi tawassali da sunanyensa ɗari ba ɗaya tsarkaka ki roƙe sa mafita. Ki nema wa mahaifiyarki shiriya Allah ya sa ta gane illar abin da take aikata. Sannan ɗabar da nake son na ja hankalinki sosai akan sa shi ne kar ki sake shaiɗan ya yi nasara akanki ki wa mahaifiyarki rashin kunya ko ki raina ta ki daina ba ta girma da kimarta a matsayinta na uwa. Allah ya kan jarabci bawansa ta ko wani fage a rayuwa kamar yadda ya zo a tarihin Allah ya jarabci Annabi Ibrahim ta ɓangaren mahaifinsa wanda ya kasance mushiriki. Daidai da rana guda bai taɓa ƙin aikata masa abin da yake so ba, Annabi Ibrahim har tallen gumaka ya yi don jaddada biyayarsa ga mahaifinsa. Don Allah ina mai jan hankalinki da duk runtsi duk wuya da yadda lamura za su sauya kar ki kuskura ki yi wa mahaifiyarki rashin ɗa'a".
Na sauƙe ɓoyayyan ajiyar zuciya kafin na ce"in Sha Allah Malam zan yi amfani da duk shawaran da ka ba ni. Ba zan taɓa kauce wa daga wannan turban ba". Cike da jin daɗin kalamaina ya ci gaba da cewa"Allah ya yi miki albarka ya kawo miki sauƙi da mafita a cikin dukkan lamuranki. Zan ba ki wasu addu'ar da Annabi ya yi amfani da su kuma ya umarce mu da mu yi amfani da su, a duk lokacin da muka tashi roƙon wani buƙata a wajen Allah. Babu inkari matuƙar ka yi su Allah da kansa ya ce yana jin kunyar wanda zai roƙo sa da wannan addu'ar ba tare da ya ba shi duk abin da ya roƙo ba".
"Na gode sosai Malam Allah ya saka da alkhairi ya biya buƙata".
"Amin ya Allah".
Ya amsa yana miƙo mini watar farar fefe da ya rubuta mini addu'ar a jiki, na amsa ina ƙara yi masa godiya. Tun kafin a tashi daga islamiyyar na haddace addu'ar kafin na iso gida ta zauna ɗas a kwanya da saman harshena.
Ina isowa gida na wuce ɗaki na sauya kayan da ke jikina na fito kasancewar ban tarar da Umma ba. Ɗakin su Amira na nufi don karanta mata dashin dacewar abin da ta aikata mini ɗazu, tana kwance a cikin kujera a falo ta duƙunƙune waje guda yayin da ta lumshe idanunta tana ƙare matse wayar da yake kunnenta. Da hakan ya hana ta jin sallamar da na shigo da ita ɗauke a bakina.
Ganin ba ta da niyyar saurara ta ya sani na fizge wayar, ta tashi ta zauna tana kallona bayan ta dafe kanta.
"Wallahi na san duk gidan nan babu wanda zai yi min wannan wulaƙanci sai ke Amatullah". Na galla mata harara"kin kyauta abin da kika yi min kenan ko?".
Cikin rashin fahimta ta ce"da na yi me ye kenan?".
"Ya dace ki je ki sama Umma ki sanar da ita inda aka sama wannan kuɗin? Ni da nasan haka ne ma ba zan bari ki ɗauka ba". Ta tuntsire da dariya har da riƙe ciki lamarin da ya ƙara fusata ni na cika na yi fam na zo har wuya.
"Au! Dariya ma maganar ta ba ki kenan?".
"To Amatullah idan ban yi dariya kuka kike so na yi? Me ye don na sanar da Ummar hanyar da muka sama kuÉ—in?. Ince dai ke ce kullum kike jan hankalina da yi min nasiha akan na guji faÉ—ar abin da daidai ba duk runtsi da matsin lambar da za a yi min na faÉ—i iya gaskiyata a cikin ko wani irin yanayi. Cikin ikon Allah kuma yau na faÉ—i gaskiya kin zo kin titsiye ni".
"Ni ba titsiye ki na yi ba amma ai kin san zancen da ya dace a faÉ—a da akasin hakan".
"Ni dalla ba ni wayata ina shan soyyaya da masoyi kin zo ki katse min jin daÉ—ina".
Ta ƙare zancen tana fizge wayarta da yake hannu ta koma ta kwanta ta ci gaba da wayarta, yayin da na nema waje na zauna na yi tagumi. Babu abin da yake yi mini yawo da kai kawo a cikin raina face yanayin da na sama Umma jiya da yadda Abba ya sauya a safiyar yau. Duk da Abba yana da sauƙin kai da hakan yake sa mutane da yawa tunanin ya fiye sanyi, amma tsayayye ne kuma jajirtaccen mutum ne akan iyalinsa da ba ya ɗaukar wargi a wannan fanni ko kaɗan.
Kamar daga sama na ji an manna mini ways a kunnuna hakan ya dawo da hankali da tunanina da suka yi nisan kiwo gare ni. Na cira kai ina duban Amira.
"Mansur ne za ku gaisa".
Na amshi wayar muka gaisa da shi sannan na yi masa ya hanya ya amsa mini da sun sauƙa, kafin mu yi sallama ya dinga jeranta roƙo akan na kula masa da Amira kafin ya dawo ya ba ni amanarta ya bar ta a hannuna da makamantan su. Sai da na dara sosai kafin na amsa da cewar zai dawo ya same amanarsa yadda ya bar ta da iznin Allah. Da haka muka yi sallama na miƙa mata waya ita ma ɗin sallama suka yi ta ajiye wayar.
Na gyara zamana ina kallonta haɗe da cewa"Mansur yana matuƙar sonki ta yadda ba iya ɓoye hakan har a cikin kalaman da suke fita daga bakinsa. Don Allah kar ki ba wa kowa irin damar shiga zuciyarki balle har ya kai inda Mansur yake, kar ki ci amanar bawan Allah nan ko da wasa". Numfashi mai ƙarfi ta sauƙe da har sai da na ji sautin fitarsa kafin ta soma magana a hankali alamar na taɓo mata inda yake yi mata ƙaiƙayi.
"Ni ma ina jin sa har ƙasan raina, kuma ina sonki fiye da tunaninki. In sha Allah zan yi amfani da duk shawarwarin da kika ba ni".