Sashe 7
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[7/7, 10:28 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 0ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
Sakeke na yi ina kallonta kamar doluwa sai da na ja dogon numfashi na fesar daga bakina kafin na sama damar sarrafa harshena da ya cika mini baki ya kuma yi mini nauyin É—agawa.
"Umma wani irin laƙani ke kuwa? Akwai wanda ya isa ya yi abinda Allah bai yi ba ne? Me yasa ba za ki kwantar da hankalinki ba?. Ko ba ki yi sana'ar komai ba ba za mu rasa ci da sha ba haka nan ba za mu tafi tsirara ba, to mene ne na tada hankali har kike ƙoƙarin faɗawa cikin halaka....". Kafin na rufe bakina ta sauƙe mini marin da ya sani ganin gilmawar baƙin dubu a idanuna, na yi tangal-tangal zan faɗi saboda gazawar ƙafafuwa. Sai da na yi sa gaske kafin na iya riƙe kaina na dafe kuncina ruwan ƙwalla suna ciko mini kurmin idaniyata.
"Ke har kina da bakin magana akan wannan matsalar Amatullah? Bayan ke ce matsalata ke ce sila da tushen shiga ta cikin kowani irin damuwa. Me ye amfanin haihuwarki in har ba za ki zage damtse wajen warkar min da raunin da yake cikin zuciyata ba? Me ye amfanin haihuwarki in har ba za ki kashe wutar da take ƙoƙarin ƙona min zuciyata ba?. Kina ganin yadda Amira take yin komai wajen ganin ta farantawa mahaifiyarta, ba ta taɓa yi mata jaura ta dawo mata da shi ba face ta sai ta sayar da shi tas komai yawansa. Shin ke hakan bai ishe ki ishara ba? Ban da rashin zuciya irin naki ke ko wani abu ba kya ji a zuciyarki game da ita?".
Ji nayi kaina ya soma juyawa jiri yana ƙoƙarin kai ni ƙasa. Ban taɓa zato da tsammanin haka Umma ta ɗauki wannan abun azimun ba. Na gaza cewa komai illa hawayen da suka soma gudun famfalaƙi akan kuncina. Da ƙyar na furta"Umma ki yi haƙuri". Na ƙare zancen cikin raunin da ya bayyana har a muryata ina durƙushewa akan gwiwoyina na riƙo ƙafarta.
Tsawon wasu mintuna ba ta ce da ni ko kanzil ba sai da na cire tsammani da samun amsa daga gare ta kafin ta furta zancen da ya girgiza ni ainun.
"Babu wani zaɓi Amatullah dole ne ki yi amfani da wannan laƙanin. Ga shi nan kamar yadda kike kallo kwalli ne sai kuma turare, a duk san da za ki fita talla za ki saka kwallin a idanunki turaren kuma za ki turara kayan tallan da su. Malam ya ba ni tabbacin matuƙar kika yi hakan ko talla dubu ɗari kika fita da shi sai ya ƙare tas kamar yadda wuta take cinye auguda cikin ƙiftawan ido. Amatullah idan kina da hankali da hangen nisa yadda Amira ta zama cinye du kaɗai ya ishe ki ishara kuma hakan ya isa ya zaburar da ke wanda ke da kanki za ki ce na je na nemo miki wannan laƙanin".
Tunani gabaɗaya ya tsaya cak bugun zuciyata ya tsananta. Gaɓoɓin jiki gabaɗaya suka yi sanyi na kasa motsa su. Ina ji ina gani ta zare ƙafarta daga riƙon da na yi mata ta bar ni yashe a wajen. Cikin rashin kuzari na tashi na yi sallan asr na kwanta a inda na yi sallan ina jin zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin rufe ni.
Shiga goma fita goma Umma ba ta ce da ni ko kanzil ba har aka yi ƙiran sallan magrib, a zaune na yi sallan na ci gaba da zama a wajen na kafa kai da gwiwa. Ina karanto karantun al'ƙur'ani a cikin zuciyata. Kamar a mafarki na soma tsinkayo amon Umma a kusa da ni, sautin da kunnena yake tantance mini shi ya tabbatar mini da a kusa da ni take zaune.
"Amatullah".
Ta ƙira sunana cikin wata iriyar murya na amsa ba tare da na ɗago kaina ba. Hakan bai ɗaɗata da ƙasa ba ta ci gaba da maganarta.
"Ki buɗe idanuki ki kalli abubuwan da suke faruwa a duniyar zahiri. Me ye Amira ta fi ki da shi kyau, diri, sura, asali, zaƙin murya ko kuma sa'a ta fi ki? A bayyane yake duk waɗannan abubuwan da na lissafo kin fi Amira su ban da abu ɗaya shi ne sa'a. Kuma shi ma na yi alwashin sai kin fi ta shi".
Muryata a dushashe na ɗago kaina ina faɗin"Umma da kin fara nazari akan hanyar da Amira take bi wajen sayar da tallanta domin shi ne gaba da komai. Wallahi kin ji na rantse miki samari ne suke yi mata juye kuma su suke ba ta maƙudan kuɗaɗe har wayan da yake hannunta saurayi ne ya ba ta. Babu wani sa'a da take tare da shi haƙiƙanin gaskiya kamun kai ne ba ta da shi".
Kallon da ta kafe ni da shi ya tilasta mini mayar da ƙwayoyin idanuna ƙasa ina sauraran abin da yake faɗi a zafafe alamar ta soma fusata ta kuma zo har wuya.
"Yau ina ganin ikon Allah wai na zaune ya faɗi, Amatullah har ke za ki zaunar da ni kina gaya min abin da ya dace na yi?. Ƴar iskan yarinya marar kunya to ko karuwanci za ki yi sai kin kawo min kuɗin tallan kununa babu gara bin zago, wallahi ba zan ƙara ɗaukar asara ba tun da na lura ba mutunci ne da ke ba shegiya mai mataccen zuciya". Duk yadda zuciyata ta so ba ta haƙuri cikin ƙasƙantar da kai bakina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen furta abin da yake kan harshena, haka ta gama ta tashi ta shiga kicin. Na kasa motsawa daga wajen gabaɗaya na gaza gane abin da yake yi mini daɗi cikin duniyar. Ina jin sallamar yaran da nake yi wa darasi a ƙofar ɗakinmu amma na kasa amsawa balle har na tashi na ji da me ye suka zo, har Umma ta fito ta fararraƙe su suka tarwatse a haka Abba ya dawo ya same ni na ji jugum kamar majinyaciya.
Babu nau'in tambayar da bai yi mini ba amma na ce da shi babu komai da ya matse na ce kaina ne yake ciwo. A daren ta fita kemis ya karɓo mini magani na sha sannan na kwanta. Haka na yi ta juyi don bacci sam ya yi ƙauracewa idanuna suna nan ƙamas kamar na kifin da aka tsoma a cikin ruwan mai aka tsamo. Haka na yi ta juyi har aka ƙira sallan assalatu na tashi da ƙyar saboda mutuwan da jikina ya yi na gabatar da sallan a zaune.
A ɗaki ya na ci gaba da zama saboda ruwan da aka soma yi kamar da bakin ƙwarya bai tsagaita ba har sai ƙarfe takwas saura. A lokacin na yi ƙarfin hali na bayyano waje na haɗa wuta wanda sai da na ci kwakwa kafin ya ruru na ɗaurawa Abba abin kaci. Kunnu na dama na ɗumama sauran tuwon dare ba kai masa har zan tashi ya dakatar da ni na koma na zauna kaina a ƙasa ina sauraronsa.
"Amatullah tun daren jiya na lura da yanayin da kike ciki tabbas akwai wani abun da yake faruwa. Shin mene ne ki sanar da ni komai kar ki yi ƙoƙarin ɓoye min".
Sai da na sauƙe gwauron ajiyan zuciya kafin na sama zarafin cewa"babu abin da yake faruwa Abba, kamar yadda na sanar da kai jiya kaina ne yake yi mini ciwo. Bayan hakan babu komai".
Ya kafe ni da kallon da ya fi kama da na tuhuma duk da idanuna suna ƙasa amma tabbas jikina ya tabbatar mini da irin kallon da yake yi mini, shuru ya ratsa wajen kafin can ya zarce da cewa"ba na son kin sanya kanki a ciki damuwa Amatullah. Ki
ƙara haƙuri akan wanda kike yi kuma na san ki da shi in sha Allah za ki ga riban hakan ko ba daɗe ko ba jima".
"Ai dole ka zaunar da ita a nan kana biya mata zancen banza da na wofi har da cewa wai ta ƙara haƙuri. Ai dole ka ce ta yi haƙuri tun da cutar da ita nake yi ko kuma ka ga alamar ina gallaza mata. Ka taɓa shigowa gidan nan ka gan ta a wulaƙanci ko ka ga alamar yunwa ko ƙishi a tattare da ita?. Ƴar iska mai baƙin hali ke kuma har da wani zama ki sadda kai ƙasa kina sauraronsa shegiya munafuka kawai".
Tsam! Abba ya miƙe akan ƙafafunsa ya yi taku uku ya isa dab da Umma ya nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa yana cewa"Hafsatu kar ki ƙara cewa yarinyar nan ƴar iska balle har ki yi gangancin sheganta ta. Ki kiyaye ranar da za ki kai ni bango, na fara gajiya da halinki fa".
"Manniru ban ga dalilin da za ka zaunar da Æ´arta kana aibata ni a gabanta ba kuma na zuba ido na yi shuru. Wallahi ka yi tsararo".
Cike da takaici Abba yake jinjina kansa"Hafsatu ki kiyaye harshenki Manzon Allah ya ce"kuffa alaika haza" ku kiyaye wannan a gare ku. Ki dinga tauna magana kafin kin furta ta domin masu iya magana sun ce magana zaran bunu ce in har ta fita ba a mayar da ita". Ya sausauta amon muryarsa kafin ya ci gaba da magana"na roƙi ki zubar da waɗannan halayen ki zo mu zauna mu ba wa ƴarmu ɗaya tilo tarbiyyar da ta dace. Na yi muku alƙawarin ba ku kula daidai ƙarfina samun aljihuna".
Dariyar da Umma ta ba she shi ya sanya Abba dakata wa ba don ya gama bayyanar da takaicin da yake cikin ransa ba.
"Alamar ƙarfi ai tana ga mai ƙiba Manniru. Na tabbatar ko zuciyar da take dashe a cikin ƙirjinka ba ta yarda da zancen bakinka ya furta ba. Yanzu kai ko wani ne ga tare ka a hanya ya ce kai Manniru za ka iya ɗaukar ɗawaniyyar iyalinka sai ka yarda?. A aikinka na maluntan ne za ka ɗauki nauyinmu?Shekarunmu nawa tare amma har yanzu ko gidan kanka ba ka mallaka ba ban da keke mai kake da shi a duniya?".