Sashe 22
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina rufe bakina yana isowa wajen ya zauna a kan bencin da yake fuskantar mu. Ya soma zuba kamar bishiyar magarya.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yake da ikon juya dare zuwa safiya. Kuma ya yi mini tagomashin yin tozali da kyakykyawan suranki a matsayi abin mafi kyau da burgewa da na fara gani a wayewar garin yau. Da ke da na kwana a cikin ƙirjina shi yasa yau na yi ƙudurin zuwa na ganki kafin na aiwatar da dukkan ayyukan na ranan yau".
"Kan bala'i! Bash yana kashe wuta ina bin ka da fetur. Irin wannan kalaman tashin kai haka ai ni da nake gefe ma kana sawa na fice daga cikin duniyar balle ita kuma wacce ake yi domin ta".
"Babbar yarinya ke dai ki kawai lamarin ya wuce duk yadda kike tunani da zato a cikin zuciyata. Ban taɓa ɗanɗana garɗin soyayya ba sai yanzu da na faɗa kogin soyayyar Amatullah".
Raina ya cika fam zuciyata tana tafasa tamkar talgen da aka aza a bisa wuta, na gaza cewa da su komai illa hararar da nake banka musu a faƙaice.
"A zuba min kunun. Don yau na yi wa kaina alƙawarin ba zan sha komai dangin abin sha ba sai na fara shan wannan daddaɗan kunun nakin, ya ke Gimbiyata".
"Na nawa kake so?".
Na furta zancen a zaffafe kamar zai kai masa duka. Hakan ya sanya Amira kallo ni tare da faɗin"Haba! Amatullah ya haka kamar da gaba? Ki tuna wanda ya ce yana sonka fa, komai lalacewarsa ya fi maƙiyi".
"To laifi ne don na tambaya na nawa yake so?". Ta jijjiga kanta alamar a'a tana ƙunshe dariyar da yake son kufce mata.
"Ban so kika dakatar da ita ba, ko kalmar zagi da cin mutumci ne zai fito daga bakinta ina son na ga waɗannan kyawawan leɓan natan suna motsawa. Ki ba ni na ɗari biyu".
Ban tanka masa ba na zuba masa na dosara masa a gabansa. Ya É—auka yana sha yana ta suturan da sam ba na gane kansu balle gindinsu, da na ga zaman ba zai fishshe ni ba na amshi wayar Amira ina kallon hotuna.
Muna zaune har masan ya ƙare duk wanda ya zo sayan kunun ya yi mini wata maganar ko ya yabi surar jikina, sai na fasa sayar masa na kuma buga masa rashin mutunci. Hakan ya sa ban yi ciniki da yawa ba.
"Bari na kai wa Naziru masarsa". Na bita da kallo yayin da take miƙewa tana ɗaukar take away ɗin. Na janye hannuna daga tagumin da na zagba kafin na sama zarafin faɗin.
"Ni fa Amira na lura zaman cikin tashan nan ban gishiri a baka manda ne. Sai ka mayar da kanka bolar da kowa ta kwaso jujinsa zau juye akai. Allah ya sani ba zan iya wannan rayuwar ba".
Ta tsaya tana kallona"bari na je na dawo sai mu yi magana. Kar na bar shi yana jira na". Tana dire zancen ta juya ta bar wajen wanda hakan ya yi daidai da sauƙe sakakken ajiyar zuciyar da na yi ina zabga wani uban tagumi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa.
"Yan mata adon gari idan ba ku gari ya ɓaci idan kuka yi yawa gari ya ɓaci". Kalaman da suka dira a ƙofofin kunnuwana kenan da suka tursasa mini ɗago kaina ina ƙarewa mutumin kallo tun daga sama har ƙasa. Babban mutum ne wanda a ƙalla zai kai sa'an Abbana a kwanakin duniya ya yi shigar kamala cikin cikakken jamfa har ƙasa ga jakar kaya riƙe a hannunsa.
"Me ye kike tsayarwa ne ƴan mata?". Ya kuma jefa mini wani tambayar a karo na biyu har lokacin idanunsa ƙar a kaina ba ya ko ƙiftawa.
"Kunu ne. Na nawa za a zuba maka?".
"Ga shi kuma ni ba na shan kunu. Sai dai na sha mai tsayar kunun".
Tsam! Na miƙe kamar wacce aka tsigarawa alluran doki na tsaya ƙyam akan ƙafafuna duk da rawar da suke yi mini tsabar firgicin da zancen nasan ya jefa ni a ciki.
Muryarta har sarƙewa yake yi idanuna yana kawo ruwa na soma faɗin"wani irin banzan magana ne wannan bawan Allah?. Babban mutum ne kai don haka ka ja girmanka don billahillazi idan ka yi gigin zubar da ni babu abun da zai sa ba zan sanya ƙafa na tatttake sa ba. Ni ba iskanci ne ta fito da ita daga gidanmu ba face sana'a".
Kafin na rufe bakina na ji ya ɗauke ni da mari kafin na yi aune ya ƙara sauƙe nuni wani marin a karo na biyu na ɗayan kuncina. Na ɗago kaina a gigice sai dai kafin na sama zarafin cewa wani abun tunin ya tari numfashina.
"Ke yarinya kar ki sake ki yi min rashin kunya irin na ku na Æ´aÆ´an zamani. Ni nan da kike gani na shekaruna É—aÉ—É—aya shekaru sittin da biyu a duniya. Jikata da farko yanzu haka tana gidan aurenta har da Æ´aÆ´a, da kina da mutuncin ni É—in nan na matsayin uba ya kamata ki kalle ni".
Na dafe kuncina raina cike da fal da takaici. Ƙirjina yana dakan lugudan tara-tara sau goma sha tara. Ruwan da ya wadaci kurmin idanuna suka kwaranyo akan kuncina.
"Ai ba ka riƙe girmanka ba ne shi yasa har na sama fuskar gaya maka ko wani irin magana". Na yi maganar jikina har ɓari yake yi tsabar ɓacin rai da ƙuncin da nake cikinsa. Kafin ka ce kwabo mutane sun cika a wajen kamar kai ka ce kisan kai aka yi a wajen ko kuma wani babban laifi.
Girmamawa da mutuntawan da duk wanda ya zo wajen yake yi wa mutumin shi ya fi komai ɗaure mini kai da jefa ni cikin kokonto. Wasu har tsunguwana suke yi har ƙasa kafin su gaishe shi ko ya miƙo musu hannu don su yi musabaha ba sa miƙa nasu.
"Wai me ye yake faruwa ne ya Sheik? Me ye ya haÉ—a ka da wannan yarinyar?". ÆŠaga daga cikin mutanen da suka cika a wajen ya jefawa mutumin tambaya kafin ya amsa masa wani ya amshe zanen ya soma furzar da zancen da yake cikinsa cikin tsananin fusata, tamkar zai kai mini bugu.
"Allah dai wadaran naka ya lalace. Yanzu ke don fitsara da rashin kunya ki dubi tsabar idanun wannan mutumin da ya yi kusan jika da ke kina yi masa rashin kunya irin na ku na Æ´aÆ´an zamani. Ke kam alla wadaran halinki hakan ya nuna ba ki sama kyakykyawan tarbiyya ba a gida".
"Alhaji Mamman ka yi haƙuri mana mu ji ta bakinta. Kafin mu yanke hukunci".
Ɗaya daga cikin mutanen wajen ya furta kafin ya juyo yana dubana tare da faɗin"ke yarinya me ye haɗinki da wannan mutumin kar kika nema ki yi masa raini da rashin kunya". Duk yadda na so na yi magana lamarin ya gagara hawaye ne kawai suke gudun famfalaƙi akan kuncina na kasa furta ko da kalma guda.
Ana cikin haka Amira ta dawo ta tambayi me ke faru aka mayar mata da ba'asi ita ta yi ta masu haƙuri, amma da farko tsayawa suka yi tsayin dakan akan sai sun lakaɗa mini na jakuna. Yayin da manyan wajen suke ta ba wa mutumin haƙuri kamar wanda aka yi mata wani gagarumin zunubi. Da ƙyar Amira ta shawo kansu shi ma sai da taimakon samarinta na wajen da suka sanya baki.
Ƙurar tana lafawa na fara harhaɗa kayan tallana, Amira ta riƙe ni tana jijjiga ni"wai Amatullah me ye yake damunki ne? Hauka kika yi ko kuma aljanu ne suka shafe ki?".
Na kawar da hawayen idanuna kafin na sama lasisin faÉ—in"babu ko É—aya kawai tafiya zan yi ne".
"To ki tsaya mu nema almajirai su É—eba mana kayan mana". Ban kula ta ba na ci gaba da tattare tattaren da nake yi. Ta nema almajirai suka É—eba mana kayan muka bar wajen har yanzu hawaye ba su daina kwaranya daga idanuna ba.
"Don girman Allah ki nutsu ki daina wannan kukan haka ya isa mana. Ki bari mu je gida mu zauna sai mu tattauna akan lamarin".
Na shece majinan kukan da ya zo mini kafin na ce"Amira ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba har sai na san wane ne wannan mutumin, da ya ƙware a munafurci da launa zance". Kafin na gama ta yi saurin kai tafin hannunta ta rufe mini baki.
Kamar mai raɗa ta soma cewa"ke Amatullah ki rufa mana asiri, kar wani ya ji ki kina wannan maganar. Kin san waye wannan mutumin kuwa? To idan ba ki sani ba ki saurara ki ji wannan mutumin sunansa Sheik Dawood Nasarawa babban malamin addini ne a jihar nan da ma kewayenta, ya yi shura sosai a fannin ilimin addini da sanin hukunce-hukuncensa. Sannan kuma malamin jami'a ne a babban jami'in jihar na koyar da kimiyya da fasaha kuma na ji an ce ma ba a iya wannan jahar yake koyarwa ba. Kin gan sa nan babu wani abun duniyar da za a ba shi ta ruɗe sa haka nan babu adadin kuɗaɗen da za a ba shi a rinjayi hankalinsa, kin gan sa nan ko motar kansa bai da shi. Duk wani shugaban da ya yi ba daidai ba ga al'ummarsa ba ya ragar masa fitowa yake ya tsigale shi ba tare da fargaba ko tsoron abin da kan je ko ya dawo ba. Da yawan mutanen suna yi maka kirari da murucin kan dutse ba ka fito ba sai da ka shirya wasu kuma su ce da shi gaskiya dokin ƙarfe".
Ba kaɗan ba kalaman Amira suka daki ƙwaƙwalwata tare da munana ƙalbina. Take yanke zuffa ya soma tsatstsafo wa daga jikina. Na yi maza na cafko hannunta na riƙe gam saboda rawar da ƙafafuna suke yi.
"Ki na nufin wannan mutumin shi ne Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe?". Na galla mini harara"ƙwarai kuwa shi ne".
Na dafe kaina ina karanto auzila kafin na ci gaba da magana cikin tsananin kaÉ—uwa da ruÉ—ewa.
"Na daÉ—e da sanin muryarsa babu wani malamin da nake bibiyar wa'azinsa kamar sa. Hatta Abba yana son wa'azinsa saboda yadda yake feÉ—e gaskiya komai É—acinta".