Sashe 32
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Don Allah ki kwantar da hankalinki babu komai fa,Anty Sawwaman ma fa yanzu na ga ta fito za ta tafi".
Na zabura na miƙe zan fice Amira ta riƙo hannuna ta riƙe gam" ina kuma za ki je?".
"Zan je wajen ta ne kafin ta tafi mana".
Ta gizgiza mini kanta"bai kamata ki je yanzu ba Amatullah. Idan maganar da suka tattauna ta shafe ki to ko ba ki je ba za a ƙira ki, amma tun da kika ga ba a neme ki to maganar ba ta shafe ki ba ne ta kowacce fuska".
Cikin sanyin jiki na koma na zauna tare da buga wani uban tagumi, ganin yadda Amira ta dage ita da Ummanta wajen kwantar mini da hankali hakan ya sani dole na saki fuskata ba don na daina jin raɗaɗi da zogi a cikin raina ba. Haka kawai na ji gabaɗaya zaman gidan ya ishe ni har yunƙurin ƙiran Anty Sawwama na so yi da wayar Amira sai dai ban haddace lambarta a kaina ba haka dole ina ji ina gani na haƙura.
Umma ta soma ƙwala mini ƙira tana shelanta mini na fito na gama dama kunnun, sai da na yi wanka na shirya kana na ɗauki tallan muka fito tare da Amira yayin da almajirin da yake tafiya mana da kayan ya yi gaba.
Inda muka saba zama kamar kullum yau a nan muka yada zango, ba mu yi awa guda cikakken ba muka sayar da komai.
"Bari na yi sauri na je na kai wa Naziru masarsa kar ki gaji da zaman".
Amira ta yi zancen tana miƙewa tsaye, taɓe baki na yi ina faɗin"ni yau gabaɗaya ma wallahi ba na sha'awar komawa cikin gidan nan. Don tashin hankalin cikinsa ya fi komai yawa".
"To Amatullah ya ya za mu? Tun da ƙaddara ta jefo nan kam ai haka za mu yi haƙuri".
Haka kawai na ji wani sanyi a raina da na hango Bashir yana nufo wajen har sai da na kasa haƙuri na fito da abin da yake raina, wanda ni ma kaina ban taɓa zato da tsammanin bakina zai iya furta makamancin irin wannan kalamin ba.
"Yauwa! Ga can Bashir ma yana tahowa, za mu yi hira da shi kafin ki dawo don na lura mutumin akwai shi da barkwanci".
Sakeke Amira ta yi tana kallona hakan ya sani ankara da fahimtar cewa na kwafsa, sai dai ban bari na bugo jirgin nawan da wuri ba na yi wuf na gyara maganan.
"Malama ni fa ba wani abu nake nufi ba don na ga kina ƙoƙarin fassara ni ta wani fuskan daban".
Ta sheƙe da dariya mai isarta sai da ta tsagaita kafin ta ce"a yi dai mu gani in tusa tana hura wuta".
"Ni fa ba abin da kike nufi ne a cikin raina ba. Kawai ba na son komawa gidan nan yanzu gabaÉ—aya shi yasa". Ta yarfa hannayenta alamar babu abin da ya shafe ta da abin na furta, daidai lokacin da Bashir ya iso wajen bakinsa har kunne.
[10/1, 1:48 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 2ï¸âƒ£5ï¸âƒ£
"Barka da warhaka yake tauraruwar da ke haska ilahirin birnin zuciyata. Ban san yadda zan kasancewa a duk lokacin rana ta fito ta faɗi ba tare da na yi tozali da wannan kyakykyawan fuskarta kin ba, da ke nake kwana a cikin raina haka zalika da ke zan farka ƙunshe a ƙirjina, zan so ki ba ni dama don na nuna miki ainihin yadda nake yi akan ki Amatullah".
Na tallafe kuncina ina kallonsa tare da cewa"to wani irin dama kake buƙata daga gare ni ya kai bawan Allah?". Da alama maganar tawa ta haifar masa da wanzuwar farin ciki a cikin ransa da har sai da ya bayyana ɓaro-ɓaro a bisa fuskarsa.
"Ki ba ni dama shiga cikin zuciyarki ni ma na yi miki alƙawarin wadata da dawwammen farin ciki kuma ba zan taɓa sanya ta yi dana sanin zaɓina ba".
Na saki taƙaitaccen murmushi kafin na sama damar cewa"ga shi kuma babu abin da yake zama dawwammen a cikin duniyar gabaɗaya, face ikon Allah". Ya ɗan rusunar da kansa ƙasa yana sosa ƙeyarsa haɗe da cewa"to na ji amma na ba ki tabbacin ba za ki taɓa yin kuka ba idan ina kusa da ke".
"Ikon Allah sai kallo wai na zaune ya faÉ—i. Amatullah ke ce dai wacce na sani ko kuma gizo idanuna suke yi min?". Amira ta yi furucin cikin zallan mamaki da al'ajabina.
Na yi fari idanuna kafin na furta"wai daman ba ku tafi ba ne? To dai ki yi sauri don ba zan tsaya jiranki da yawa ba". Ta sheƙe da dariya haɗe da cewa"wannan kuma zance kike yi". Tana dasa aya a nan ta juya ta tafi kai wa Naziru masarsa.
"Ina so ki ba ni dama a yau domin na fallasa sirrin zuciyata izuwa na ki zuciyar. Don so nake yi na tabbatar mata da cewar ta sama abokiyar rayuwa na har abada wacce ba ta san komai ba face so da ƙaunarta".
Kalaman Bashir kenan da suka yi silar dawo da idanuna kansa. Har yanzun fuskarsa ɗauke da maɗaukakin annuri haka kawai na ji na tsinci kaina da kallon fuskarsa da take zagaye da kwantaccen saje baƙi wuk da shi har wani sheƙi yake tamkar yana shafa masa mai.
"Tafi kanka tsaye wajen isar da saƙon da yake ƙunshe a cikin zuciyarka".
Da alama ya ji daɗin zancen nawan, ya gayara zaman yana fuskanta na da kyau kafin ya soma zubo jawabi babu ƙakkautawa. Yi kawai yake yi ina ji da sauraronsa yayin da na gaza ɗauke idona daga gare sa har ya kai aya wanda hakan ya yi daidai da canzuwar bugawar zuciyata da hakan ya haifar mini da runtse idanuna.
"Tauraruwata lafiya kuwa? Na ga gabaÉ—aya yanayinki ya sauya".
Na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na ce"ba komai". Ya yi hanzarin katse ni"ai kuwa yanayin ki ya nuna cewar akwai wani abu da kike ɓoyewa. Sanar da ni mene ne? Don yanzu zuciyata da taki sun zama aminan juna babu abin da za mu ɓoyewa junanmu".
Ya ƙare zancen yana ƙara matso da bencin da yake zaune a kai kusa da ni, na cira kai na yi masa wani irin kallo da ya sanya sa shan jinin jikinsa.
"Na ce maka babu koma ko za ka yi mini dole ne?". Na yi zancen fuskata a É—aure mur tamkar magribar É—inya.
"Ki yi haƙuri ba nufina kenan na ɓata miki rai ba". Ban tanka masa ba na miƙe na soma harhaɗa kayanmu, ina cikin aikata hakan Amira ta dawo.
"Har kun gama hirar da ku kenan? In kuma ba ku gama sai na koma na ba ku waje".
Na wurga mata harara da wutsiyar idona"in za ki zo mu tafi ki zo. In kuma ba yanzu za ki tafi ba sai ki sanar da ni". Maimakon ranta ya ɓaci bisa yanayin da na yi mata maganar sai ma murmushin da ta saka ta ce"daɗina da ke saurin hawa Amatullah. To haɗa kayan sai mu tafi". Muryar Bashir ta katse ni daga tattare kayan da nake yi na tsaya cak.
"Ki yi haƙuri idan ni na ɓata miki rai, na roƙe ki har ki azabtar da zuciya da ruhina ta wannan hanyar".
Haka kawai na ji gabaɗaya ilahirin jikina ya yi sanyi ƙalau na ja dogon numfashi na fesar kafin na waigo, na yi turus ganinsa durƙushe akan gwiwoyinsa. Na runtse idanuna ina faɗin"don Allah ka tashi kar mutane su ganka haka".
Ya marairaice murya"ba zan tashi ba har sai kin tabbatar min da cewar ba ni na yi silar canzuwar yanayin fuskarki ba Amatullah".
Banza na yi da shi ba tare da na ce da shi uffan ba na ci gaba da aikin gabana sai da na haɗa kayan tsaf, almajirin da yake ɗauka mana kayan ya zuba su a wheelbarrow ya yi gaba da su. Ganin Amira ba ta da niyyan tafiya hakan ya sani jan hannunta muka bar wajen har mun yi nisa sai na ji ta tsaya cak ba ta tafi, na ja hannunta ta ƙi motsawa hakan ya sani waigowa don ganin abin da ya hana ta tafiya.
A zafafe na soma cewa"me ye hakan Amira ina jan ki kina turjewa? In ba tafiya za ki yi ba ai sai ki sanar da ni". Ta jijjiga mini kanta alamar duk abin da na faÉ—a ba su hau gwadaben dalilin da ya hana ta tafiya ba.
"Amatullah don Allah ki duba lamarin Bashir, na yi wa masa farin sani kuma duk wanda zai ba ki labarin halinsa to a bayana yake. Ban taɓa jin ya furtawa wata mace kalmar so ba a kaf cikin tashar nan sai ke, ina da tabbacin da dukkan zuciyarsa yake sonki. Duba ba fa ki ga tun ɗazu yana kan gwiwoyinsa bai tashi ba".
A faƙaice na juya na kalle shi har yanzu yana durƙushe akan gwiwoyinsa bai gusa ba. Tagwayen ajiyar zuciya na sauƙe ina dafe goshina saboda sarawan da kaina yake yi mini tamkar zai tsage gida biyu. Ban ce da ita komai ba na koma wajen Bashir na tabbatar masa da cewa ni bai yi mini komai ba.
"To indai har ki na so na yarda da duk abin da kika furta sai ki yi min wani alƙawarin guda".
Na ware idanuna"wani irin alƙawarin ne haka? Faɗi ko mene ne matuƙar bai fi ƙarfina ba zan yi maka shi Bashir".
Sai da ya gyara tsayiwarsa kafin ya ce"ina so yi min alƙawarin gobe za ki ba ni lokacinki don mu tattaunawa". Ba tare da tunanin komai ba na tsinci kaina da faɗin"in Sha Allah na yi maka wannan alƙawarin". Cike da jin daɗi ya amsa da cewa"to ina godiya, mu je na yi muku rakiya ko?".
Na jijjiga kaina"ba buƙatar hakan, kai dai kawai ka koma wajen sana'arka".
"To shikenan yadda kika ce haka za a yi ranki a daÉ—e". Murmushi kawai na sakar masa na bar wajen muka ci gaba da tafiya tare da Amira. Har mun yi nisa da tashar na tsaya.
"Lafiya kuma kika tsaya?". Amira ta jefa mini tambayar cikin zaƙuwar son jin amsa daga gare ni.