← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 58

Sashe 45

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ja dogon numfashi ta fesar kafin ta soma cewa"Ramlatu ƴar ƙanina ne da iyayenta suka rasu tun tana jaririya, ni ce na raine ta da hannuna har ta girma kuma na ba ta mummunan tarbiyan da yanzu haka take kan gwadabensa. Mus'bahu wani saurayinta ne da ya yi hidima da ita tun zamanin ƙuruciyarta har ta riƙa ta zama cikakkiyar budurwa sun yi soyayya da shi na bugawa a jarida kafin daga bisani masu hannu da shuni suka soma danno gare ta, a lokacin ne hankalinta ya karkata zuwa gare su har ta zaɓo ɗaya daga cikin su ta tura shi can ƙauye ya magantu da manya. Tun daga wannan lokacin ta fara wasan ɓoya da Mus'bahu don ya yi ikirarin cewar idonsa idonta sai ya lahanta ta ko kuma ya gurgunta mata rayuwa, sai dai ban taɓa kawowa a raina cewar yana da wannan mungun nufin a cikin ransa ba. Amatullah ƙaddara Ramlatu ce ta faɗa akan ki". Wani zazzafan kuka mai sauti na fashe da shi tabbas na yarda ƙaddarar bawa ba ta wuce ranarta sai dai ban taɓa tunanin ta wa ƙaddarar za ta zo a irin wannan siffan mai muni ba.
Duk su biyun suka haÉ—u suna rarrashina amma na kasa tsayar da kukan da nake yi, tausayi da tunanin halin da Abba zai shiga shi yake ta kai kawo a cikin birnin zuciyata yana yi mini yawo a cikin kwanyata.

Haka muka kwana da idanunmu har aka yi ƙiran assalatu Hajiya Tasalla ta ƙara dafa mini ruwan zafi na shiga na yi wanka, tun kafin gari ya gama wayewa na zara hijabi na kallo Amira da ta buga tagumi na ce"ki tashi mu tafi in kuma ba yanzu za ki tafi ba. To ni kin ga tafiyata".

Ta yi sauri ta riƙo ni"don girman Allah ki yi haƙuri ki bari tukunnan mu ƙara ganin yanayin jikin nakin zuwa nan da gari ya yi haske".
"Amira ki bar ni na tafi kawai". Na yi zancen ina fizge jikina daga riƙon da ta yi mini. Na durƙushe a ƙasa ina hawaye tare da sumbatu.

"Amira da kin san yadda nake ji a cikin zuciyata da ke ce mutum na farko da za ki fara taimaka mini da hanyar barin cikin gidan nan. Ashe akwai irin wannan baƙar ranar cikin ranakun rayuwata? Ashe duk yadda nake tattali da killace mutumcina wani wanda shari'a ba ta mallaka masa ni ba zai rusa mini dukkan tanadin da na daɗe ina yi a rayuwata. Amira da wani idon zan kalla Abba?".

"Ai ba za su taɓa sanin abin da ya faru ba ma har abada". Na kafe ta da ido don na kasa cewa komai sai da na fizgo numfashina da yake maƙale mini a ƙirji kafin na zama zarafin faɗin"ke ma kin goyi bayan abin da Tasalla ta faɗa kenan?".

"Ba wai ina goyan bayan ta ba ne ina dai goyan bayan abin da zai siya miki mutunci ne Amatullah. Haƙiƙa idan maganar nan ta fita ba ke hatta ni ma na kaɗe balle kuma iyayenmu don shiga cikin jama'a ma sai ya gagare su, an dinga yi musu zumɗe kenan ana nuna su da baki tamkar watan Ramadana. Ki yi haƙuri ki karɓa ƙaddarar da ta faɗa miki, na tabbatar ko a wajen Allah ba ki da laifi don ba son ranki hakan ya faru ba. Kowani bawa da irin na sa salon ƙaddara ke ma kuma ta wannan fannin Ubangiji yake son ya gwada ƙarfin imaninki".

"Ko zan ɓoyewa kowa ba zan iya ɓoyewa iyayena ba".
Ta zo dab da ni"za ki iya matuƙar kika sa a ranki cewar za ki yi hakan. Yanzu dai ki bari gari ya ƙara waye wa sai mu tafi". Na gaza cewa da ita komai illa kukan da na ci gaba da ni, a haka Hajiya Tasalla ta shigo ta same mu ta kawo mana abincin karin kumallo sai dai gabaɗayamu mun kasa cin komai, da kanta ta je ta sayi maganin da aka rubuta ta kawo mini, da ƙyar Amira ta lallaɓa ni na sha maganin muka fito za mu tafi, har zaure Hajiya Tasalla tako mu tana jeranta mini sannun da ko kallon arziki ba ta ishe ni ba balle na amsa mata.

Muna shawo kwanar da za ta sada mu da gidanmu muka hango Abba tsaye a ƙofar gidan, sai waige-waige yake yi. Cak na tsaye ina lalumo hannun Amira yayin da hawaye suka ciko mini kurmin idanuna.
[10/21, 5:05 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

____________________________________

Page 3️⃣3️⃣

Amira ta riƙe hannuna gam"don girman Allah Amatullah ki nutsu kar ki tona mana asiri, kar ki bari ya gane da wani abu".
"Na shiga uku kin ga fa Abba ne tsaye".
"To don Abba ne sai me ye? Ki nutsu dai kawai ke kam kar ki yi abin da zai gane cewar wani abu ya faru". Ban kuma cewa da ita komai ba na goge fuskana da hawaye suka ɓata mini shi kana mu ka ci gaba da tafiya har zuwa lokacin hannuna yana cikin nata.
Muna doso wajen muka haɗa ido da Abba ya sauƙe wani ƙatuwar numfashi yana kafe mu da idanu.

"Uwata sai yanzu kuka dawo, a ina kuka tsaya?". Kafin na yi magana Amira ta yi hanzarin karɓe zancen cikin faɗin"Abba ba sa buɗe gidan da wuri ne shi yasa. Don a cewarta babu wanda zai fita sai gari ya yi haske ido na ganin ido". Ya yi ɗan jim tamkar yana nazarin wani abun kafin can ya ce"shikenan tun da kun dawo cikin ƙoshin lafiya alhamdulillah, amma dai ku daina tsayawa a ko'ina. Ku wuce ku shiga ciki".

"To in sha Allah". Muka haɗe baki wajen amsawa, muka soma tafiya ina jan ƙafana a hankali saboda ciwon da gabaɗaya jikina yake yi mini. Cak duk mu biyun muka tsaya bisa zancen da Abba ya furta da ya kusa tarwatsa zuƙatanmu.

"Uwata lafiya na ga ki na tafiya kina ɗingisa ƙafa?". Take gumi ya keto mini jikina ya soma rawa cikin in'inar da ban san ina yin ta na soma cewa"daman-daman-daman Abba...". Ban ƙarisa ba Amira ta yi caraf ta amshe zancen cikin hanzari.
"Abba zamewa ta yi a banɗaki shi ne ta bugu". Cike da tausayi da jin ƙai Abba ya furta"subhanallahi! Sannu ba ki dai ji ciwo ba ko?". Na runtse idanuna a ƙoƙarin hana hawayen da suka ciko mini koramar idanuna samun damar kwaranya.

"Ban ji ciwo ba Abba akwai bugu na yi a ƙuguna". Na yi zancen cikin sanyin jiki da na murya.
"Allah ya kiyaye na gaba. In sha Allah in zan dawo zan taho miki da magani sai ki sha kin ji?". Kaina kawai na sama damar gyaÉ—a masa na yi masa fatan a dawo lafiya ya tafi yayin da mu kuma muka shige ciki.
Muna shiga zaure na sulale a ƙasa saboda wani ƙarƙarfan kukan da ya yanko mini, Amira ta dafo kafaɗuna haɗe da faɗin"don Allah Amatullah ki yi haƙuri wannan kukan da kike yi fa ba shi zai gyara abin da ya riga ya afku ba. Ki nutsu mu yi tunanin hanyar da za mu ɓullowa lamarin nan".

"Allah in wani laifin na yi maka ka jarabce ni ta wannan hanyar, Allah na tuba ka yafe mini".
Na yi furucin cikin ƙanƙan da kai da jingina dukkan lamurrana ga Sarkin da ba shi da abokin tarayya wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. Cikin lanƙwasar da murya da rarrashi ta soma yi mini magiya da ban haƙuri.
"Don Allah ya ya kike so na ya miki ne Amatullah? Na ba ki haƙuri na ƙara ba ki haƙuri amma kin ƙi fahimta ta, abin da ya faru fa ya riga da ya wuce sai dai a kiyaye gaba, yanzu idan wani ya fito daga cikin gidan nan ya gan ki a haka ai shikenan asirin mu ya gama tonuwa".
"Amira kin san yadda nake ji a cikin raina kuwa?". Ba ta bar ni na ƙarisa ba ta katse numfashina ba tare da na dire zancen ba.

"Duk abin da kike ji a cikin ranki ina jin makamancin sa a cikin raina Amatullah. Don Allah ki yi haƙuri ki tashi mu shiga ciki". Tana rufe bakinta muka jiyo sautin muryar Auwal saurayin Ummi ya buga sallama. Zumbur na miƙe ina karkaɗe jikina tare da goge hawayen da suka ɓata mini fuskata.

"Ƴan mata adon gari, Hajiya Amatullahi manyan gari ashe ana ganin ku a cikin duniyar nan?". Ta buga masa harara ina sauƙe numfarfashi na ja hannun Amira muka shige ciki, har muna na ƙoƙarin cin karo da Ummi yayin da take fitowa ta ja gefe ta tsaya tana bin mu da ido tare da riƙe haɓa.

"To ikon Allah! Wai na kwance ya faÉ—i ku kuma fa lafiyarku?".

Cikin mu babu wanda ya tanka mata har ta yi ta gama. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama ƙarfin gwiwan shiga cikin ɗakin mu bayan Amira ta gama ƙara mini ƙarfin gwiwa da ƙarfafa ni. Da sallama na shiga ɗauke a bakina kaina a ƙasa saboda nauyin haɗa ido nake da Umma ma balle kuma Abba da tausayinsa ya gama ragargaza mini zuciyata. Na durƙusa har ƙasa na gaishe ta ba ta amsa mini ba illa mayar da hankalinta da ta yi akan ci gaba da irga kuɗin da take yi.
Na tashi zan shiga ciki na je na kwanta don gabaɗaya ba na jin daɗin jikina ga wani azababben zazzaɓin da yake ƙoƙarin rufe ne lokacin guda. Har na fara tafiya zan doshi hanyar ɗakin ta dakatar da ni ta hanyar faɗin abin da ya gigita dukkan nutsuwar da ya yi saura a gangar jikina, hanta cikina ya haɗa yayin da kaina ya juya jikina ya ɗauki rawa tamkar wacce akan jona wa wutan lantarki, haƙwarana suka datse harshena, yawun bakina ya ɗauke cak kamar rijiyar da ruwan cikinta ya kafe ya tsawon zamani.

"Me ya same ki na ga yanayin tafiyarki ya sauya?".
Chapter 45 · 0% Book details