← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 58

Sashe 43

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dafo kafaɗata cikin son kwanta mini da hankali ta soma cewa". Amatullah ki haƙurƙantar da zuciyarki daga ni har ke ba mu da yadda muka yi iya shi yasa. Kina ganin dai irin rayuwar takurar da muke yi muka iyayenmu duk muna rayuwa ne a ɗaki guda, dole za ta sa mu zuwa ba wai don son ranmu ba". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kafin na furta"haka ne Amira to Allah ya kawo mana mafita cikin sauri".

"Amin ya Allah".

Ta amsa da shi tana tashi ta koma É—akinsu. Ina gama girkin na zubawa Abba na shi na kai masa ciki na ajiye masa a gabansa na fito na ci na wa a waje, na san Umma yanzu sai ta yi niyya take cin abinci don haka na juye ragowar a cikin kula. Na É—auro alwala na shigo ciki har yanzu Abba yana nan inda na bar shi da alama ko buÉ—e abinci bai yi ba balle ya ci.
Na tsuguna a gabansa ina faÉ—in"Abba lafiya kuwa ka zauna ka yi shuru? Ko dai akwai wani abun ne?".

Ya saki sakakkiyar ajiyar zuciyar da har sai da na ji sautin ta kafin ya soma magana.
"Na daÉ—e ban shiga cikin matsanancin tashin hankali irin na yau ba, na daÉ—e ban ga Maman Umar cikin irin yanayin da na gan ta a yau ba. Tun muna yara mace ce mai fara'a da sakin fuska mace ce mai son nata akan komai da kuma son É—abbaka zumunci. Amma yau a dalilina har hawaye sai ya taro a idanunta Amatullah".

Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau" Abba wani abun ne ya faru tsakanin ku?".
Ya goge zuffa da ta taru masa a saman goshi kafin ya ce"na je na sanar da ita saƙon mahaifiyarki na cewa ba ta son ci gaba da ganin ta a cikin gidan nan. Haƙiƙa lamarin ya jijjiga ta amma sai dai ba ta bar ni na fahimta. Ba ta ce da ni komai ba illa fatan ɗaurewan lafiya da ta yi a gare mu, ta kuma ƙara da cewar idan har hakan zai samar mana da kwanciyar hankali babu matsala don tana maraba da duk abin da zai haifar da zaman lafiya a tsakaninmu".

Lokaci guda na daskare a wajen ina jin kamar ana ɗauɗare mini dukkan gaɓoɓina. Ban yi zaton Abba zai iya zuwa ya sanar da Anty Sawwama wannan lamarin kai tsaye haka ba. Ban yi aune ba na ji hawaye sun ciko mini koramar idanuna.
A raunane na ce"Allah ya daidaita tsakanin ku".

Ya amsa da amin yana É—aurawa da"yau za ka fara tafiya gidan kwanan ko?". Na gyaÉ—a kaina da hakan ya ba shi damar ci gaba da maganar.

"Nasiha ɗaya zan yi miki shi ne ki ji tsoron Allah Amatullah. Ki sani cewa duk in da kike da duk abin da kike aikatawa Allah yana kallonki ko da kuwa mu kin ɓoye mana, ki kiyaye mutumci da kimarki a duk kika tsinci kanki sannan tarbiyyarki ta bayyana a cikin aikinki, Allah ya kiyaye ki ya kuma tsare ki da tsarewar sa a duk inda kika kasance".

"Amin ya Allah. Abba in Sha Allah ba zan ba ka kunya ba".

"Allah ya miki albarka". Na amsa da amin ina tashi na shiga cikin ɗakin na tarar da Umma tana bacci na yi sakeke ina kallonta don ina da tabbacin ko sallan magrib ba ta yi ba balle isha'i. Kayana na ɗauka na fito na shiga wanka na dawo na tarar a lokacin ta tashi muka yi sallama da ita na fito. Na tarar da Amira ma ni take jira tun da muka fito take waya da Mansur tana yi masa kwantacen gidan Tasallan har muka isa. Kamar yadda na yi zato haka muka iske ƙofar gidan cike da masu jaura muka kutsa kai zuwa cikin gidan, inda muka iske Tasalla zaune a bisa tabarma ta ba za hajarta a gaban ta, muka isa muka zauna a kusa da ita bayan mun gaishe ta Amira ta yi mata bayanin komai.

Ta riƙe haɓa"tirƙashi! Ga shi kuma yanzu babu ɗaki duk da mutane a cikin sa, daman na yi tunanin zuwan nakun zai kai gobe ne hala ko jibi don zuwa lokacin akwai wacce za ta tashi".

"To Hajiya yanzu ya ya za a yi ke nan? Ko za mu je kawai sai goben to?".

"A'a bari na ƙira Ƴar gold na ji ko kwana za ta yi a can inda ta je ɗin, in kwana za ta yi sai ku yi amfani da ɗakin kafin na gyara muku waje zama"
Tana ƙare zancen ta ɗaga waya ta shiga latsawa, ba ma ji abin da ake faɗa daga ɗayan ɓangaren mun dai ji sai amsawa take yi da to to har ta zare wayar daga kunnenta.

"Za ku iya amfani da ɗakinta don ita ta yi nisan zango, dawowanta sai wani sati ta tafi can ƙauyen su saboda batun auren da ya taso. Sai ki tashi mu je ka ga can ɗakin sai na kai ku". Haka kuwa aka yi ta tashi ta kai mu har ɗakin kuma ta sa aka sayo mana maganin sauro ta kunna mana, muna zaune wayar Amira ta yi ruri ta kalle ni"tashi mu je Mansur ne ya iso".

"Sai dai ki je ki don babu inda zan iya zuwa yanzu".
Ba takura mini ba ta tashi ta fita bayan ta buɗe wayarta ta bar mini ita da nufin ta ɗebe mini kewa. Mahanjar shafukan alƙur'ani na shiga na soma karantun. Sai ƙarfe sha ɗaya Amira ta shigo na galla mata harara ina faɗin"na yi tunanin ai a can za ki kwana".

"Har kin fusata kenan? Yanzu dai bari na yi je na yi fitsari na zo na ba ki labari". Ban kula ta ba illa lasje wutar É—akin da na yi na ja bargo na yi kwanciyata a bisa katifar. Tamkar daga sama na ji an yaye bargo na yi zumbur na tashi ina lalumar inda na ajiye wayar Amira don na kunna haske na ga an dalle mini idanuna da haske tocila.
"Watau aure za ki yi ki bar ni ko? Kin sama wanda ya fi ni shi ne za ki juya min baya. To billahillazi ba ki isa duk gyaran da kika yi sai na buÉ—e ki sai dai a kai ki gidan nasan a haka".

Take jikina ya soma rawa na fara kuka ina masa magiya, cak numfashina ya tsaya bayan da na jin ƙarar rufe ƙofa da hakan ya yi daidai da lokacin da aka kashe tocilar.
"Wallahi ba ita ba ce don girman Allah ka yi mini rai kar ka cutar da ni....". Ban ƙarisa maganar ba na yi an sa wani abu mai kauri an ƙulle mini bakina da hakan ya hana sautina fita, na sanƙare lokacin da na ji yana ƙoƙarin raba ni da kayan jikina, na so kai masa duka, yakushi da cizo ya falla mini marin da sai da na ji bakina ya cika da ruwa wanda nake kyautata zaton jini ne, ya hankaɗe ni gefe guda kaina ya bugu da ginin ɗakina. Da wani irin ƙarfi na ji ya yage rigar jikina na yi saurin kai hannu na rufe ƙirjina, ina ƙoƙarin tashi ya jawo ni, tun daga lokacin ban ƙara sanin inda kaina yake ba saboda zafin buguwan da na ji da ya ratsa har tsakiyar ƙoƙon kaina.

[10/19, 3:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________________

Page 3️⃣2️⃣

Tun daga lokacin ban ƙara sanin inda kaina yake ba, numfashina ya ɗauke na wucen gadi na gaza motsa ko da ƴatsan hannuna balle sarrafa sauran gaɓoɓin jikina.
A hankali na soma buɗe idona da suka yi mini nauyi wasu hawaye masu zafi da ɗumi suna gangarowa ta gefe da gefen idanuna suna wanke mini fuska da nake jin sauƙar su bisa fatana tamkar tafashashshen ɗanyen ruwan dalma, na yi yunƙurin motsa jiki amma na kasa saboda wani zafin da na ji ya ratsa dukkan ilahirin jikina tun daga ɗan ƴatsan ƙafata har zuwa tsakiyar kaina.

Jin wani abu na bin tsakanin cinyoyi yana gudu zuwa ƙafafuna ya tilasta mini runtse kumburarrun idanuna ina sakin wani irin kuka marar sauri haɗe da cin rai. Na ji an buɗe ƙofar ɗakin an fita babu jimawa na ga an kunna wutar ɗakin haske ya gauraye ko'ina.
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Na shiga uku ni Amira me zan gani haka? Me ye ya faru Amatullah?". Na tsinkayo muryar Amira cike da damuwa tana nufo inda nake yashe tamkar gawa ban da idanuna babu abin da nake iya sarrafa a cikin jikina.

"Amira ki taimaka ni ki É—aga ni na zauna".

Ta kamo kafaɗana da nufin ɗago ni na calla wani uban ƙaran da babu shiri ta maida ni na koma na kwanta. Duk inda ta latsa a jikina ciwo nake ji yana yi mini.
"Amatullah wai me ya faru ne? Waye ya yi miki wannan É—anyen aikin?".

Na gaza magana illa kukan da ya ɓalle mini na ke yin sa tamkar da bakin ƙwarya. Ji nake yi gabaɗaya duniyar tana juya mini ina ganin rufin ɗakin tamkar zai rikito a bisa kaina, na yi nadama ainun na kuma ƙara yin da na sanin kasancewa ta a raye har zuwa wannan lokacin da wannan ƙaddarar ta afka mini a bisa turban tsautsayi.
"Amira jikina gabaɗaya ciwo yake yi mini, jini zuba yake yi daga jikina. Amira mutu zan yi mutu zan yi". Na furta zancen cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa cikin kalmomin da baki kan iya furtawa, ji nake ji tamkar ba zan iya ƙara ko da sakon ɗaya a raye ba saboda tsananin azaba da masifar azababben ciwon da nake ji a cikin jikina.
Chapter 43 · 0% Book details