← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 58

Sashe 26

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin ya yi wa ƙofofin kunnuwana dirar mikiyar da ya sani hanzarin kai duba na zuwa ga inda na jiyo sautin. Ban san lokacin da har ya dawo bayan motar ya zauna dab da ni ba har ina iya jiyo fitar numfashinsa ya ƙura mini idanu kamar zan cinye ni ɗanya.

"Malam ka fita tun kafin na kurma maka ihu". Da mamakina sai na ga ya bushe da dariya har da ƙyalƙyalewa, takaici ya cika ni na yi fam babu shiri na soma ture sa daga kusa da ni amma ƙarfina ya gaza don ko gizau bai yi ba balle na haƙata ta cimma ruwa. Mutuwar zaune na yi yayin da na cafko dukka hannayena ya haɗe su waje duka ya riƙe, ya fizgo ni na faɗo kan ƙirjinsa. Na runtse idanuna da mungun ƙarfi hawaye suna kwaranya.

"To yanzu ki yi ihun na ji, kina tunanin ko kin yi ihu anan akwai mai kawo miki ɗauki ne? Ko an samu ma to duk ire-irena ne nan wajen babu wani mutumin kirki da yake ko wucewa ta hanyar balle har ya faka a nan. Ki ba ni haɗin kai kawai mu yi mu gama a wuce wajen, ni ba baƙon zafi ba ne shafa jikin ma kawai ya isa ya gusar min da ishina akan ki".

"Allah ya haramta abin da zake ƙoƙarin aikatawa, ba saduwa ba ce kawai zina akwai hanyoyin aikata zina da dama. Abin da kake ƙoƙarin yi yanzu yana ɗaya daga cikin su, ka cika mini hannayen duk kafin na yi maka mummunan raunin da duk sadda ka gani sai ka tuna da ni".

Da alama bazaranar da na yi masa ba su shige ba, ya ci gaba da cewa"ki yi duk abin da za ki yi. Amma ni dai kam sai na aiwatar da ƙudurina". Kafin ya rufe bakinsa tunin na fizge hannayena daga cikin nasan na soma kai masa yakushi da cizo ta ko'ina har sai na kai shi ƙasa ya kwanta akan seat ɗin, na cire takalmina ina kai masa duka da shi cikin tafasar zuciya da ɗacin rai.

Ina cikin haka na hango Amira da Almustapha sun dosa wajen hakan ya sani furta"ka tashi ka koma mazauninka tun kafin na tona maka asiri". Tsam ya tashi ya zauna ta tsakanin kujerar direba da na mai zaman banza ya wuce izuwa mazauninsa yayin da na kimtsa kaina na zauna. Har Amira ta shigo ta rufe ƙofar Almustapha ya ja motar ban ko kalle ta balle na ce da ita wani abu, tamkar talgen da aka aza bisa wuta haka zuciyata take tafasa ina jin wani ɗaci yana gauraye mini dukkan wani kusurwan bakina yana bi har ta cikin maƙoƙarona.
Na daɗe da yi wa kaina alƙawarin ba zan taɓa ba ta kaina wani ya yi amfani da ni alhalin ina cikin hayyacina ba. Sai
dai ya yi amfani da abun da zai gusar mini da hankali kafin ya kai ga cimma burinsa a kaina.

Jin motar ta tsaya ya sani dawowa daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa. Na ɓalle murfin motar na fito na tsaya ina jiran Amira.
"Ki yi min abin da tun da uwata ta haihu ni ba a taɓa yi min irin sa a cikin duniyar bariki ba. Ina mai tabbatar miki da duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, sai na fanshe abin da kika yi min a lokacin da ba ki da wani abun da za ki kare kanki da shi".

Na cira kai ina kallonsa yayin da yake furta zancen cike da ƙwarin gwiwa yana tsaye a gabana, na galla masa harara kafin na soma furzar da takaicin da yake kwance a ƙasan raina.
"Da Allah a dogara kuma na yi imanin duk wanda ya jingina yarda da yaƙininsa zuwa gare shi ba zai taɓa kunyata ba, balle tozarta. Don haka ni kai ɗan halak ka fasa". Na ƙare zancen ina jefa idanuna cikin nasan, na daɗe da yakice wannan tsoron a cikin raina, wannan dalilin ya sanya ko kaɗan kalamansa ba su yi nasarar ɗaɗani da ƙasa ba balle su haifar da tsoro a cikin raina.

Kafin ya yi wata maganar Amira ta iso wajen ban tsaya ɓata lokaci ba ya ja hannunta muka bar wajen har sai muka tsallaka titi kafin na sakar mata hannu, daidai lokacin da ta sama sararin jefa mini tambayar lafiya?. Na yi kunnen uwar shegu da ita na ci gaba da tafiya ita ma ta yi banza da ni har muka iso gida cikin mu babu wanda ya ce ko kanzil. Muna shiga zaure ta riƙo bayan hijabina na juyo a fusace ina kallonta.
"Ga shi in kin ga dama ki ɗauka in kin ga dama ki bar shi a wajen. Tun dai ke duk abin da mutum zai yi ba ya yi miki gwaninta". Ta ƙare zancen tana ajiye mini ledar da ke hannunta a gabana, har za ta shige ciki na dakatar da ita.

"Ki yi haƙuri Amira wallahi raina ne a ɓace, da ya kai matakin da har na kasa sarrafa fushina".

"In ce dai ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni ko? Don haka sai da safe". Na yi wuf na sha gabanta tare da zayyana mata duk abin da ya faru, ita ma kanta na hangi mamaki kwance akan fuskarta.

"Amatullah me ye kai sa'in'sa da shi? Irin su fa billahillazi ba a yin ja-in-ja da su yanzu kana zaman zamanka sai su jawo maka wata masifar da babu mai iya fitar da kai. Shin ke ba ki san hanyar da za ki bi ki kuɓuce masa ba sai kin bi wannan hanyar".

"Magana ake fa ta kare mutunci da kimata Amira. Shin na yi laifi don na kaina da kimata?".

"Ba za ki gane ba Amatullah amma ina fatan nan gaba kaɗan ki gane duk karantun da nake yi miki, ba tare da kin nema fassaran su". Na sauƙe gauron numfashi kafin na furta"ba na fatan na gane wannan karatun har duniya ta naɗe". Ba ta ce da ni komai ba illa jinjina kanta da ta yi ta wuce ciki, nima na rufa mata baya bayan na ɗauki ledar.

A ƙofarmu na hango Abba tsaye yana riƙe da tocila a hannunsa kallo guda za ka yi masa ka fahimce nutsuwa da kwanciyar hankali sun yi hijira daga gare sa. Yana ganina ya iso inda nake cikin hanzari.
"An samu kuwa Amatullah?".

"E an samu".

Na amsa da shi yayin da nake miƙa masa ledar dake hannunsa, sai da ya sauƙe numfashi kafin ya duba ya gani ya ce"alhamdulillah! Allah ya miki albarka Uwata, wuce mu je ciki". A raunane na amsa da kalmar amin na wuce gaba yana baya na har muka shiga ciki.

Na zauna a falo yayin da shi kuma ya wuce cikin ɗakin wajen Umma. Tun ina lissafin fitowarsa nan kusa har sai na kishingiɗe ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba, sai ji na yi kamar a mafarki ana ƙiran sunana na yi firit na tashi. Kafin na tsinkayo muryar Abba.
"Ki tashi ki je ki kwanta dare ta yi". Ban ce komai ba na wuce ciki na kwanta saboda gajiyar da na yi jikina gabaɗaya ciwo yake yi mini, ko sallar asubahi a makare na yi ta bayan na iddar na soma karatun alƙur'ani har lokacin Umma ba ta tashi ba, shigowa huɗu yana tambayar ko ta tashi na ce masa a'a. Har sai da na yi shara na shigo ɗakin na samu a sa'ilin take tashi na tsuguna har ƙasa na gaishe ta ta amsa mini a daƙile.

"Umma me ye za a É—aura?".

Ta yi banza da ni sai can ta ce"ki dafa ko ma mene ne".
"To". Na amsa ina ƙoƙarin ficewa daga ɗakin ta tsayar da ni.
"Zo ki ɗauki wannan ledar fankasau ɗin ki fitar min daga ɗaki". Kamar yadda ta buƙata haka na yi na je na ɗauki ledar sai jin ta da nauyi alamar ba a ma buɗe ta ya hana ni fita.
"Umma ya kamar ba ki ci ba?".
"Ba a kawo min ita a lokacin da nake so ba ne".

"Umma da kin yi haƙuri kin ci ko kaɗan ne. Wallahi ba ki ga irin ƙoƙarin da Abba ya yi ba, har kasa kwanciya ya yi sai da ya ga an samu miki fankasau ɗin nan. Ko kaɗan ki ci ai shi ma zai ji daɗi....". Kallon da ta tsare da ni shi ya tursasa mini yin shuru ba tare da na gama furzar da zancen ba.
"Ba zan ci ba idan kuma dole ne cin sai kin sani dole na gani". Na sadda kaina ƙasa kafin na ce"ki yi haƙuri". Na fita daga ɗakin na je ƙofanmu na zauna na tisa ledar a gaba na zabga tagumi ina hashasho irin abubuwan da suka faru da ƙoƙarin da muka yi da Amira kafin mu samo fankasau ɗin nan.

"Tunanin me ye kike yi kuma?". Muryar Amira ta sauƙa a kunnuwana. Na bi ta da kallo yayin da take ɗauko kujera ta zauna kusa da ni kafin na yi magana da ci gaba da cewa"wannan ba ledar jiya ba ce?". Ba ta jira na ba ta amsa ba ta buɗe ganin ba ci ba ya sa ta kallona tana faɗin"ya haka kuma Amatullah?".

"Yadda kika gan shi ni ma haka na gan shi, Umma ta ce ba za ta ci ba wai ba a kawo mata shi a lokacin da take buƙata ba".
"To Abba kuma ya ya ya yi?". Na zame hannuna daga tagumin da na zagba kafin na ce"ya ya zai yi kuwa? Dole shi ma ya haƙura ai". Ta saki dariya mai matuƙar sauti da hakan ya sani kafe ta da ido.
"Mata masu duniya, lalle Umma ta na sha'aninta. Tana gara Abba kamar ƙwallon tamula wallahi shi yasa wani lokacin har cikin raina take burge ni don mazan yanzu sun zama zuma dole sai da wuta".
[9/21, 10:16 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________________

Page 2️⃣1️⃣
Chapter 26 · 0% Book details