Sashe 47
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na daɗe ina karatu kafin na ɗaga hannuna sama sai dai na kasa cewa komai illa kukan da ya kubce mini. Na kifa kai da gwiwa ina rero shi. Yadda na ga rana haka na ga dare don ko ya ya na rufe idanuna sai na ga kamar abin da ni jiya ne zai ƙara maimata kansa. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya lokaci yana shuɗe wa tun ina kwana na tashi cikin fargaba da zulumin abin da zai je ya dawo har tunanin hakan ya fara raguwa, daidai da rana guda Umma ba ta taɓa fahimtar halin da nake ciki ba balle ta lura sauyawar yanayin jikina.
Haka har sati cif ya cika lokacin ya rage saura sati biyu sauƙarmu komai ya kankama, tun ina saka rai da dawowar Ramlatu kamar yadda Hajiya Tasalla take faɗa har na miƙa lamarin ga Allah na kuma yi yaƙinin dukkan abin da ya zartar a kaina shi ne daidai. Cikin ƙanƙanin lokacin na rame na zabge na yi baƙi kowa ya ganni sai ya ce na rame. Duk wanda ya tambaye me ke faruwa na kan ce da shi karatun sauƙanmu ne kawai na sa a gaba shi yasa. Na yi duk yadda zan yi na haɗu da Ramlatu ko shi Mus'bahun amma lamarin ya ci tura duk da kuwa irin naci da bibiyar lamarin da nake yi daki-daki.
Komai nawa ya sauya hatta a karatun islamiyya ƙoƙari na ya ja baya. Har gida Anty Zulaihatu ta aiko mini kayan da Yaya Alhassan ya saya mini kasancewar ban sama nutsuwar zuwa gidan ba balle na amsa, Umma ta daka tsalle ta dire ta ce ba zan yi amfani da kayan ba.
Babu yadda muka iya daga ni har Abba, haka muna ji muna gani aka mayar da kayan, na ci kuka har na godewa rabbana.
Ana saura kwana uku sauƙan mu a wani yammaci Malam Suleiman ya zo gidan mu ya yi sallama da Abbana, tun da na ji sunan wanda ya zo neman Abba na tsinci kaina cikin faɗuwar gaba.
[10/22, 7:02 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 3ï¸âƒ£4ï¸âƒ£
Tun da Abba ya fita ganawa da Malam Suleiman na kasa zaune balle tsaye, haka kawai na tsinci kaina cikin tsananin faɗuwar gaba da kuma tsinkewar zuciya. Amir ya bankaɗo labulen ƙofar falon da hakan ya sani miƙewa zumbur na miƙe akan ƙafafuna ina sauraren abin da yake faɗi cikin tsiwa.
"Wai ki zo in ji Abbanki suna zaune".
"Ni kuma?". Na jefa masa tambayar cikin ruɗewa. Ya taɓe baki kafin ya ce"e ke ɗin fa malama". Yana dasa aya anan ya saki labulen ya juya ya fice yana wasu ƙananun magana. Jikina a sanyaye na fito ina tafi kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki na iso cikin zauren bakina ɗauke da sallamar da ta sama amsawar Abba da Malam Suleiman.
"Abba ga ni an ce kana nema na". Ya yi ɗan jim kafin can ya furta"Uwata wai me yake faruwa ne? Ga malaminku nan ya kawo min ƙorafin cewar yanzu ba kya mayar da hankali akan karatunki".
Na rusunar da kaina ƙasa ina faɗin"Abba babu komai". Ya yi saurin datsen numfashina"Uwata akwai wani abun mana ai da ba haka kike ba".
"Abba kawai jinyar da na É—an yin nan ne cikin kwanakin nan shi yasa".
Malam Suleiman ya but caraf ya karɓe zancen"Amatullah akwai abin da yake damunki duk yanayinki ya sauya, kin daina mayar da hankali akan karatunki bayan kin san cewar kina ɗaya daga cikin ɗaliban da za su yi karatu a ranar taronmu. Ki cije damuwar da ke cikin ranki ki fuskanci abin da yake tunkaro rayuwarki". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau kamar wacce aka zarewa laka, hawaye suka ciko mini koramar idanuna hakan ya sa na yi hanzarin rutsunar da idanuna ƙasa da hakan ya ba wa hawayen da ke cikin idanuna kwaranyowa.
Cikin sanyin murya Abba ya ce"Amatullah me yake faruwa ne?".
"Babu komai Abba".
"Kar ka matsa mata Malam Munnir, amma zan so ki ƙara mayar da hankalinki akan karatunki sosai. Don ba zan ɓoye miki ba ke ce hope ɗinmu gabaɗaya Amatullah, duk ƙoƙarin da za ki yi ba iya kanki zai tsaya ba har mu malamanku da makaranta abin zai shafa".
"In Sha Allah Malam na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Duk suka haÉ—e baki wajen amsawa da amin, suka ba ni iznin tafiya na tashi na koma ciki É—akin su Amira na nufa na iske ta tana waya da Mansur na zauna a gefenta na buga uban tagumi tamkar mai takaba.
"Ke kuma fa lafiya?".
"Amira wai ya ya zan yi na dawo yadda nake ne a baya? Ni kaina na san na sauya irin sauyawar da ba zan taɓa dawowa daidai ba".
Ta sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya da har sai da na ji sautinsa kafin ta sama zarafin cewa"komai fa sai a hankali zai dawo daidai ba zai yiyuwa a lokaci guda ba. Yanzu kuma me ya faru sanar da ni". Na kwashe duk yadda muka yi da su Abba na sanar da ita ta yi shuru na tsawon wasu mintuna kafin can ta ce"sai ki mayar da hankali kan karatunki tun kafin su fara zargin wani abun. Na san abin da nauyi Amatullah amma ya ya muka iya da ƙaddara".
Na fashe da kuka kamar wata ƙaramar yarinya har jikina yana rawa tamkar mazari. Ta riƙo hannuna na kwantar da kaina a bisa cinyarta.
"Amatullah wai me kike so ki mayar da kanki ne? Ko so kike yi ki jawa kanki wani ciwon na daban?. Tun ranar da abin nan ya faru kullum sai kin yi kuka fiye da sau biyar a yini guda, Haba Amatullah abin da ya faru fa ya riga da ya faru damuwa da wannan kukan ba shi zai gyara abin da ya wuce ba".
"Allah na tuba ka yafe mini kar ka hukunta ni akan laifin da na aikata a bisa rashin sani....".
Ban ƙarisa ba Amira ta rufe mini baki"kar ki ɗaura wa kanki laifin abin da ba ki da ikon sauyawa shi ko hana faruwar sa, kowa fa da kika gani a cikin duniyar nan da irin na shi salon ƙaddaran. Kuma yarda da ƙaddara tana daga cikin cikar imanin mumini". Ban ce da ita komai ba har lokacin da wayarta ta soma ruri ta ɗaga suka yi magana da Mansur sai da suka yi sallama kana ta ce"tashi mu je ga can Mansur a ƙofar gida".
"Ki je kawai". Na furta a taƙaice numfashina yana cushewa waje guda.
"Kar ma mu fara gardama da ke Amatullah, ki tashi kawai mu tafi don na tabbatar da zaran na gusa daga nan wajen kukan dai za ki ci gaba da shi". Ban tanka mata na tashi gabaɗaya jikina babu ƙwari muka fita tare da ita muka tarar da Auwal da Ummi a zaure suna hira, ta banko mana harara Amira ba ta yi wata-wata ba ta maida mata. Muka iso wajen Mansur da yake tsaye a jikin motarsa kamar ko yaushe yana latsa wayarsa tare da jijjiga makullin motarsa.
"Barka da fitowa Tauraruwar birnin zuciyata, hasken da yake haska ƙalbina ta yadda zan yi tafiya ko babu sandan jagora".
Lumshe idanunta Amira ta yi cike da jin daɗin zantukansa ta soma cewa"maraba da zuwa Sarki mai sarautar dukkan zuciyata. Ban san da wasu kalmomi zan yi amfani da su wajen nuna maka yadda na yi kewarka ba Ya masoyin raina". Wani murmushi mai laushi suka soma sakarwa junansu mai ɗauke da wani ɓoyayyan saƙonni.
"Ni kam bari na koma ciki kafin kun gama". Na yi zancen da ya yi silar dawo da su cikin duniyar zahiri tare da figzo hankali da nutsuwarsu zuwa ga gangunan jikkunansu. Mansur ya haɗe hannayensa wajen guda alamar roƙo yana faɗin"afuwan ranki ya daɗe babban ƙawa, sam ban lura da ke ba ne ayi min aikin gafara". Na taɓe baki"idan ina da zuciya ni ma dai ya kamata na daina rako ta. Kullum sai an ce da ni ba a lura da kasancewata ba a wajen". Duk suka saka dariya kafin Mansur ya ci gaba da magana.
"Tuba muke yi a yi mana afuwa. Kuma mussamman zuwan don ke aka yi ta ba na zo duba ki don ta ce da ni ba ki daÉ—i tsawon kwanaki".
Na jinjina kaina"ai na ga ana ƙoƙarin yi mini kora da hali ne".
"To yanzu dai ya ya jikin?".
"Da sauƙi alhamdulillah".
"Sai dai sauƙin musulunci aminiyarmu, amma ban ga alamar sauƙi a tattare da ke ba. Ga shi duk kin faɗa kamar kin yi shekara kina jinya". Na yi ƙarfi hali na murmusa kafin na ce"kuma fa da sauƙi sosai fiye da lokacin baya ne, ka san ciwo ne yake shiga lokacin guda amma warkewa ko samun sauƙi sai a hankali-hankali".
Ya jinjina kansa alamar gamsuwa da furucina kana ya ɗaura da cewa"haka ne kam. Allah ya ƙara sauƙi da lafiya mai amfani".
"Amin ya Allah". Muka haɗe ni da Amira waje amsawa, mun ɗan taɓa hira kafin Mansur ya ce mu shiga mu fito ya sauƙe mu a gidan Hajiya Tasalla. Muka shiga ciki muka yi wa Ummana da Umman Amira sallama muka fito, ba don raina ya so ba muka shiga motar Mansur ya kai mu gidan.
Ya fito da wasu manyan ledodi guda biyu ya ajiye su a gabana da bi ledan da ido kafin na sauƙe idona akan sa alamar son ƙarin bayani.
"Wannan naki ne ranki ya daɗe, Allah ya ƙaro sauƙi". Zan yi magana ya katse ni"don Allah kar ki ce komai kuma kar ki hana ni aikin alkhairin da na yi niyyan aikatawa. Ke fa Malama ce kin san cewa ba kyau mayar da hannun kyauta baya".